← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 95

Sashe 15

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita yashiga mota Munir yabishi da kallo yanda yake cire boturan wuyan riganshi da sauri sauri sai kawai yahau dariya yace “banda business da yawo gari gari banga uban abinda ka iyaba Riyad wlh” wani juyowa Riyad yayi yamai mugun kallo baice komiba Munir ya kyalkyace da dariya zaiyi magana wayan Mom yashigo yakalli wayan kaman zaiyi kuka yadafe kanshi yace “ohhhh Mom nadamuna wlh” murmushi kawai Munir yayi baice komiba daga wayan yayi Mom tace “kana ina”? Ahankali yace “muna hanyan dawowa” katse wayan kawai tayi jin ana kiranta adayan wayan ganin batamata rai Riyad yakeson yi da ranan nan, ganin Waziri ne ke kiranta yasa tadauka cikin barkwanci yace “Inlaw Inlaw to Alhamdulillah, yanzun nan Maman Haleematu ke gayamin Yarima Riyad yaje yaga Haleematu da alamu akwai nasara” murmushi Mom tayi tace “eh haryama fara dawowa wai kunya, kasan fa Riyad akwai miskilanci da shegen kunya har yanzu abu yake kaman karamin yaro” dan dariya Waziri yayi yace “abinki da auta, yaro kwallin kwal, ai saisa yayi farin jini awajen kowa ina mai tabbatar miki yawanci yan kwamitin nada sarki idanunsu akanshi suke nadauka zanmasha wahalan convincing nasu amman bahaka ba wlh sunason Yarima Riyad sabida yacika sharuddan zama sarki, nafarko ga tsatso mai kyau jininshi gaba da baya asalin sarauta uwa da uba, banda haka baida any criminal record ko wani case da police ko wani abu, ga ilimi boko da islamiyya ga business daya bude dake kawoma Kano cigaba sosai dazun nan Gwamna ma yakirani kinsan Meyace mini?” Dasauri Mom tace “a’a meyace?” Dariya Waziri yayi yace “cewa yayi cikin yaran sarki waye mai manya manyan hotels din nan da gidajen mai din nan nacemai ai Riyad ne” dan dariya Mom tayi tace “ai Dodo ma nakirashi nasa yama Gwamna maganan” Waziri yace “ai ina mai tabbatar miki kaman Riyad yagama dawowa sarki dudda naga take taken Baffan su Mujitapha dakuma Kabeer amman Riyad yamusu fincikau dole ki tashi tsaye” dasauri Mom tace “tuni natashi kaga yanda ake sauka akanshi ne, duk nasamai magungunan tsari a abincin danake basa da kaikayi koma kan mashekiya” Waziri yace “yauwa hakan kinyi daidai, ranan da sarki yacika bakwai za’a sa ranar da za’a nada sabon sarki sai ayi bikin Sarautar da aurensu tare koyaya kuka gani”? Mom tace “kwarai ai duk inda zan shiga saina shiga na tabbatar Riyad yagaji sarautan nan yarona kadai ya chanchanci mulkin nan bayi yanda naga dama”.

BAYAN 1YR…..

SO WANNAN NE FIRST PART NA THIS LABARI NAKAWO SHİNE SABIDA KU GANE TUSHEN LABARIN BAN WANI SO NABATA LOKACI.

GOBE ZAMU CIGABA DA LABARIN BAYAN 1YEAR RIYAD YARIGA YAZAMA SARKI❤️

💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 🔟
Cobweb tafara ciccirewa kafin tafara shara da vacum cleaner sannan tafara goge goge tundaga kan su desktop din, frames na bango, admiring design da komi na office din kowaye maishi really shows love nashi ma simplicity and art, gyara ko’ina tayi har labule saida tai dusting sannan tabude first kofan data gani ga mamakinta saitaga bedroom ne ga lafiyayyen gado awajen ga closet gyara komi tayi sharp sharp tai moping har bayin dake dakin sannan tafito tabude dayan kofan taga nan ma bayi ne ta gyara kusan 1hr tabata sannan tagama komi tafito takoma station nasu, kafin akira waya anason tazo room 456 ta gyara ta wuce taje ta gyara haka dai tai aiki had 5 sannan ta tashi.

Changing room takoma ta chanza kayan aikinta ta maida atampanta na safe tasaka pink crocs dinta na safe tana murmushin tuna Mama data siyamata sanan ta goya jakan nata tafito tana tafiya ahankali receptionist dinsu dake wajen tana ganinta cikeda fara’a tamata waving hannu tace “bye beautiful Rashy” dan kallonta Rashida tayi hatta daga hannu zata mata waving itama saikuma tasauke hannun like a weirdo, tadan kyafta ido sau biyu kafin tace “thanks” tawuce da sauri tafita dayan receptionist din tace “when will you stop throwing kanki on Rashida? Ko Madam dinmu tasan yarinyar is a weirdo” dan murmushi tayi tace “is because she’s like that nake sonta, I don’t want normal people irinmu as friends inason irinsu Rashida as friends, the girl is lovely” tabe baki dayan tayi tace “nidai nawuce asha night duty lafiya see you in the morning”.

Tana fitowa waje ta tsaya saikuma ta juyo jakanta da sauri zuwa baya tana kallon jakanta taja zip tashiga budewa tana kokarin ciro wayanta….

Ahankali yasauko da kafanshi dake sanye dawani Bottega veneta coffee color takalmi mai tsinannen kyau daga cikin motan, kumbunan shi farare kal kal agyare kaman an musu fenti tsabagen sheki dasuke, kafin gentle yakarasa saukowa yafito daga motan, dogone sosai yana sanye dawani coffee color soft yard na yan Malaysia mai bala’in taushi anmai simple aiki a wuyan, idanunshi sanye da bakin glasses na Cartier, glasses din yasa baka ganin idanunshi sai pink lips nashi dayayi so pinkish gawani irin lafiyayen bakin saje dayabi fuskanshi zuwa gemunshi da gashin baki daya karama fuskan shi kyau sosai da kwarjini da haiba kaman wani balarabe, hannunshi na daure da agogon Cartier shima latest collection dinsu, his entire body speaks luxury, he looks squeaky clean kaman ka lashesa,
daidai taciro wayan tana kokarin manna earpiece a kunnenta dan Mama takeso takira kawai taji sahun gudu gudu sauri sauri dasauri tajuyo dan taga meke faruwa, daidai lokacin itama Mirabel data fito daga cikin hotel din tazaro ido tace “Oga yazo OMG” tai parking space dagudu itama same with sauran ma’aikatan dake waje, kallon inda sukayi Rashida tayi har tana dage but still bama ta iya hango wanda ake kira da Oga sabida yanda ma’aikatan suka zagayeshi cikeda farinciki sunamai sannu da zuwa, dauke kanta kawai tayi takarasa makala earpiece din tafara tafiya abinta tana dialing number Mama….

Shifa he hates too much attention, the way suka zagayeshi ana gaidashi kaman wani celebrity yazo sai abin yakara batamai rai dan har yanzu abinda Mom tamai da Haleema na batamai rai, the way suka wani fito suna gaidashi abin kular dashi ma yayi wucewa kawai yayi batare daya kula ko mutum daya cikinsu ba yana tafiya a kasaitacce Munir shine ya tsaya amsasu daidai takai gate zata fita taji wani iska ya kadata kamshi mai dadi gaske wanda bata taba jin irin shi aduniya ba yadaki hancinta da saida ta lumshe idanu sabida dadin kamshin daidai an budemai kofa shima ya tsaya sabida sanyin dayaji yakai 10secs ahaka kafin yadaga kafa yashiga cikin lobby su dan security sun budemai glass door din, ya shiga ciki yana bin ko’ina da kallo sai kawai yawuce wajen elevator manager tafito dasaurin ta daga office dinta tana murmushi tace “welcome Sir” Gyadamata kai yayi yadauke kai yadaga hannunshi yana kallon agogon hannunshi daidai kofan na rufewa 5th floor yawuce direct office nashi yaje hannu yasa a aljihunshi yaciro wayanshi kawai ya manna a kofan kofan yabude yashiga ciki an kunna AC wajen sanyi, tsayawa yayi chak yana kallon frame na artwork dake bango dudda manager ta turama Munir hotunansu ta email shikuma ya nunamai but yanzu daya gansu in reality sai sukamai mugun kyau. Daga kafanshi yayi yataka zuwa wajen yasa hannunshi yasauko dashi yana kallo sai kawai yayi murmushi for the first time today yaji abu yasashi farin ciki. Zama yayi akan kujera tareda lumshe idanu yadaura hannunshi aka yayi shiruu he don’t like the way Mom kesashi yin abubuwan dabayaso yayi, she made him king dudda bayaso, she made him marry dudda bayaso, yanzu kuma she’s telling him how to handle family shi, bude kofan office din akayi aka shigo hakan yasa yabude ido kadan Munir ne yamaida kofan yarufe yashigo yaja kujera ya zauna kai tsaye tace “waikai meke damunka eh”? Kallonshi Riyad yayi saikuma yayi shiru tareda fuzar da iska, tashi Munir yayi yasan bazai gayamai ba yawuce wajen kofan bathroom haryasa hannu a kofan yajuyo yakalleshi yace “Riyad I hate seeing the slightest damuwa akan fuskan ka, banda you’re my brother, you are also my best friend, kowani yanayi kake ciki affects me, life can be colorful idan you let it be that to you, be the Man of your life karka bari kowa yagaya maka ga yanda zakayi, you are loved, jama’a harda wayanda basu sanka ba na yabonka, kana adalci asarautan dakake yi kadena bari anything na damunka kaji”? Dan kallonshi Riyad yayi for the second time yayi murmushi yace “okay” bude kofan bathroom din Munir yayi harzai shiga ahankali Riyad yace “thanks” kallonshi Munir yayi sai kawai yayi murmushi yawuce yashiga bayin maganan Munir yasa yaji sanyi aranshi he will take things easy on kanshi and everyday he will try and do wat makes him happy he will live his life, daga yanzu kullum saiya fita zai chanza schedule nashi daga 4:00 har dare ya warema kanshi da safiya kuma fada, he will leave 2 separate life dinshi privately and peacefully, tashi yayi ahankali shima yawuto yabude kofan dakin yashiga bathroom yawuce direct yadauro alwala yafito abu yataka dayaji ya chaki kafanshi dasauri ya tsaya yadaga kafar ya kalli kasan carpet din yaga karamin dankunne ne baki ya shiga kafanshi dudda bai shiga sosai ba, ahankali yakai hannunshi yacire daga kafanshi yakalli earring din murya chan kasa yace “who dropped this here?” Yayi shiru yanabin dan kunnen da kallo daidai Munir yace “kana alwala ne koka fito? Muje mosque” dasauri ya zura dan kunnen a aljihunshi absentmindedly gudun kar wani yataka, yataho yabude kofan yadauki glasses nashi da waya Munir yace “ba nan kasa zamuje salla mudawo muyi aikin ba” wucewa yayi yace “I thought kaikace i should always be happy, zanje na buga golf yau, tunda Mom tasamin aikin sarki ban buga golf ba” murmushi Munir yayi sai kawai yabiyoshi suka wuce suka fita.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 1️⃣1️⃣
Chapter 15 · 0% Book details