← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 95

Sashe 48

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tabita da kallo saikuma tace “hala batasan inada HiV ba” saikuma takalli Rashida da yau bata minshari sosai sabida batai aikin wahala sosai ba tashafa kanta tana murmushi tace “Amaryan Riyad” knocking akayi aka shigo office din Dr Bugaje ce sanye da scrub tana kallon Mama tace “kinga sai yanzu nafito daga surgery nan dana gayamiki wlh nace nadubaki kafin natafi, akwai wani abu dake miki ciwo?” Tayi maganan tana makala stethoscope dan duba heartbeat na Mama, Mama tace “lafiyana kalau wlh kaman ki sallame ni gobe ma naje nafara shirye shiryen bikin Rashida” dan dariya Mrs Bugaje tayi tace “mother Inlaw of the year Mama” kafafun Mama ta kalla da sun sabe kusan rabi tace “Alhamdulillah Mama kin sami lafiya sosai Welldone Mama, you’re a superwoman, wannan hartai bacci” tanuna Rashida, Mama tace “ai Rashida gatada nauyin bacci kamanme” Mrs Bugaje tace “tom bari naje Mama saida safe, banda tunani kinji ko” murmushi Mama tayi tace “to nagode, a gaida yara” juyawa Mrs Bugaje tayi hartakai kofa Mama tace “Doctor” juyowa Mrs Bugaje tayi Mama tace “ina alfahari na sanki, nasan ko bani Rashida nada wata uwa da mentor, thank you for everything” dan blushing tayi tace “Mama stop thanking me ki warke sabida ki koma gida nan da jibi ko gata” Mama tace “shikenan a kiyi tuki ahankali dare yayi” “toh” tafadi tana fita Mama kuma tashiga shafa fuskan Rashida har bacci yasoma kwasheta kafin chan bacci yayi nasaran dauketa.

Jijjiga da bed keyi up and down yasa cikin nauyayyen bacci Rashida tadan bude idanunta sabida yanda motsin ke mugun damun kanta, kafin chan motsin yayi yawa tabude idanun gabaki daya tana tashi zaune, Mama tagani tana wani bankarewa tana kama cikinta tana. “Hasbunaallahu wa ni’imal wakeel, Lailaha illallah wayyooo cikina wayyooo cikina” dawani irin sauri Rashida tai ihu. “Mama” daidai Mama tawani irin mirgino zata fado daga gado Rashida ta tareta takamata ajikinta tama rasa mezatayi, bata taba ganin Mama in this pain and agony ba cus tanada dauriya na ban mamaki, kankame Mama tayi datake abu kaman zata tashi ga kafafunta basa motsi tsabagen azaba tace “Rashida cikina wayyooo Rashida cikina, Rashida cikina” “somebody help me Doctorsssss!” Rashida tai wani irin ihu daya dauka ako’ina daidai lokacin kawai hancin Mama yafara fitowa da jini dayasa tasake buga wani uban ihu. “Doctors” daidai nan Dr Mumina dawasu nurses suka shigo ganin Rashida da Mama akasa yasa tace “meya sameta”? Jikin Rashida kawai rawa take bamata iya magana ba, kankame Mama tayi a hannunta Dr Mumina tashiga saka handglove hakama Nurses din wasu Drs ma na shigowa aka daga Mama daga jikinta aka daura akan gado Rashida na wani irin kuka tace “wat happened to her? Why is she bleeding daga hanci” Dr Mumina tama Nurse alamu tafita da Rashida wayanta Rashida ta dauka Nurse tafita da ita, rawa jikinta yake tana tsaye awajen Doctors sai zuwa suke ana shiga dakin da Mama ke, tanajin wayyyoo Allah cikina, cikina abinda Mama ke fadi kenan, tunda ta taso bata taba ganin Mama tai ihu tana kururuwa for ciwo ba sai yau, chan Rashida taji ana call Professor call him fast, taga nurses sun fito da gudun gaske sai kawai taji kafafunta na lankwashewa ta zube akasan wajen flat hannunta ya shiga rawa tabude wayan nata tashiga contact taga Riyad hakan yasa tai dialing number.

Yau sabida damuwa yamai yawa koda yagama abinda zaiyi da Haleema anan kan gadon ya kwanta bayan yayo wanka, wayanshi yahau kara hakan yasa yabude ido is so odd akirashi da night wayan yatashi yadauka Rashida tafito jikin screen din dayasa kawai yaji gabanshi yafadi fita yayi daga dakin yasauko kasa daidai wayan na katsewa yayi dialing number back yana ringing ya daga. Anatse yace “meke faruwa?”Nunfashinta kawai yakeji bata iya magana da kyar tace “zan…..zan mutu” katse wayan kawai yayi yakoma sama yashiga saka kaya Haleema na tashi dan tun ringing na wayan ta tashi tace “ina zaka Baby”? Ahankali yace “sleep fita zanyi” zatai magana yadauki car key yafita da sauri yashiga motanshi yana danna remote gate yabudu yaja motan aguje dayake dare ne wlh cikin 5 good minutes ya iso asibitin sama yahayo aguje, tana zaune a inda take akasa ta hangoshi yana tahowa yana kallonta she felt as if her strength is coming towards her, dawani irin gudu cikin kuka ta tashi tai wajenshi batai wata wata ba tawani irin fada cikin kirjinshi ta kankameshi gamgam kaman wani zai rabata dashi tana wani irin kuka tama kasa magana, ahankali yasa hannunshi on her back yariketa yama kasa magana sai breathing fast, suna ahaka saiga Mrs Bugaje da hijabi tana gudu sosai tawuce su tai dakin kawai his mind tell him something hakan yasa yayi hugging nata so tight tareda manna mata peck a wuya, cikin wani irin murya na lallashi yace “stop crying Jewel, come” yadagota hannu yasa ya sharemata fuska yace “I’m here now Mama will be fine kinji”? Gyadamai kai tayi yakama hannunta saiya sauka kasa da ita yayi wajajen wasu kujeru ya zaunar da ita yaduka agabanta yace “stay here bari naje sama naga meke faruwa” gyadamai kai tayi yatashi yajuya yakoma sama gabanshi faduwa kawai yake non stop, direct yabude kofan dakin daidai lokacin da babban professor kecewa ke daga hannunshi yana kallon wristwatch dinsa yace “Time of death 4:57AM” chak Riyad ya tsaya kanshi na wani irin making bell sound yashigabin kowa na dakin da kallo tundaga kan Mrs Bugaje datai mutuwan tsaye tanama Mama wani irin kallo da idanunta ke kallon sama ga jini a hancinta da bakinta na gangara har lokacin, kafin ahankali Professor yakai hannunshi dake sanye da glove ya rufemata idanu sannan yaja farin zanin gadon yarufeta.

EPISODE 3️⃣1️⃣
Sarawa kawai kan Riyad keyi, Mama dasuka gama hira jiya, he left this hospital shida Munir jiya around 7 Mama was absolutely fine tana bacci, Mama was out of danger, kafafunta kumburin sun soma sauka, now tarasu? Yakasa anything tunanin, ahankali Mrs Bugaje tasa hannu tadauki wayan Mama data gani saman fridge tajuyo takalli Riyad that looks terrible tabashi wayan anatse tace “call Baba Liman!” Saikuma muryanta na rawa tace “how do I face Rashida?” Hannu yasa ya karbi wayan cikeda taurin zuciya na maza yadanna wayan yaga Baba Liman a dial calls yakira asuba tayi so wayan na ringing yadaga da sallama me sanyi ganin lokacin da ake kiranshi da wayan Zainab, ahankali Riyad yace “Baba Riyad ne Allah yayima Mama cikawa!” “Innalillahi wa Innailaihi raji’un! Allah ya gafartama Zainab! Zainab Allah yasa karshen wahalan kenan! Nazo ne ko zaku taho da ita? Ahankali Riyad yace “zamu taho da ita” Baba Liman yace “toh! Allahu Akbar akwai lokacin da Zainab ta taba bani number dan uwanta Sama’ila tace duk randa ta mutu nakirashi nagayamai shi kadai ne jininta daya rage aduniya, hakkine agari ni nayi hakan bari nakirashi” ahankali Riyad tace “toh” yadaga wayanshi yakira Buba yakira Munir duk sukace gasunan zuwa, yakalli Dr Bugaje yace “lemme get Rashida” gyadamai kai tayi tana hawaye maganan da Mama tamata dazu na dawomata sabo azuciya.
Rashida na zaune inda ya ijiye ta gabanta sai faduwa yake none stop bini bini tana goge hawaye, kamshinshi kadai taji hakan yasa tadago takalleshi wani irin tsawaa kirjinta yayi sabida yanda taga idanunshi sunyi jaaa, amman ta daure tana dafa kujera tamike tsaye ta tako zuwa gabanshi ta tsaya tahau bude baki tanaso tai wani specific tambaya but tambayan yaki fitowa daga bakinta, Riyad jiyayi zai fashe da kuka ganin reaction na Rashida, runtse idanunshi yayi dayasa Rashida tawani irin kurma ihu a inda suke tace “nooooooooooo!” Saikuma tabi ta gefenshi ta kwasa da gudu tai sama yabita shima, ahankali tabude kofan Mrs Bugaje tafara gani tsaye idanunta sunyi jaaaaa hakan yasa tafara kokarin daga kanta tanaso takalli gadon dakin amman tana tsoron kallo kafin ta daure ta kalla taga Mama kwance an lullubeta da farin zani, wani kalan lankwasewa kafafun Rashida sukayi nan daidai Riyad na shigowa yazo gabanta ya duka gadon tamai pointing tana nunawa da hannu still takasa magana sai kuma tafara wani irin jiniya tace “Ma………Ma……..Mama na……..ni……” kaman ta zare ta nuna kanta tace “ni……Mama…..Mamana……Maman Rashida…..ni….ni…..Mama na ni, nawa My Mama achan”? Kai! Wani irin fadowa hawaye sukayi daga idanun Riyad yanda kalaman ke fita daga bakinta adaburce, akuma hargitse, ya gyadamata kai gently yace “Mama ta ras……….” “Noooooooo!” Rashida tai wani irin ihu tafashe da wani irin kuka da majina yafeso daga hancinta har zuwa baki tana wani irin babbaka kuka tana dukan kirjin Riyad da babu karfi a hannunwanta, daidai Munir ya iso shima yaci birki ya tsaya yana kallon yanda Rashida ke kuka beating Riyad chest, kuka Rashida take dake tsumarai daidai nan shima Buba ya iso da manyan abokanenshi mota guda sukayo dawata mota doguwa cikeda hikima da dabara yace “Munir kayi procedures kabiya komi abamu gawanta mutafi dashi” yakalli Riyad yace “Riyad take her to the car kujiramu tunda bamusan gidansu ba” ahankali Mrs Bugaje tace “I will go with you Riyad nima bansan gidan ba” daga Rashida dake kuka yayi kawai ta sheme a suma daukan ta yayi chak yawuce mota ya ijiyeta abaya.

*SANYI DA ZAFI*

*EPISODE 32*
Cikin minutes Buba yayiarranging canopy ganin ranayasoma fitowa ga jama'a atsaye, aka kawo taburmaitundaga makarantan sa akashimfida awaje, Munir daRiyad suka kawo likafani dahandglove da turare dasuaudugu Matan anguwa dukababu wacce tai attempting yimaMama wanka da Mrs Bugaje ketambaya duk sunki karsu samiHIV, wai tsoro, hakan yasa MrsBugaje ta karbi komi tashiga kairuwa ciki ita zatayi.
Ahankali Rashida ke budeidanunta takalli Mrs Bugajedake kanta anatse tace"Rashida!" Tashi tayi zaune dagudu tana kallon matan layinsuda hijabai da suka cika falonwasu na kuka suna kallontawasu na mata kallon tausayisai kawai ta tashi kamanwacce bata hayyacinta tayiuwardaka tana daga labule MrsBugaje taje wajen tace "zanmaMamanki wanka Rashida come"
Chapter 48 · 0% Book details