Sashe 61
Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Kowa kallonta yake tace “nasan zata iya karyatani amman kun ganni nan kap rayuwana bansan wani me HIV ba ita ke gayamin cikin bayin da aka kawo mata daga wani yaki lokacin akwai wata daketa ciwo takaita asibiti akama yarinyar gwaji akace HIV ne inhar zaku tuna cikin bayi da aka rarraba lokacin wata mai suna Safara’u Mamanka akaba” Gwaggo tace “kwarai natuna Safara’u idan naje dakin Maryam ina cewa ke bakicin abinci ne amman daga baya nadena ganinta, Jummai tace “bayan tagano tanada HIV ta sallami yarinyar a boye tabata kudi takula da kanta shine take gayamin zata iya kiran yarinyar awaya mu mata allura mu debi jininta musan yanda zamuyi mu sama Zainab jinin ajiki” Kowa kallon Jummai yake adakin tace haka takira yarinyar ita oo baniba tasa hannu tadauki sirinji taja jinin yarinyar tabani natafi dashi lokacin Zainab batada lafiya cus cikin na wata guda mugun laulayi take, ana ma kara mata ruwa ne tana bacci kuma tanada nauyin bacci, lokacin yayi daidai da lokacin da babu kowa adakin, Muji yafita aiki naje na zare karin ruwan kaman yanda ake dura maka allura ta wajen yashiga jijiya haka na kafa gindin sirinjin a ramin na fesa jinin ina kallo ina murmushi cikin bacci tadanyi motsi ta tashi da sauri naja ruwan ina maidamata nace yacirene ruwan koma baccin ki, takoma bacci natashi natafi naje na jefa syringe din abola. Nadinga cewa zaiyi kuwa Mrayam nacemin ai zaiyi menene menene ahaka data fara ciwo awata na shida akace HIV n…..” wani irin fizge kanshi Muji yayi yay wajen Jummai yafara dukanta tana ihu saida aka rikeshi tahau dariya kaman mahaukaciya tace “ku kasheni to me yarage narasaka Muji I’ve lost komi, kome nayi aduniya sabida kaine dan haka tafashe kawai guess wat har asibiti na bita nabata guba ta mutu! Yes i poisoned her” Innalillahi yanda kirjin Riyad ke bugawa yakusa barewa so Mrs Bugaje was right data kirashi just last night harya fara bacci tace tana suspecting poisoning Mama akayi cus bakinta was green datana mata wanka tagani but tanakan investigation. Wannan karan wani kalan zubewa Muji yayi akasa yana kallon Jummai dake kallonshi tace “I was a good wife babu abinda bana maka, kusan bautamaka nakeyi, after Allah da shine ubangijina wanda nake bautamawa you were the next person in my life, ka kama kayimin kishiya ka manta dani da duk abubuwan dana maka, wata ta dauke maka hankali dare daya, nikuma nai alkawari saina rabaku har abada!” Runtse idanu Riyad yayi duk yanda yaso yadaure saiga hawaye sun zubo daga idanunshi, ko shine Rashida bazaiso yayi zaman aure da wanda members of his family are like this ba. Fuskanshi ya share yamike tsaye tareda juyawa yace “ku kulle both Maryam and Jummai and call the police they will both pay for crime nasu, Mama will get justice” dasauri Mom tace “Riyad Riyad” wani ihu yayi yace “take this two women out of this room now!” Fita dasu fadawa sukayi shikuma Riyad yawuce sama da gudu. Hatta Maman Kabeer saida jikinta yayi sanyi tasan da sunso su kashe Riyad but bayan yazo yazama sarki sun hakura ganin be wani iyaba sunsan zaiyi making mistake daga baya, or da kanshi ma yace yasauka, wickedness din Jummai da Mom bazata taba iyawaba, haba HIV fa ina mata zasu da kishi, itada mijinta yayi mata hudu curr da kwarakwari fa tace me? Ina mata zasu da kishi? What is this? Infect innocent woman da HIV Ya Allah, jitayi jikinta yayi sanyi wani tuba da tsoron Allah na shiganta, remembering yanda Mama ke kuka alokacin tana cewa ita ba fasika bace Allahu Akbar! Allahu Akbar! Inama tana raye! Wayyo Allah.