← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 95

Sashe 27

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

sabida yanda kirjinta ke bugawa da gudu da sauri sai kawai ta tsugunna, wani irin tausayi yaji tabashi yakasa cemata komi, da kyar kusan 30sec sannna ta mike jin tadawo daidai cikeda karfin hali tace “ina Mama wat happened to her? Nace mata kartazo tabada hakuri but taki jina, normal Mama da tuni tadawo, tana ina yanzu? Just tell me wat happened to my mother mekuka mata? Me kuka gaya mata? My Mom is very sick, tell me tana ina yanzu?” Tai maganan hawaye na cika idanunta harwani kyalli suke adake still kallonta yake yace “she’s fine now but tana hospital” hannuwanta biyu ta daura a fuska saikuma ta juya takai hijabinta ta goge fuskanta tass tajuyo ta kalleshi da jajayen idanun hijabinta daya jike da kuka ya kalla sannan yakalleta, cikeda dauriya da karfin hali tace “inane asibitin bani address din natafi” batare dayay magana ba yajuya yace “get few things da Mama zata bukata lock the house I will take you there is late bazakije da kanki ba” yayi maganan authoritatively yawuce yabude motan ya shiga gaba, kallonshi tayi sai hawaye sai kawai tajuya takoma cikin gida, drawer tabude takwaso simple t-shirt tasa ajaka tadaga kayansu ta dauko ledan duka kudin dasuke ijiya 139k, tadauki dadduma da zanin gado wankakke tasa ajakan bayanta takashe wuta tafito sai goge hawayenta take tarufo kofan waje tasa key sannan tajuyo ta kalli motan, bata taba shiga mota babba haka ba, ahankali yakawo hannunshi yabude kofan ganin yanda take kallon motan kaman matsoraciya, daurewa tayi ta matso ta shigo ta zauna agaban ta maida kofan tarufe wani sanyi da kamshi na dukanta ta rungume jakan a hannunta gam. Tada motan yayi ahankali sannan yafara tafiya bini bini tajuyar da kanta takalli gefen window tana goge fuska, sunyi tafiya na kusan 30min sannan sukakai asibitin da saida ta firgita ganin kyanshi dan tasan zaiyi tsada tayaya zata biya kudin?Parking motan yayi yafito, kokarin bude kofanta tashigayi tafito takasa, cus ba irin normal kofan mota data saba dashi bane, abinma yana nema yakarasata kuka ta daure ganinshi ya zagayo ta inda take yana kallonta ta glass dan wannan motan ba tinted bane, bude mata kofan tayi da sauri ta sauko batare data kalleshi ba ta tsaya gefenshi dan nesa dashi maida kofan yayi yarufe sannan yafara tafiya tabiyoshi abaya da saurinta suka shigo cikin hospital din har zuwa dakin da Mama take kwance kafinma yasa hannu yabude kofan da sauri tasha gabanshi ta rigashi tura kofan tashiga ta tsaya chak tana kallon Mama dake bacci an samata ruwa an makala mata wasu abubuwa a hannu yarda jakan dake hannunta tayi awajen tawuce dakin da gudu taje inda Mama take kawai ta kwanta jikin Mama ta manna fuskanta akan wuyanta tana kuka sosai wanda babu kara idanba ka kalli kakkarwan da jikinta keyiba bazaka gane kuka takeyiba, ahankali yaduka yadauki jakanta yashigo dakin yakawo gefen gadon ya ijiye saikuma ya zuba hannayenshi a aljihu yana kallonsu, takai 3min ahaka sannan ta taso da sauri ta dauki Dr note dake saman table na gadon ta shiga karance karance magungunan da alluran dake wajen ta shiga duddubawa tana karantawa har drip din da aka samata sannan ta sauke ijiyan zuciya tasake zama bakin gadon takama hannun Mama tarike gam tana kallonta, kawai kana ganin Rashida kasan yanda takeson Mamanta, ta dade ahaka tana kankame da hannun Mama sannan tasaki hannun takai hannayenta ta share fuskanta tajuyo tareda tashi tsaye ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta dauke kai cikin muryanta dahar ya chanza sauti sabida kuka tace “nawa ka kashe nabiyaka inaso akira Dr ya sallameta na nemo keke napep nakaita chan asibitin datake amfani dashi” yana kallonta right in the eye yace “which hospital”? Ahankali tace “teaching hospital” kai tsaye cikeda izza da iko kaman Mamarsa yace “kibarta anan” da sauri ta kalleshi sake hada ido sukayi cikin konewan idanu Rashida tace “wannan kuma nice next of kin nata i decide and make decision for my Mom not you, nawa nidai ka kashe” yadade yana kallonta baitaba ganin feisty mara kunyan yarinya irin this girl ba, yana kallonta yace “idan Dr yazo ki tambayeshi” yajuya zai wuce tace “eh zan tambaya and i will pay you back cus banson any favor ko taimako from anybody zan kawoma kudinka” dan jimm yayi sai kawai yabude kofan yafita, mota yawuce yashiga yatada yayi dialing number Dr yana dagawa yace “Dr on no condition zakai releasing that patient without letting me know, don’t let the Daughter take her to another hospital, sign them up for abinci” cikeda girmamawa yace “to Ranka shi dade” dan yatsine fuska yayi ahankali yace “and about that!” Yadanyi shiru chan yace “don’t disclose my identity to anyone nor address me ahaka in front of anybody” Dr yace “shikenan Riy….” Harya katse wayan ya bala’in gaji hotel yakoma ya kashe mota ya sauke ya shiga ciki ana gaidashi ko amsasu baiyiba yawuce office nashi straight yana budewa ya shige ganin desktop a kunne yasan Munir na ciki, hakan yasa yawuce ciki Munir na kwance yana buga game a tv dagashi sai singlet da 3quater ganinshi yasa ya ijiye remote yataso yace “ance Maman yarinyar tazo and she fainted kasata a mota hospital ka kaita” yana cire riga yace “eh” tsayawa Munir yayi yana kallonshi yace “I know the girl itace wacce saved you but are you sure zaka barta tacigaba da aiki kai the girl have quiet a temper” batare daya amsashi ba kawai yawuce yafada bayi wanka yayo yafito daure da towel a waist turaruka ya tsaya ya fesa sannan yazo yazauna, Munir tace “Mom takirani yafi sau goma nace mata we are not together tace she will call back in the next 5mins idan ban hadata dakai ba zata kai karana wajen Ammi” Shiru yasakeyi hakan yasa Munir yadafa kafadanshi yace “common mana fushin ya isa haka before kasa karyan vakada lafiya da Mami tayi azo asani please go back home” yatsine fuska yayi yace “I’m hungry Muneer, please kaje gida ka kawomin abincin Ammi” tashi Muneer yayi yace “okay”. 💫 SANYI DA ZAFI 💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 1️⃣6️⃣
Chapter 27 · 0% Book details