← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ahankali yake tafiya da shi da Munir dawasu ma’aikata guda biyu dake biyedashi abaya, akwai some changes dayakeso ayi abinda ma yakawo shi hotel din kenan this morning, duk ya gama nuna musu saura changing room na ma’aikatan shi corridor suka shigo suna biyeda shi yasa hannu yabude kofan yasakai ciki yana magana yace “the lockers nakes…….” Shiru yayi ganin yanda Rashida tawani yarda takeaway jellof rice din da ruwan yashiga tittila akasa ta tashi tsaye da sauri daidai su Munir zasu biyoshi su shigo ciki yace “wait!” Duk kallonshi sukayi suna tsaye bakin kofan batare da sun shigo ba strictly yace “kuje lobby” yanayinshi kawai yasa Munir yace “okay” yajuya ma’aikatan ma suka bishi yajuyo yazuba mata ido tana kallonshi cikeda fada baki tabude zatai magana dan akwai abinci abakinta sai kawai tai wani wawan kwarewa sai tari, maida kofan yayi yarufe ya kalleta ganin yanda take tari kaman zata mutu yasa gently yaduka yadauki bottle water nata daya fadi yadan zube yamike tsaye yasake kallonta tsabagen tarin datakeyi tama kasa tsayuwa ta tsugunna idanunta sunyi jajir ga rice guda daya fito daga hancinta alamun ba karamin kwarewa tayi ba, dasauri yataka zuwa inda take ahankali ya tsugunna yamika mata bottle water batare dayayi magana ba yana kallon fuskanta, tsabagen azaba sabida ga yaji a abinci ga kearewa mai kyau batasan lokacin data daura duka hannayenta biyu saman kan nashi ba takama both hannunshi da goran takai bakinta hakanan jiyayi jinin jikinshi ya tsaya chak jin saukan hannayenta biyu kan nashi, ahankali yadaura idanunshi kan hannunta dake saman nashi sannan yakai idanunshi kan fuskanta da yanda takeshan ruwan kaman yaki, tass ta shanye ruwan sannan tacire bakinta daga goran har lokacin tana rikeda hannunshi dabatasan tayiba tana sauke ijiyan zuciya kaman wacce tagudo daga hanyan mutuwa idanunta sunyi jaa, kusan 1min tayi tana sauke ijiyan zuciya sannan ahankali kaman mara gaskiya tadan dago kanta tadaura idanunta akan nashi yanda yake duke dab da ita kamshin turarenshi ya bade wajen da sauri ta maida idanunta kasa still bata sakeshi ba, yana kallon fuskanta baya ko kyafta ido yace “can you let go off my hand now”? Dawani irin sauri ta kalleshi saikuma ta kalli goran ruwan data rike ganin yanda ta kama hannunshi da duka hannuwanta biyu saida taji kaman ta kurma ihu sabida kunya dawani irin sauri tasakeshi hakan yasa ya mike tsaye ya kalli magungunan ta dake kan bench na wajen sannan yawuce kofa haryasa hannu yabude kofan ya tsaya batare daya juyoba yace “kifito amaidaki gida, kafin ki mutu in my building” dasauri ta kalleshi kaman wata damusa dan juyo da kanshi yayi but bai kalleta ba yace “take days off when you feel better you can resume” yasa kafa yafita saikuma ya tsaya yace “someone will clean the place you don’t have to, kifito akaiki gida!” Yana maganan yawuce yafita takai almost 2min aduke a inda yabarta saikuma ta daga hannuwanta ta kalla yanda tarikeshi saikawai taji kunya da haushin kanta sai abin yasa taji mugun zazzabi ya rufeta tanama jin sanyi, ahankali ta lallaba ta mike tadauki jakanta ta goya abaya batare data chanza uniform nata ta maida abayanta ba kafin wani ya sake shigowa yaganta tana chanza kaya she will not take the risk, tadauki magungunanta tarike a hannu tafito tana tafiya ahankali hakanan kawai sanyi taji tanaji barinma a hannuwanta dasuke abude dan uniform nasu short hands ne, gashi small farin baby hijab ne jikinta that covers her chest only, ahankali take tafiya is as if every step datai taking yana kara mata zazzabi harta fito lobby kadan kadan take tafita tana jin sanyi kaman akwai kankara awajen, hakan yasa bakinta yahau kakkarwa irin na me jin sanyi din nan kaman an sata a cold room, idanunta na rawa rawa suna kukkullewa kadan kadan take bude idanunta tasan ta hango mutane zazzaune da suit a lobby daganan kuma batasan meya sake faruwa ba dipp kaman an dauke wuta ta zube awajen.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣8️⃣
Chapter 32 · 0% Book details