← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 95

Sashe 12

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Around 5 Mama ta tadata daga bacci, da kyar ta tadunma Mama, Mama tace “ke yarinya sai nauyin bacci kaman wani kato, tashi kin manta yau zaku koma makaranta eh? Hope kin dauki permission wajen aiki an baki shift na yamma”? Gyadama Mama kai tayi cikin gajiyan bacci, hannu Mama tasa tadagota ta taro kafadanta hakan yasa Rashida tasauke kanta akan kafadar Mama tana kara lumshe idanu still cikin bacci, dan jijjigata Mama tayi tace “Rashida” ahankali tabude idahunta tass takalli Mama dasu Mama tace “I think drop most of ayyukanki tunda kin koma school kinga yanzu year 5 kike you need to study well, nakosa naga diyata tazama likita, saura 1yr yanzu, Allah ya aramin rai, ranan super wax zan saka amin combination da super lace” dan murmushi kadan Rashida tayi tanason taji Mama na maganganu haka it makes her happy, Mama tace “yanzu dai kinga kina bukatan lokacin hutawa da lokacin karatu bakiga yanda kike gajiya ba da kyar kike tashi, ki saki sauran ayyukan ki rike na hotel din nan kadai tunda anfi biya, su Maman Miwa da sauran wajajen nan ki sakesu” dan murmushi tayi sai kawai tahau yunkurin tashi ahankali dan muryanta baya fita sosai sabida daga bacci ta tashi tace “Mama so kike na bar aiki sabida mudinga karban abincin sadakan da yan anguwan nan suke kawo mana out of pity?” Tadanyi shiru daidai takarasa mikewa tsayen batare data kalli Mama ba tace “this year is clinicals, zamuyi aiki a pediatric da obstetrics&gynecology, I can manage everything Mama trust me, Alhamdulillah kome aka koyamin sau daya ya zauna akaina, sannan daga yanzu koda ranan Sunday ne zan dinga zuwa library duk sati sau daya nayi muraji’an duka abinda aka koya mana na that week, I can study Mama, I can do my duties na kula dake da siyamana kayan abinci da kudin magunguna, I can manage my work also” tana maganan tayaye labule tafita daga dakin tawuce waje saida tafara sa abinci awuta sannan tawuce bayi tayi wanka tafito lokacin har sanwan yayi tazuba taliya sannan takoma daki tashiga saka kaya Mama na zaune kan dadduma tana kallonta, tana kallon yanda taketa ciro kayan ghana masgon dasuke agoge daga gani kasan dan kaya mai kyau take nema na zuwa school abu Mama taji ya tsaya mata a wuya sai kuma ta daure kawai ta dauke kanta daga kallonta.
Wani doguwan rigan atampa maroon ta zaba ta maida gefe, taciro lab coat nata dayake a goge shima ta ijiye gefe sannan ta maida sauran kayan ta shirya tsaf tawuce tafita tasake juya taliyan sannan tadawo tasa hijabi ta kabbatar salla.

Tana idarwa bata tsaya yin azkar ba ta fita ta juyo taliyan a kula tasama Mama ruwan zafi na wanka sannan tadawo tasake zama kan dadduma tafara azkar tana gamawa ta kalli Mama dake kallonta tace “Good Morning Mama na nikadai, Mama naji dadi nikadai kika haifa nake moreki banda kanni dazaki dinga raba attention naki akanmu” most time tana maganan ne idan taga abu na damun Mama dan tasata tai murmushi, ganin Mama batai murmushi ba yasa takama hannunta tarike dasauri ahankali tace “Mamaaaaaaa” tai maganan ashagwabe tana lankwasa kai, ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “babban burina arayuwa shine ki zama likita Rashida, banson wani abu dazai hanaki zama, kina bukatan lokacin dazaki karatu, banson ki fadi, banson ki sami carry over, nasan kinada kokari but dudda haka karatu yanada amfani, kina all this ayyuka bazaki sami lokacin yi ba, ki manta da kula dani Allah daya tsaga mana baki bazai hanamu abinda zamusa abakin ba, after this year next year zaki gama, please Rashida kibar ayyukan nan and focus a karatu” tunda Mama ke maganan take kallonta batason sata cikin damuwa hakan yasa tace “to naji Mama amman tunda kinga satın nan muka koma karatu da practicals bazasuyi serious ba kibari nayi aikin zuwa karshen wata abiyani kudina saina dena kinji, zancen night shift ai HOD mu tasan dani bata taba sani a night shift ba sabida ke Mama, so ko yanzu ma bazan bazanyi night shift ba, kinga na karbi albashina saimu ijiye, kuma Mama kidena damuwa yarki ta dauko brain dinki bazan fadiba In sha Allah bayan kinamin addu’a, to yanzu kin hakura na karasa zuwa karshen watan nan duk sai na saki aikin nabar na hotel din?” Shiru Mama tayi tana kallonta Rashida da taurin kai da kafiya hmm, ijiyan zuciya tasauke tace “okay! Yau sha uku ga wata, karshen wata zaki sallame kowa, next month banson ganinki kina zuwa ayyuka nan” gyadama Mama kai tayi tace “naji” tashi Mama tayi tace “ai shikenan” tawuce sip wani akwati zata dauko dasauri Rashida ta tashi tace “Mama stop ki kirani na dauko miki” dasauri tasa hannunta tadauki akwatin tasaukar dashi kasa Mama tazo wajen ta zauna itama Rashida ta zauna gaban box din tana jiran tadauki abinda zata dauka tasake daukan akwatin ta maida sama, wata yar jaka Mama tadauko acıkın box din tamika mata tace “gashi ungo” dasauri Rashida ta kalli jakan data bata tace “na menene Mama”? Tasa hannu tana karba, zage zip din box din Mama tashigayi tace “naki ne kibude” da sauri taciro bakin ledan data gani cikin jakan dayake a kulle tashiga budewa saiga crocs a ledansu pink color mai kyau ba asalin designers one dinba but irin normal wanda ake saidawa a market yan 5k-7k dakuma stethoscope pink shima mai kyau, da mamaki take kallon kayan dakuma murmushi akan fuskanta tama kasa cewa komi Mama ta kalleta tace “bakiso ne oya bani kayana, last month danaje clinic wata Hajiya tarabamana kudi a envelop naduba naga 20k ne shine na shiga kasuwa na siya miki crocs naga shi likitoshi kesawa a clinic dimu duka likitocin wajen shine akafansu shine na shiga kasuwa na sayomiki ashe haka takalmin keda tsada dubu takwas aka saidamin na hada miki da wannan abun gwajin nace nima y’ata tai kaman yan gayun likitocin danake gani a clinic dinmu” hawaye ne yacika idanun Rashida tana kallon Mama na bata labarin Mama takare da “nazo naboyesu nace bazan baki ba sai ranan dazakuyi resuming school” daidai lokacin hawaye ya sauko daga idanunta Mama tace “ke mehaka kuka kikemin”? Kawai rungume Mama tayi da gudu ta kankameta ahankali tace “thank you Mama thank you” shafa bayanta Mama tayi tace “gabaki dayan rayuwanki Rashida nine na cinye miki ita, bakida lokacin kanki, komi kika samu ni, kome kikeyi sabida nine, konace ki sayawa kanki abu bakiyi saisa na saya miki kema ki shiga sahun yan gayu aga y’ata fess fess akara kallonta sabida yanda tai kyau, Allah yakawo miji na gari” cikin shagwaba ta ture Mama tace “ni bazanyi aure ba Mama, bazan taba iya barinki ba” baki Mama ta kama tace “ke kodai zan kaiki gidan zumane amiki rukiya kaman me aljanu bazaki aure ba” gyadama Mama kai tayi tadauki takalminta tana budewa daga leda tace “inhar ban samu mijin dazai yarda na daukeki muje gidanshi tareba ina ganinki ina baki kulawa wlh gara na kare rayuwana ahaka” da sauri Mama tamata dakuwa tace “kinci mai garinku Rashida” dariya Rashida tayi sosai tace “wlh Mama da gaske nake bazan taba rabuwa dake ba Allah Mama” ganin Mama zatai magana yasa ta tashi da sauri tace “bari nasa takalmina” fararen kafanta ta zura cikin crocs din sun mata bala’in kyau Mama tace “Masha Allah Tubarkallah komi kema yarinyana kyau wlh, kinga kafanki aciki kuwa dudda kafan fara ba lalli amman yayi kyau” wani juyi tayi cikin takalmin tace “Mama inason takalmin thank you so much Mamaa, bari na tafi” tawuce tasa doguwan rigan data fito dashi yakamata ya nuna her flat tummy sosai da very full chest nata cus she has boobs kaman Mama, itama Mama harda rama yasa ba’a ganin nata yanzu, dan kwali ta daura tayafa gyalenta tai arranging lab coat nata a bag pack da books da stethoscope da Mama ta siyamata da komi ciki ta goya abaya tasa yar wayanta a aljihun riganta da earpiece tace “natafi Mama” Mama tace “dan Allah kici abinci kinji kada ki manta” dasauri tace “to Mama zanci, bye Mama” Mama tace “ubangiji Allah bada za’a Allah ya taimaka Allah ya tsareki Allah yakuma baki miji nagari”.

Shagon Maman Miwa taje ta gayamata ta koma school da safe zata dinga zuwa aiki, nan da nan tayi wanke wanke ta share ko’ina tai mopping after 8 tagama komi Maman Miwa tabata 2k saikuma ta bata 200 tace “kihau adaidaita kitafi makaranta baki takaba” murmushi kadan tayi tace “nagode Maman Miwa” sannan tawuce tafito MamanMiwa tabita da kallo tace yarinya ga kyau har kyau ba miji.
Chapter 12 · 0% Book details