← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 95

Sashe 24

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama takara shiru saikuma tasa hannu tadauki bowl din fruit din tarike tadauki spoon tadau lemu zatakai baki is as if akwai so many things acikin zuciyanta dake damunta tace “wlh, wlh tunda nake arayuwana bantaba fasikanci ba, inada cikin 6months ina laulayi sosai aka kaini hospital akamin gwaje gwaje the next thing inada HIV, aka gwada Mijina baida shi, kishiyata ma baidashi babu wanda ya yarda da magana ta, Mijina ya koreni, yamin koran kare, nakoma garinmu dayake dagani sai yayana iyayenmu suka haifa shima ya koreni wai bazan jamai abun kunya ba yana babban mutun a kauye karnazo naraba ma kauyensu kanjamau, haka nai garari aduniya da ciki ajikina” Tasakeyin shiruuu tana kallon bowl na fruits din tace “har yau har yau bansan tayaya nakamu da HIV ba Riyad, haryau bansani ba” saikawai tafashe da kuka dayasa idanun Riyad sukai ja yasauke kanshi kasa Mama tabashi tausayi and wlh he believed her cus you can see honestly a maganan ta, her body language, maida bowl din tayi ta ijiye tace “cikin garari na haifi Rashida, komi nawa saida na saida just to sustained bata madara dan ban bata nono ba haka likitoci suka gayamin, ina zuwa clinic lokacin da karfina nafara aikace aikace ina goyata ahaka nasata school ta taso tanada ilimi har yar baiwa ake kiranta lokacin, cikin wahala sosai Rashida ta tashi, ba gatan uba ba gatan yan uwa, just ni kadai takedashi, tun batasan menene HIV be sabida yanda jama’an unguwa ke constantly singing dinshi akanta tazo tasan menene shi, tana wajajen JSS1 karfina yasoma gasawa as small as that girl sai ita tasoma zuwa gidajen danake aikatau tanayi amadadina nina zauna agida sabida rashin lafiya tundaga lokacin kawowa yau Rashida dakake gani itace ci na, sha na, suturata, wajen zamana, magunguna na, kudin makarantan ta da komi, anywhere da zata samu aiki tayi she wants to go sabida batason taje taroki kowa yamana abu, ko an kawo mana taimako bata amsa, she’s 23 but she works like a 45yrs old man” Mama tai shiru tasa hannu ta share fuskanta chan tace “Riyad I’ve become a burden arayuwan y’ata, I’ve become a curse in her life, I believe idan na mutu she will enjoy life better….” “Mama!” Riyad yakirata da sauri, fashewa dawani irin kuka Mama tayi takalli Riyad tana bubbuga zuciyanta ta saman riga tace “I am hurt sabida I have the best daughter a duniya dabana iyama komi kawai nasata a wahala ne, I am selfish Riyad dan dana haifeta dazan iya kaita gidan marayu amman nace nizan raineta ta taso suffering, yara yammata irin ta suna gidan iyayensu akillace nawa na garari aduniya from morning to night bata airport, bata shagon abinci, bata hotel tana shara da wanke wanke da wanke bayi just to make ends meet, so I am selfish Riyad” Mama tafara sheshekan kuka da kawai kasan matan nan ta tara abu dayawa azuciyanta ne tace “na zaman ma Rashida alakakai arayuwa, na zaman mata annoba, sabida ni kullum aiki take, kowace yar budurwa na gidan iyayenta na jin dadi iya yen na nemo abinci su bata taci ni tawa ke gararin duniya ta nemo tabani naci, I’ve burden my poor daughter, I don’t deserve to be her Mother wlh I do not!!” Tashi Riyad yayi ahankali yazauna bakin gadon dan kukan da Mama take is getting too much, calmly yace “Mama don’t say that, you are wrong Mama!” Ahankali yace “kinsan yanda yarki ke sonki kuwa?” Saikuma yasa hannu a aljihunshi ya ciro handky yamika mata yace “goge fuskanki Mama nabaki labari” da kyar Mama tasa hannu ta karba ta share fuskanta tass takalli Riyad da jajayen idanunta, dan murmushi yayi just to calm her down but jiyake kaman yamata kuka shima yace “Mama all abubuwan dakike tunani akan yarki is totally wrong cus I see complete opposite of abinda kika fada” dan shiru yayi kaman mai tunani chan yace “all I see a idanun yarki is you are her motivation, her inspiration, her strength, her confident, Mama kece dalilin dayasa yarka is strong! Fearless and resilient, bold, I witness how she fought with her soul sabida ke Mama!” Dan murmushi Mama tayi ganin haka yasa Riyad yace “Mama ke kinga yanda tayi ne ai harni namiji saida na tsorata kartazo ta hada dani” daidai lokacin Mama ta kwashe da dariya yanda yayi maganan was sooo funny, ganin tai dariya yasa cikedason kwantar mata da hankali yace “Mama karki taba tunanin ke burden ce arayuwan ta ko curse all I see is kece the whole entire reason na existence nata, Mama yarki na sonki fiyeda tunaninki and duk yaran dake son iyayenshi bata taba daukansu koya kallesu a matsayin wahala kowani abu trust me Mama” murmushi Mama tayi tana kallonshi har cikin ranta taji sanyi da maganganunshi yace “idan you want her to keep being her ki warke kiji sauki sabida hankalinta ya kwanta Mama inba hakaba rashin lafiyanki will shatter her tiny little heart I’m sure ko’ina take yanzu hankalinta rabi da kwata na kanki she might not concentrate ko a school right”? Gyadamai kai Mama tayi ahankali saikuma chan tace “nagode Riyad, you made me feel good” murmushi yamata yace “kici abincin ko zakisha yoghurt”? Gyadamai kai Mama tayi freely kaman ta sanshi da dadewa kawai saiya sauka daga gadon yabude ledan daya kawo yaciro komi yakawo ajuwa dates, ruwan Zamzam babban gora dakuma yoghurt, cup ya dauka na tea da aka kawoma Mama yaje ya zubar Mama sai binshi da kallo take ta natsu da yaron kaman tasanshi da chan, yataho da cup din ya tsiyaya mata yoghurt din aciki yabata karba tayi ahankali tace “bani dabinon” dasauri yabude daya yabata ta karba yadawo ya zauna tashiga sha tanacin dabinon wlh haka ya zauna da ita sai hira suke kaman sun san juna har Dr yashigo yadubata yadan shiga hiran shima na 5min kafin yawuce yatafi wajajen zuhur yafito yatafi masallaci ana idarwa yadawo yazauna Mama tace “bakaci komi ba” cikinshi yataba yace “kuma yunwa nakeji sosai Mama tea kawai nasha dazan fito” dasauri Mama tace “tashi kaje gida kaci abinci dan Allah” zaiyi magana aka bude kofan dakin da sallama Rashida ce tana sanye dawani material ja dogon riga ne har kasa ta yafa gyale baki kayan sun mata kyau sosai ta goya jakan school abaya da pink crocs din nan akafanta sai wayanta dake hannunta tana gumi a goshi dan da kafa tazo gashin gaban kanta duk sun kwanta, ko kadan batasan zata ganshi ba ganinshi yasa ta hade rai sai kawai ta shigo ta ijiye jakanta kan kujera tazo ta gefenshi takai hannunta da sauri ta taba goshin Mama tace “Mama ya jikin meke miki ciwo yanzu”? Dauke kanshi yayi daga kallonta Mama tace “lafiya na kalau” da idanu ta nuna mata Riyad hakan yasa ba yabo ba fallasa tace “sannu” wayanshi yaciro yashiga dannawa Mama tamata dakuwa da hannu hakan yasa ahankali tace “ina yini” shiru yayi chan yace “fyn” sai shegen jiji dakai sabida yaga yanada hotel halama na babanshine ba nashi ba tafadi aranta, maida wayan yayi a aljihu yamike tsaye yace “Mama bari naje”dasauri Mama tace “nagode nagode Riyad Allah maka Albarka nagode kaji saika dawo agida Mama” “zasuji” yayi maganan yana juyawa yawuce yafita wucewa wajen wardrobe na dakin Rashida tayi taciro kudin tarike a hannu tace “ina zuwa Mama” kafin Mama takirata harta bude kofa tafita daga dakin dagudu tabishi abaya ita bama tasan sunanshi ba hakan yasa ta kasa kiranshi gashi wayanshi na kunne har parking space yabude mota ya shiga mota yana kokarin tadawa tai knocking glass din hakan yasa yasauke glass din kasa ya zubamata mayun idanunshi haka nan taji gabanta yafadi kawai saitaji muryanta ya makale, dan gyaran murya tayi kadan duk yana kallonta sannan tadago hannunta dake dauke da kudin ta mikamai yabi kudin da kallo da aka daure da lobari sannan yajaye idanunshi dagakan kudin yazuba mata manyan idanunshi still baice komiba aranta tace “amman anyi dan wulakanci anan” saikuma ta daure ganin kallon kudin me yake mata tace “150k ne nan, sauran kudin daka kashe I will pay you back small small” dauke kanshi yayi daga kallonta ya kunna motan kaman wanda akace dole yayi magana yace “keep your money ban bukatanshi” jitayi ranta yafara tafarfasa sabida yanda yayi maganan a wulakance ta kalleshi tace “nikuma ban bukatar taimakon ka ko angayamaka i need your help to take care of my mother ne”? Da kokarin yin reverse yake but jin maganan ta yasa ya dan dakata yakalleta yace “you need all the help Rashidahhh!” Faduwa gabanta yayi yanda yakira sunanta saikuma amsan daya maida mata yadawo mata wani irin sparking taji tanayi zatai magana taga yayi reverse abinshi yana kallonta yana saka wani bakin glass a idanu sannan yajuyar da kan motan yafice abinshi kaman ta kurma ihu takeji.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣4️⃣
Chapter 24 · 0% Book details