← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 95

Sashe 3

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Dudda yanajin warin bolan dayake ciki kaman zai kasheshi ga tsoron dayakeji but hakanan muryanta da yanda take wakan hold on na calming nashi down sosai, muryanta yamafi na asalin wanda yayi wakan dadi, what a voice! Tass tagama aikinta ta jingine komi inda zata jingine sannan tadauki jakanta tarufe tagoya abaya tasa hannu tabude kofan bayin hada ido tayi da maza biyu daketa sintiri awajen ta ballamusu harara tacire board na close dake gaban kofan bayin takoma ciki ta ijiye sannan ta gunguro garbage can din da kyar sabida nauyi amman ta daure tafita tafito dashi ko kallonsu batayiba saima wakanta data cigaba dayi abinta tawuce tasauka har kasa tazaga baya inda suke ijiye dattin saida ta jujjuya ganin babu kowa yasa tabude marfin bolan batare data kalli cikiba tace “you are safe yanzu you can come out” kafinma ya yunkuro tajuya abinta tahau tafiya dan sauri take is already 3:30 by 4 zata shagon abinci gashi this whole drama yabata mata lokaci, da kyar ya iya ya lallaba yafito daga bolan sai amai duk wani abu dayaci saida ya amayar dashi sai kakkabe jikinshi yake yadago zai mika mata gyalenta daidai tanashan kwana harta tafi, he wanted to say thank u dudda she’s a crazy wicked girl tana zubamai dirt tana murmushi but she helped him, hannunshi yakai aljihunshi yataba but baiji wayanshi ba kuma baisan a ina ta fadi ba wlh kuma shi bazai duba bolan nan ba, daidai wani cleaner na gunguro nashi bolan dasauri yace “please bani aron wayanka nakira” binshi yayi da kallo ganin kaman ba lafiya yasa yabashi wayanshi Munir yakira kafin yayi magana yace “Munir kazo ka daukeni a airport pls karka fadama kowa kana zuwa katambayi wajen zuba bola ina wajen” kafin yayi magana ya katse wayan yabama yaron yazauna awajen kawai feeling terribly sick kusan 1hr yana wajen jikinshi yadau mugun zafi ga tsigan jikinshi na tashi kaman zai mutu yana zaune ahaka yaji ance. “Riyad” dasauri yadago kanshi da gudu gudu sauri sauri Munir yataho wajen yace “what happened to you like this? Wat are you doing here? Why are you so dirty”? Tashi yayi yana kokarin yima Riyad magana yace “someone tried to kill m…..” kawai ya sume da kyar Munir yasamu wani cleaner yazo kawo datti shima aka tayashi daukanshi suka tafi mota aka sashi sai gida bayan yakira Mom akira Dr.

Tawani special secret gate Munir yabiyo aka budemai already ga mutane tsaitsaye Gwaggo (Mai Babban daki) gawata black beauty mata dake sanye da hijab mai dan kiba (Mom), Wambai, Waziri, Kabeer da su Halilu, Ibrahim da Shuaibu, Baffa Mujitapa dukansu suna wajen da family Dr nasu, yayi parking agurguje Munir duk sukai wajen fashewa da kuka Mom tayi tace “what happen to yarona Munir? Wakeson kashemin shi daga shigowanshi garin nan? How did they even know ya shigo? Gwaggo jini a hannunshi look, Doctor do something” Mom tai maganan tana kama hannunshi ashe wukan ta yankeshi dazu, atare dukansu mazan suka ciccibeshi zuwa wani dabkareren flat na Mom Gwaggo tace “meya sameshi haka Munir? Jibi jikinshi? Meya faru Munir”? Dasauri Munir yace “Gwaggo nima bansani ba but kaman he was attacked ne, yana kokarin fadamin wai ana kokarin kasheshi ya sume ba wayanshi taredashi, shi babu akwati, akusa dashi, awajen bola naganshi da bag pack yana mota dawani dan kwali black, kafin yafadamin komi kuma yasuma” gam Mom tarike hannunshi har daki kan wani taskeken gado aka kwantar dashi Dr yashiga dubashi yanda skin nashi da fatanshi keyin wani bororo dahar wani motsi suke yasa yace “a chanzamai kayan jikin nan nashi maza, ku goggogemai jiki with clean towel, allergy ke damunshi, he’s allergic to dirt da kazanta right from small, kuyi sauri pls” fita kowa yayi daga dakin akabar Munir da Mom, Waziri da sauran duk suka zauna a falo yace “wazai attacking yaro daga durowan shi kasan nan?” Anatse Wambai yace “call the police I think sai anbincika airport din maybe ta CCTV za’a gani” faduwa gaban Kabeer yayi amman yadaure yaranshi always do a clean job he hope bazasu kwofasashi ba, fitowa Munir yayi yace “Dr an gama” dukansu komawa ciki sukayi Kabeer sai tsaki yake aranshi shida yakeso kowa yaji haushinshi amman jibi yanda kowa ke nan nan dashi, attention yakoma kanshi ma infact, skin nashi gabaki daya yakoma so red, drip akamai fixing da allurai ciki Dr yakalli Mom datafi kowa damuwa adakin yace “anjima kadan zai farfado don’t worry” dan murmushi tayi tareda gyadamai kai Waziri yace “ki zauna dashi” Gwaggo tace “nima ina nan kome za’a kawomai kowa zaizo yadubashi saina ganshi inga uban waye keso ya cutar mini da jika, bangama kukan mutuwan d’ana ba yanzu halakamin jika za’ayi wlh jinina yasha karfin kowa” kallon Munir Mom tayi ahankali tace “thank you Munir” gyadamata kai yayi yawuce yafita daga dakin hakan yarage daga Gwaggo sai ita, dafata Gwaggo tayi tace “ki tsare yaron nan ki dage da addu’a akanshi, tun ranan da aka haifi Riyad akace yanada taurari masu kyau kuma babban mutum ne shi, kiduba kigani yaran marigayi maza shidda amman shi kadai akeso ahalaka tun yanzu kenan bama asan waye zai gaji kujeran sarautan ba kenan amman so ake akasheshi balle kuma ace shine zai gaji sarautan ki tashi tsaye Maryama, saikin tashi tsaye, kinyi zaman gidan nan basai na fadamiki hadarorin dake cikinsa ba, inde kalubale ne yanzu Riyad yafara gani, idan kuma yazama Sarki yadinga ganin kalubale iri iri kenan har abada, ki tsare yaron nan, kizama idanunshi kunnuwanshi uwa uba kizama inuwarsa dakuma lullubinsa” gyadama Gwaggo kai Mom tayi takama hannun Riyad tarike gam tana kallonshi tace “Gwaggo meya musu Riyad dako zaman gidan nan baiso, na tabbata baimason ya gaji kujeran nan, dan bata gabanshi” Gwaggo tace “kwarai” Mom tace “shi kadai Allah yabani, shi kadai gareni, Riyad kadai Allah yabani yau ana kokarin rabani dashi” kankame hannunshi tayi tace “Gwaggo zan iya zuwa bangon duniya sabida Riyad! Kuma nayi alkawari duk Wanda yace zai cutar da yarona saidai yafara dani dan daga yanzu zan zama shamaki tsakanin Riyad da komi na duniyan nan, zan zama inuwa hazo zan lullubeshi nakuma kareshi daga duk wata hari” sosai Gwaggo take kallonsu sai kawai tai murmushi tadauki charbi ta tacigaba da ja itama bini bini tana tofama yaron addu’a aka.

💫 SANYI DA ZAFI 💫
EPISODE 3️⃣
✍🏻M SHAKUR
Chapter 3 · 0% Book details