← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 95

Sashe 45

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mama na ganin an shafe Fatihan daura aure sai kawai tajawo Rashida ta rungumeta tana wani irin emotional kuka bata taba sanin Allah zai nuna mata auren yarta Rashida haka ba, itama Rashida kuka take she can’t believe ita aka daurama aure just now, wai yanzu tazama matar Riyad? Dreaming takeyi ne, tasowa Buba yayi yazo wajen su yace “kidena kuka shi ciwo na Allah ne, hakama waraka ta Allah ce, komi yayi zafi maganinsa Allah, Allah zai baki lpy kinji” gyadamai kai tayi ahankali Mama tana sakin Rashida tace “Riyad” zuwa wajen yayi yadan saci kallon yanda Rashida ke sharce hawaye Mama tace “nagode Riyad!” lumshe idanu yayi, Buba ya juyo ya kalli Rashida dake kuka sosai sai kawai yaduka agabanta hannunshi yakai yakama kuncinta hakan yasa Rashida takalleshi da jajayen idanunta, cikeda wani irin tausayin yarinyar da kaunarta dayaji Allah yasamai hakanan yace “dena kuka Allah zai bawa Mahaifiyarki lafiya kinji” gyadamai kai tayi ahankali cikeda kunya ganin tsoho dashi ya duka agabanta, murmushi yayi mata yasa yadauki byro daya gani akan table na Dr Bugaje yace “dan tsammini takarda Docta” paper Dr Bugaje tabashi rubuta number shi yayi yabama Rashida yace “duk randa Riyad yamiki wani laifi, koya bata miki rai, call me zanzo har gidanku na sabamishi, saina ciwa mijin naki mutunci” akunyace ta sunnar dakai Mama tai murmushi sosai Buba yace “karba” ahankali Rashida tasa hannu ta amsa sannan yatashi yakalli Munir yace “muje ka maidamu gida” dasauri Riyad yace “zan maidaku Buba” kallonshi Buba yayi yace “stay da iyalanka kabar Munir ya kaini” wani iri Rashida taji jin ance iyalanka shikuma Riyad saiya gyadamai kai suka wuce suka fita nurses sukazo suka wuce da Mama aka fita da ita, ganin Riyad har lokacin tsaye a office din itakuma Rashida takasa mikewa sai hawaye take gogewa yasa Dr Bugaje ta tashi itama tace “bari na bisu” gyadamata kai yayi tawuce tafice ganin haka yasa itama Rashida ta tashi da sauri tazo zata fice kawai taji yakama hannunta, mugun faduwa gabanta yayi da saida ya lura dasauri ta kalleshi hada idanu sukayi yamata wani irin kallo kaman baimasan yarike hannunta ba gently yace “who is that guy”? Yanda yamata maganan yana kallon kwayan idanunta dasuke ajike yasa takasa jure kallonshi takasa magana, dan jawota yayi sabida yanda take so light this days kawai ta taho dab dashi gabanta nafaduwa sosai mehaka yake mata, cikin whispering voice yace “me tsakaninku”? Heart dinta na racing sosai tace “bakomi classmate dina ne” “mesa yakawo miki kudi?” Dan kallonshi tayi yanda yau yake kallonta saitaga kaman ya banbanta da yanda yasaba kallonta ada, sake sauke kanta kasa tayi tace “nayi seeking help a group namu for Mama” hannunshi dake free ya mikamata yace “your phone” dan kallonshi tayi saikuma ba musu tasamai wayanta a hannunshi ya karba a aljihu taga yasaka wayan nata ahankali yace “the next time he approaches you tell him someone owns you now! And that person is Me!” dago kanta Rashida tayi da sauri ta kalleshi yanda yake maganan kaman yaci wani competition saikuma ta gyadamai kai yace “zanje and get you food and clothes you need to shower and change” sake gyadamai kai tayi takosa yasaki hannunta dataji yana mata kaman shock, ahankali yasaki hannun yace “let’s go” tare suka fito har zuwa ICU Mama da Mrs Bugaje dake tare duk suka kallesu murmushi Mama tayi Dr Bugaje tace “congratulations Mama, Allah ya sanya albarka, Mama yanzu saiki kwantar da hankalinki ayanda nake ganin yaron nan Riyad he will protect Rashida no matter what so dan Allah kiji sauki BP ki ya sauko” gyadamata kai Mama tayi tanajin wani karfi da lafiya na shiganta.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣8️⃣

Gyadamata kai Mama tayi cikeda farin ciki dudda maganan ta baya fitowa da kyau tace “Alhamdulillah Mrs Bugaje wlh ina cikin wani irin farin ciki da bazan iya misalta miki shi ba” murmushi tayi.
Wucewa Riyad yayi yatafi yabar Rasheeda awajen, fitowa Mrs Bugaje tayi takalli Rasheeda tace “scrub in kije wajen Mamanki” da sauri ta taso tayi cikin ICU din bayan tasaka abubuwan Mama na ganinta cikeda karfin hali tasa hannunta asaman hanci tace “ayiri…..” saikuma tahau tari da sauri Rashida tazo wajen tace “Mama stoppp” ijiyan zuciya ta sauke tace “Rashida kinsan yanda nake murna kuwa naga aurenki Alhamdulillah kinga na warke tass kalli kafafuna harsun soma sakewa” kafafun Rashida takalla saikuma takalli Mama yanda taketa murmushi is not like tanason auren nan, infact ita bamata taso da burin tai aure ba sannan one single feeling batada shi for Riyad kawai dai daga jiya saita fara kallonshi ta fuska daban compare to before data tsaneshi, jiya ta gane Riyad shi mai sonsu ne ba kyamatan su ba, yana kula da Mama, shine the first person that genuinely know them kuma yasosu ahaka sannan ya tsaya musu, kallonta Mama tayi tace “me mijin naki yace? Ina yaje”? Dasauri ta kalli Mama jin kalman mijin yamata wani banbaran, murya chan kasa tace “wai zaije yakawomin kaya da abinci nai wanka” wani irin blushing da Mama keyi saida Rashida kawai ta maida Mama tv tana kallo is this aure of a thing yakesa Mama farin ciki haka ko wani abun ne dabata sani ba to wani abuma? Is just auren nan, sai murna Mama keyi. Wajajen 4 Riyad yadawo tareda Munir dake rike da basket na abinci shikuma yana rikeda wani paper bag dan babba Mrs Bugaje ta kallesu tace “yauwa I was waiting for you to come inaso na maida Mama wani daki kodan this big occasion she seems very happy, her biggest fear and worry is yartane yanzu data damka maka ita kaman 90% of matsalanta sun tafi” anatse Riyad yace “I prefer private single room” gyadamai kai Dr Bugaje tayi tasa Nurse ta gunguro Mama daga dakin tana fadamusu dakin da za’a kaita, dan satan kallon Rashida Riyad yayi dayaga idanunta sundan soma sabewa, first floor aka kaisu wani single room mai kyau da komi ciki akai connecting Mama da machine na zuciyan still sannan Nurses din suka fita ijiye abincin Munir yayi shikuma Riyad ya kalli Rashida tareda bata bag din, dan kallonshi tayi saikuma tasa hannu asanyaye ta karba murya chan kasa ta yanda dagashi sai ita zasuji maganan yace “shower before I come back, zanje mosque” gyadamai kai tayi suka wuce mosque Mama tawani yunkuro ta tashi kaman maison gulma tace “zonan mugani meya kawo miki? Imaza jeki wankan ke to karya dawo ya ganki daka daka” kallon Mama kawai Rashida take with a huge suprise kaman ba Mama ba, farin cikinta yaki boyuwa, bag din tamikama Mama, Mama ta zazzage tana fito da abin ciki tana washe baki sosai abaya ne kala uku acikin jakan duka black black amman sun hadu duba tsayinsu tayi taga 58 wlh tsayin yarta, sai cream dakuma wasu lafiyayyun turare guda biyu, daya cikin abayan Mama tazaba tadauka tabata tace “ungo wannan zakisa jeki wankan, ki chanza breziya da wando kuma, akara wanke baki ba kyau miji yaji wari” sokoko Rashida ke kallon Mama wai ba Mama ce mara lafiya ba take maganan wani miji? Ita Mama tadauka ta Riyad take she’s just after her taji sauki kawai shine burinta, just to make her happy ta karbi wanda ta zaba mata tawuce, akwatinsu tabude tadauki bra da pant tashiga bayin dakin that is very neat tai wanka ta shirya tai alwala tabude turarukan ta fesa wow saida ta lumshe idanu sunada wani irin feminine scent mai dadi, yafa gyalen tayi akai tafito Mama ta bita da kallo sabida yanda yarinyarta takoma tsaf kalan yar masu kudi tai murmushi itakuma ta shimfida dadduma tai salla Mama tace “zoki zubamin abincin bikin ki” dasauri ta juyo ta kalli Mama dake murmushi sai kawai ta tashi tawuce tadauki plate tana bude warners din ta debama Mama tuwo tazauna gaban gadon tana feeding Mama ahankali tace “Mama ai kin warke ko?” Gyadamata kai Mama tayi tace “na warke tass bakiga inacin abinci ba” murmushi tayi tace “thank you Mama dakika warke” tana cikin bata abincin suka shigo dakin duk yanda Riyad yaso ya daure karya kalleta kasawa yayi baitaba ganin abaya yama wata kyau kaman yanda yaga wannan yama Rashida kyau ba, dudda Mama bata cinye tuwon ba but taci rabi, sai satan kallon yanda Riyad ke kallon yarta take kaman tace yadauketa su tafi kawai dai dan rashin lafiya ne, Mama tace “deba kici kema” girgizama Mama kai tayi alamun bazata ci ba, Mama tace “Riyad kaga yarinyar nan batason cin abinci fa wlh sai kayi da gaske” murmushi Munir yayi duk suka zazzauna tareda Mama har magrib sannan suna tafi.
Chapter 45 · 0% Book details