← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 95

Sashe 65

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

EPISODE 56
Dasauri Rashida takalleshi jin abinda yafadi saikuma ta dauke kai takasa magana, cikin dan kakkausan murya yace “nima bawai inayi bane cus i want to do nope, as long as igiyoyin auren mu are intact you’re my responsibility and dole na cika hakkokina dake kanki you are too small kisa Allah yakamani” dasauri tadago kanta ta kalleshi wani shu’umin kallo ya zuba mata yace “get in cus I don’t want to ever force you kiyi wani abu, this is hakki akaina!” Abu tahadiye awuya kaman ta shakeshi ta fizge hannunta da karfi tanaji kaman ta kurma ihu cikeda taurinkai tashiga bayan motan ta zauna kaman bataso ta shiga, driver dake wajen gate yataso dasauri ganin ta shiga ga mamakinta gani tayi yashigo bayan shima dasauri ta kalleshi danta dauka agaba zai zauna, gyara zama yayi sai kamshi mai bala’in dadi yake, matsawa tayi chan karshe da sauri driver na zuwa ya duka yace “Barka da fitowa Ranka shi dade, Allah ya taimakeka, Allah ya karamaka daraja!” Gyadamai kai Riyad yayi ahankali, driver yasake dukawa yace “barka da fitowa ranki shi dade uwar dakina” juyo da kanta Rashida tayi haushin Riyad yasa tawani ballamai harara, da hannu Riyad yamai alamu ya rufo musu kofan, rufowa yayi yakoma ya shiga gaba yatada motan sukabar gidan sundan shiga hanya chan Riyad yace “what time zaku gama?” Kaman bada ita yake magana ba tai banza dashi, anatse yace “ban baki izinin hawa any form na abin hawaba, I asked you wat time zaki gama?” Yayi maganan yana zubamata idanu kaman bazatai magana ba chan tace “nima bansani ba” authoritatively yace “mukaje zaki shiga ciki ki duba roaster and call me ki sanar dani, i will send my driver ya dauko ki” cikin fushi tace “ko an tashi inada wajen zuwa?” Ahankali yace “where?” Shiru tayi tai banza dashi unexpectedly kawai taji ya fizgota ta taho jikinshi lokaci daya hannunshi yasa kan waist nata yarike gam, arude ta kalleshi jin yanda yakama mata kwankwaso hada idanu sukayi kawai taji gabanta na mugun faduwa sabida yanda yake mata wani shu’umin kallo takasa magana sai kokarin kwace kanta datakeyi takasa tana numfashi da sauri da sauri, hannunshi akan waist nata kaman shock, strictly yace “next time idan namiki magana open mouth ki bani amsa” yadanyi shiru kadan yana kallon fuskanta kaman yau yafara ganinta kafin yakara pressing waist nata dayaga tawani zabura yace “ina zakije after school”? Wlh she’s breathing way to fast sabida yanda take kan jikinshi ga wani irin abu da hannunshi kema waist nata, ga driver na tukasu kuma babba ne driver ba yaro ba, kunya ma taji tanaji kaman ta shige kasa batasan sanda tace “saloon zani nai kitso 4 zamu gama” yana kallonta yace “bazaki je ba!” Da sauri ta kalleshi dudda gabanta na faduwa saida ta turomai baki cikeda stubbornness, lips dinta yabida mayen kallo yana tuna randa yayi kissing nata dasauri yazare hannunshi daga waist nata hakan yasa tasauka daga jikinshi da sauri takoma waje ta zauna har lokacin kirjinta bugawa yake har sukakai school babu wanda yasake magana Riyad yace “ina zamu ijiyeki”? ahankali tace “gynae” har gaban department din sukaje sukai parking dasauri tashiga kiciniyar bude kofan saikuma ta tsaya chak takasa magana duk yana kallonta ahankali yataho wajen mannewa tayi jikin kujera kallonta yayi suka hada idanu dasauri yadauke
Tadauke kanta cikeda jin haushin shi tarasa mesa gabanta ke faduwa ahankali yasauke hannunshi daya kan cinyanta da sauri ta kalleshi hada ido sukayi hannun nakan cinyanta yana kallonta bayama kiciniyar bude kofan ture hannunshi tayi da sauri hakan yasa yakoma ya zauna wajenshi chan yace “open door for her” Dasauri driver yace “to Yallabai” haushi Rashida taji yakamata wato da gangan yahana abude mata bude mata akayi tajuya da sauri zata fita karaf taji yarike hannunta da sauri tajuyo ta kalleshi yana kallon cikin idanunta yace “today should be the last day dazaki bar gidana bakiyi breakfast ba” haderai tayi hannu yasa a aljihunshi yaciro kudade dabaisan yawansu ba zai samata a hannu azuciye tace “ni banson kudin ka karike kayanka, Allah kyauta” hannunta yabude da karfi yasa kudin a tsakiya yace “hakki nane na ciyar da matata! U can trash them kika fita idan kinga dama but dai use it eat” yana maganan yasaki hannunta zata ijiye kudin kan kujeran azuciye yace “kika ijiye kudin nan bazaki school din nan ba saikin deba kin tafi dasu” sosai taji ranta na baci ganin zai samata bakin ciki yasa kawai tajuya fuuuu tafice rikeda kudin a hannu ta shiga department dinsu.
Chapter 65 · 0% Book details