← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 95

Sashe 46

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau kwanan Mama 3 a hospital she’s recovering like magic tun jiya sukai resuming amman kiri kiri taki zuwa taki maganan ma sabida kar Mama tace ta wuce tatafi, tana zaune tareda Mama around 8 na safe Mrs Bugaje tashigo dakin ganinta tareda Mama yasa tace “ba some of yan class naku naga a A&E ana wardround dasu ba? Wani department kike this week?” Ahankali Rashida tace “Gynae” hararanta Mrs Bugaje tayi tace “my friend stand up and go” Mama tace “wai dama sun koma?” Mrs Bugaje tace “tun jiya ma taki zuwa” dakanta Mama tayi abaya bada zafi sosai ba tace “wuce kafin na saba miki” tashi tayi tawuce wajen drawer daki tadauki jakanta taciro gogaggen lab coat dinta, daya daga cikin abayan da Riyad yasaimata ne ajikinta hakan yasa ta warware gyalen tai rolling aka sannan ta warware lab coat din tasaka tadauki stethoscope nata pink ta makala a wuya tadauki pink crocs nata tasa sannan ta dauki turaren ta fesa, tunda tana asibiti yasa bazata dauki jaka ba, pen ta dauka ta makala a pocket nata sannan tadau wani dan jotter tasa a aljihu, earpiece nata ta dauka zatasa a pocket ta tuna haryau Riyad bai bata wayanta ba kuma takasamai magana ahankali ta maida ear piece din jaka ta rufe, ta rufe wardrobe din sannan tajuyo takalli Mama da Dr Bugaje ke dubawa tace “natafi” “adawo lafiya Amarya” dan turo baki tayi tana kallon Mama sannan tabude kofan tafito tafara tafiya tawuce staircase daidai ta sauka kasa Riyad na zuwa wajen hada ido sukayi yana sanye da wani jumper dark brown daya haska fatanshi yasa bakin glasses a ido, ranan nan Mama tagayamai tanaso ya tsaya akanta tagama karatunta na likita hakan yasa yasan yes she’s doing medicine but today is the first time yake ganinta cikin kayan dake nuna ita likita ce, ahankali yakai hannunshi ya zare glasses daga idanunshi yazuba mata mayun idanunshi, da sauri tasauke kanta kasa gabanta na faduwa azuciyanta tace bantaba ganin wanda baya kunyan kallon mace irinsa ba, murya chan kasa tace “ina kwana” batare daya amsaba koya dauke ido akanta ba yace “ina zaki?” Ahankali tace “department namu munyi resuming” yana kallonta still yace “which department” da dan kankanuwan murya kaman ba Rashida ba tace “this week ina outpatient department a gynae” gyadamata kai yayi yace “let’s go” dasauri ta kalleshi but haryayi gaba hakan yasa tabishi suka jera har ward dinsu yabita sannan ya tsaya yace “go” agabanshi tawuce tashiga consulting room 2 yadan jima tsaye saikuma yajuyo.

Mama na zaune ita kadai tai shiru tana tunani though good tunani yau take akai knocking kofan tareda sallama daga ciki tai murmushi jin Riyad ne tashigo “shigo d’ana” bude kofa yayi yashiga yana murmushi yawuce wajen gadon yaja kujera yana zama yace “you look good Mama, ya karfin jikin?” Murmushi tamai tace “Alhamdulillah ya iyalinka?” Ahankali yace “Alhamdulillah Mama” murmushi tamai tace “ka kwatanta adalci kaji, mata munada kishi dan haka ka lallashi matarka da kyau kaji Riyad” gyadamata kai yayi yace “toh Mama” cikin farin ciki tace “kaga nasoma samin sauki sosai ana sallamana muka koma gida sai afara shirye shiryen bikinku ko sabida Rashida ta tare gidan ka” gyadamata kai yayi feeling happy ganin how excited she’s with the whole wedding yace “Mama kome kikeso haka za’ayi” wani irin murmushi tayi harda dan kyalkyala dariya kadan tace “inaso ama Rashida lalle a hannu amata kwalliya saikuyi hoto kubani amaidashi frame nasaka a falona ina kallonku kullum” dan murmushi Riyad yayi yace “to Mama haka za’ayi” murmushi tayi sosai saikuma tace “tayani daga gadon na zauna” tashi yayi ya taba botur din dake dago gado gadon yataso Mama tai kwanciyan zama ya gyara mata bargo sannan yakoma ya zauna ganin tai shiru tana tunani yasa yace “tunanin me kike kuma Mama?” Ahankali tajuyo takalleshi cikin dan damuwa kadan tace “kana gani nakira mahaifinta na sanarda shi an daurama yarshi aure?” Shiru Riyad yayi, dan murmushi Mama tayi ganin baice komiba tace “I put you in a tight spot ko? Kona kirashi ma bazan sameshi ba yayi blocking dina tun lokacin amman nakan turamishi sakon waya duk ranan birthday Rashida na gayamai yarshi ta shiga shekara kaza kaza dakuma lokacin dataci jamb taci UTME aka bata admission medicine na aikamai sako amman haryau bansan ko yana ganin sakona ba ko baya gani ba” ijiyan zuciya ta sauke takalli Riyad tace “bari nabaka labari na yau Riyad”.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣9️⃣

Ahankali Mama tace “ni yar jigawa ce, anan kauyenmu yake ance kakan kakana daga Morocco yake wai saisa mukeda haske, iyayenmu dani da Yayana Sama’ila suka haifa, iyayena nada gonaki da dama a kauyen mu, Babana is a very very big farmer har su CNN sunyimai interview, banda nashi gonakin yanama mutane managing gonaki kaman gonakin sarkin kano nan marigayi Baba Ali naji yarasu, Allah ya jikanshi da rahama” Ahankali Riyad yace “Ameen” yana kallon Mama jin she just mentioned Babanshi, Mama tace “dudda a kauye muke Babana yasani makaranta yace yanaso na zama yar jarida nima namai interview wata rana, yayana Sama’ila shi baiyi boko ba tare suke komi na gona da Babana, kauyenmu ba school wani next village yakesa yayana Samaila na kaini makaranta kullum a machine dinsa saina dawo da dakaina” tai shiru tace “ina JSS 3 akwai wata rana nazo gida naga wasu maza guda biyu sunzo gidanmu na gaidasu natafi dakin Mamana, so daga bayane Baba kecemin ai sarkin kano ne da kaninsa Al Mustapha sunzo wajen Baba, nace Baba ina doki bangansu da kayan sarakuna ba, to alokacin nasan ashe sarakuna na private outing suyi normal shiga kaman kowa, gasu basu wani girma sosai ba Babana ya girmesu duka dan yadan manyanta, bayan kwana biyu Baba yacemin Kanin sarki na sona” Mama tadanyi murmushi tana kallon wani zoben dake hannunta tace “kafin kace me haka akamana aure anan kauye aka tafi dani gidan Sarautan Kano”.
Wani irin kallon Mama Riyad keyi to be honest besan Mama ba, dudda yasan labarin lokacin auren anata cewa Baffa yakaro aure daga kauye and Baba supported him shiyamai auren, shida baison shiga mutane, banda hakama yawancin idan zakaga matayensu da Alkyabba zaka gansu unless you’re very close to them ko kana zuwa bangarensu you hardly knows fuskansu, ko first wife na Baffan su is because tana zuwa wajen Mom akai akai yasa yasan ta daba hakaba dabai santa ba. Ahankali Mama tace “Riyad even though Mujitappa Baban Rashida yayi hurting dina deeply bazan taba iya ignoring the fact cewa that Man loves me and care for me kaman ba gobe ba, bai bar kowa ya hantareni ba, dakanshi yake koyamin etiquette na gidan Sarauta da sauransu, yasa aka cigaba da koyamin karatu a gıda, ya kuladani Riyad bai bar kowa yayi hurting dina ba hatta Jummai kishiyata” tadanyi murmushi tace “ance tana kishi dani alokacin sabida bata haihuba then nikuma bayan bayan 1yr da aurenmu saiga ciki watan cikin daya ajikina nafara ciwo sosai da saida aka kaini asibiti lokacin anmin all test but banda HIV banda komi nadawo gida yacigaba da kuladani yana nan nan dani itama Jummai surprisingly tana kula dani, tadena min kallon kishiya, she was so happy then zan haifa musu Baby” Mama tadanyi shiru kafin ahankali tace “ina around 5month Baba na da Mama na sukai hatsari a motan dazai kawosu Kano dubani, kawai abin yakara birkita jikina ina shiga 6month nai landing hospital ciwona was serious dahar ICU aka sani cus banajin magani, banci bansha na rame kaman tsinke, akamin test dayawa the next thing was inada HIV!” Mama tai shiru tareda fuzar da iska idanunta yayi ja tace “imagine ina around 1-2 months da ciki anmin all test ba’aga HIV ba ina 6 months da ciki ace inada shi dole Muji ya yarda maza nakebi da cikina da aka fadamai inada HIV, an sashi yazo yayi test din shima da matarshi Jummai sukayi su negative abinda yasa yasake yarda da zargin inada HIV sabida laulayin ciki yasa babu abinda ya shiga tsakanina dashi tundaga watan farko harna 6 din nan cus bana iya komi Riyad mugun laulayi nayi” Mama tai shiru tace “haka nadanji sauki aka sallameni yatafi dani gida naje na samu an kira yayana Sama’ila an tara jama’a a fada dan Muji bai iya fushi ba” ta share fuskanta chan tace “koran cin mutunci, koran toxarci, koran tijara akamin agaban kowa ana nunani ana shiga barayina bayi na watso kayana waje wai sabida cikin nema ba’amin duka ba aka korani no one! No one Riyad, Babu wanda a masarautan nan ya tsayamin ba mai Martaba Baba Ali ba! Ba mai Babban daki ba! Ba sauran matan sarki ba! Babu ne kawai aka koramu ni da Sama’ila ana tunkudani” runtse idanu Riyad yayi Mama tace “munafita daga fada Sama’ila yahau zubamin Allah ya isa bai yafemin ba wannan tijaran dana jamai da cikina ina fasikanci karna sake na bishi, Riyad haka yatafi ya barni dan uwana na jini biyar babu a hannuna ni da aka sallameni daga asibiti da safen ranan, nahau tafiya a hanya yunwa menene menene naje wani gidan abinci na wanke kwanuka na kusan kwana goma sannan natara kudi natafi kauyenmu nan ma Samaila yace ban isa na zauna ba, bashi bani nace to araba gado abani yace yaji haka yaraba yabani miliyan biyu nadawo nazo ina neman gida ahaka na sami gidanmu dakake gani nasaya akan miliyan daya agine ahaka nasai yar katifa nadan natsu nafara tunanin rayuwan to me yafaru? HIV Taya zan samu? Banda Mujitapa babu namijin daya taba rikemin hannu aduniya sai Babana da Yayana.
Chapter 46 · 0% Book details