← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 95

Sashe 38

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zama Mama tayi tai shiru ita kadai awajen Allah kadai yasan tunani tunanin metake bini bini tasa hannu ta share hawayenta dayake zubomata, ruwan dabatasha kenan ba, har wajen 12 na dare ita kadai, sannan ta tashi da kyar tawuce tayo alwala kanta kaman zai cire tashiga daki tadauki pure water tasha sannan tahau dadduma azaune tai sallan tana idarwa tashiga uwardaka akasa taga Rashida na bacci ko hijabi bata cireba tsabagen fitina, zama tayi wajen ta yaye skirt na jikinta tadauki ledan ta ciro man shafawan daya siyo Mama tai shiru tana kallo saikuma ta kalli fuskan Rashidan ahankali tace “stop this madness and see Riyad Rashida, is because you’re hurt abin yakara batamai rai yake miki fada not just sabida ni kadai” dan murmushi kadan Mama tayi tace “he’s romantic” saikuma takai hannunta saman bakinta kaman mainin kunya tace “ke Zainabu” budewa tayi ta lakato ta shafa mata maganin a kafafunta sannan ta ijiye maganin saikuma tai tagumi tana kallonta addu’a kawai take Allah yarage mata zafin zuciya da yawan fushi din nan kar watarana fushi yasa tai kisan kai yanda ta watsar da matan nan biyu dazu ga jini a goshinsu Mama ta girgiza ainun batasan Rashida tayi nisa hakaba.

Har asuba tayi Mama bata kulle idanu da sunan bacci ba.

Ahankali tabude idanunta jin an tabata ganin Mama sanye da hijabi tai alwala yasa ta tashi zaune da sauri ahankali tace “Mama” kallonta Mama tayi saitai shiru bata amsaba kaman irin da abin ta kwana hakan yasa tafashe da kuka mai karfi tace “Mama dan Allah kiyakuri ki yafemin bazan kara miki rashin ji ba, kome kikace nayi zanyi, Mama everything is my fault, danaji maganan ki dakikace nabari nabarsu munshiga dakin da duk haka bai faru ba, Mama da mota ya kadeki dame zan gayama Allah”? Yanda take kuka wlh saita baka tausayi Mama taso yau ta shareta Amman saitaji bazata iyaba saita zauna tace “kimin shiru” tsagaita kukan tayi tana kallon Mama da rinannun idanunta, ahankali Mama tace “yawan fushi nasa kai abu da dama dazakai nadama Doctor” cikin raunin murya tace “Mama u hate that woman, I hate mijinta, I hate entire family nasu, those people made you suffer all your life har yanzu kuma basu barkıba” Mama na kallonta tace “idan zaki bimin hakki na ne then kiyi focusing a school, ki gama school ki zama wani abu, ki nuna musu cewa Mamanki dasuka wulakanta ta haifoki diya me albarka me goshi, ki zama Dr tukunna and cure me kinji kidena fada da mutane akaina focus on goal naki nan gaba na warke no body can troll me right”? Gyadama Mama kai tayi Mama tace “bansan ko zamuyi rayuwa tare har karshe ba babu wanda yasan gobe ke babu wanda yasan anjima ma, idan bana raye kikai wani abu who will protect you and stand by you? Ayau dudda banda wani abu but at least I use strength dina na shiga gari ina neman wanda zai taimakeni ya tsayama diyata but randa bananan fa? Who will fight for you and stand by you? Lokaci yayi dazaki bar halin nan, ke kadai gareni kene komi nawa if something happens to you I die, jiya I was so scared…..” saikuma tafashe da kuka dayasa Rashida ta rungume Mamanta da gudu tace “Mama it’s okay bazan kara ba kinji, I’m here now I’m fine kinga kafan ma naji ya warke tass” ta shilla kafan sama Mama tace “maganin da Riyad ya siyamiki ne” haderai tayi da sauri tace “Mama wlh na tsaneshi baida kirki niyake gayama zai rabaki dani yana kirana selfish daughter” ahankali Mama tace “he did the right thing, kuma kika dameni zan bishi dagaske, Allah yamai albarka daya miki fada, naji dadi da akwai wanda zai iya miki fada haka kiyi shiru dan gani kike kaman kinfi karfin kowa” tashi tayi sabida bataso tace wani abu tasake batama Mama rai kawai tawuce tafita.

Alwala tayo sai yanzu ma ta Tuna ki ruwa batasha ba jiya to waka yasha? Har Mama ma batasha ba Tana salla tafita tea tahada musu sukasha sannan takaima Mama ruwan wanka tadawo tadawo ta gyara gidan ciki da waje tsaf Mama tace “zoki wanka karmu rasa sallan idi idan muka dawo mayi girki”.
Wanka awuce tayo tadawo atampanta na salla data karbo fara wajen dinki ta warware skirt da riga ne blue pink atampa ne tasaka da sabon bra da pant tayi kyau sosai dudda batai lalle ba daman jiya sukace zasuyi but Allah bai nufa ba, ta daura dan kwali Mama tace “zauna kisa kwalli ki shafa jan baki kodan darajan yau salla” batai musu ba tazauna tajawo basket na kayan kwalliya tadauki kwalli tasaka tadau wani pink tsohon jan bakinta ta shafa ta gyara gashinta wanda shi ta wanke abayi yanzu da safen nan ta shafa mai ta taje tai parking sannan ta daura dan kwali ta fesa turare ta tashi sai Mama dake kokarin sa hijabi tabita da kallo batasan lokacin datace “tubarkallah Allah ubangiji ya nunamin aurenki haka kici gayu kısa kayan amare” turo baki tayi taki amsawa tadauki pink hijabin data dinko na salla tasaka ta dauki dadduman su da yar wayanta suka fito rufe gidan sukayi da kafa sukaje masallacin ana salla ana kaiwa sujud Mama tashiga rokon Allah yabama Rashida mijin dazai sota ya tsaya mata yakuma kula da ita, sallamewa akayi suka wuce kasuwa kaji guda biyu suka sayo da kayan Miya da fulawa dasu butter sannan suka shigo keke suka tafi gida suna dawowa ta shiga kiciniyar hada gawayi dan daura abinci ganin gawayinsu saura kadan gashi tasa abinci a wuta yasa tarike kudi a hannu tawuce zaure dan neman yaro ta aika makotansu yakawo mata gawayi, tana sakai awaje karaf suka hada ido da Riyad daya bude kofa yafito daga cikin mota yana sanye da manyan kaya da babban riga da hula bugawa kirjinta yayi sabida yanda yayi kyau na bala’i, sai kawai ta tsaya chak ita takasa komawa ciki ita takasa motsi ita takasa daina kallonshi, har saida shi yadauke kanshi daga kallonta akufule yace “kifito yan duniya suga kwalliyan sallan da kyau!” Runtse idanu yayi dan baisan ya akayi maganan tafito daga bakinshi ba, saikuma yahade giran sama da kasa yajuyo yamata wani irin kallon da kawai taji tajuya da sauri takoma cikin gida kirjinta na bugawa dim dim dim chan sai ga sallaman yaro yashigo da kwalin kaji yace “gashi wai inji Riyad aba Mama” afadace Rashida tace “Kai maidamai kace batanan” yaron yace “ai yashiga mota yatafi” ranta taji yabaci daga daki Mama tace “ijiye zo ga tukuici” dasauri yaron ya nuna new 1k note dake hannunshi yace “ai yabani dubu daya” yajuya yafita abinshi, hijabi Rashida ta dauka tasaka tafita ganin bayanan yasa ta shiga makota tasayo gawayi tana dawowa taga Mama tacire just 3 acikin kajin da an gyara but ba’a yayyanka ba tace “dauka sauran kikai gidan Baba Liman kice kawo mana akayi karsuki karba” batai musu ba ta dauka tawuce takai a zaure tahadu da Liman yace “jiya naje kauye saida nadawo naji abinda yafaru Allah kiyaye gaba ki gayama Mamanki zan shigo anjima da yamma” gyadamai kai tayi tawuce ta koma gida lafiyayyen girki tayi tai dambun naman kaza ta soya some tai pepper chicken da some, tai jellof rice tai cincin around 4 tagama komi ta shiga daki ganin Mama duk bata wani cicciba yasa tace “Mama baki ciba” ahankali Mama tace “kaina kedan ciwo anjima ya sauka zan sha” kallon Mama tayi saikuma ta zauna kusada ita tace “Mama kedai sabida ina chan ina aiki ne yasa bakiciba, bude bakinki kiga” ta deba rice din takai bakinta dan murmushi Mama tayi tabude ta karba just to make her smile ta yarda taci amman ko taste bataji na abincin ba.
Har isha’i hira sukeyi around 9 tai bacci awajen Mama tabita da kallo sannan ta lallaba ta mike tana dafa bango kujera ta dauka da buta tawuce chan bakin makwarara amai ta kwara sai ijiyan zuciya takeyi ta wanke fuska tadawo daki kafafunta ta kalla da tun dazu da rana sai zugi suke mata gashi ta lura sunata kumbura, yanzu ma sun karu sai kawai ta zauna tai tagumi tana kallon Rashida damuwa da fargabanta data shigane yasa kawai taji jikinta yanaso ya rikice haryakai ga abinci ma bataso, tunani take, takasa manta maganan Jummai, dudda tahana Riyad karyay involving kansa a case din tasan yanda aka ciro Rasheedan nan that woman will find a way ta cutar da Rashida Alkawari ne wannan! She’s just scared for yarta, idan tafita school aka dauketa fa? Idan aka halakata fa? Idan tasa akama Rashida wani abu fa? Wat if she set Rashida up yanzu ta yanda zata tura mata yarinya prison inda ko Riyad bazai iya cirota ba, abinda ke kara firgitata is zuciyan Rashida just like yanda tazo jiya ta takali Rashida and she fell for it still haka zata karayi Rashida kuma ba hakuri taje tai wani abu shikenan akamata akai prison with concrete evidence. Yaya zatai protecting Rashida? Kodai su saida gidan su koma kauyensu dudda Kawu ya koreta ada dasuka je? But makarantan Rashida fa, itafa asibiti fa, auren Rashida fa? Riyad fa? Batama Rashida kwadayi tai auren kauye, tanaso diyarta tazama wata babba aduniya, but idan matan nan ta turo maza suka dauke Rashida sukai amfani da itafa suka lalata mata rayuwa tunda dai burinta na police station bai yuwuba, tayaya zata kare yarta? Dudda Rashida akwai karfi akwai zuciya but maza maza ne! Idan akai kidanapping Rashida yanzu yaya zatayi? Tunani daban daban take sai kawai jikinta yasake rikicewa har aka kira asuba yau takasa tashi tana wajen zaune tana kallon yarta,har Rashida ta farka da kanta tabude ido taga Mama murmushi tayi tai mika ta tashi tace “Mama baki tadani ba sabida ba aiki ko” gari yawaye Mama banyi salla ba”.
💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 2️⃣2️⃣
Chapter 38 · 0% Book details