← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 95

Sashe 23

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ahankali Mama ta girgiza mata kai tace “shiiiiii don’t ever blame kanki for ciwo ba cus ba laifinki bane ko daya, stop crying to bagani nan naji sauki ba, gashi nan duk kin bata fuskanki jibi yanda idanuwanki sukai ja sabida kuka bari kiga” Mama sai kawai takama bakin hijabinta takai kan fuskanta tashiga sharemata ta shafa kumatunta tasake murmushi tace “I have the most beautiful yarinya wlh idan tai kuka sainaga idanun nata ma sunfi kyau” dan murmushi kadan tayi wasu hawayen na taruwa, Mama tace “ai kaga abin karki kukan ya isa nace, yanzu dai tafi gida ki shirya kitafi school idan zaki dawo saiki biya wajen gyaran wayanki” baki Rashida tabude zatai magana akai knocking kofar just once kallon kofan sukayi dukansu, Mama tace “jeki bude kofan muga ko likita ne natafi gida” but Dr direct yake bude kofan tai maganan aranta tasa hannu ta goge fuskanta tass sannan tawuce wajen kofan tasa hannu ta bude ido da ido tayi da Riyad dake sanye cikin wata shadda yau sky blue jumper kanshi ba hula tashin Kansa ya kwanta sidik tunda take bata tabajin kamshin turare mai dadin nashi ba, da sauri ta dauke kanta dağa kallonshi Mama hangoshi yasa tace “bismillah bawan Allah” anatse akamilance yashigo har gaban gadon yaje yaduka dasauri Mama tace “tashi tashi haba zauna ga waje” tabashi kujera ijiye ledan dake hannunshi yayına gefen gadon yace “ya karfin jiki Mama ina kwana” murmushi Mama tayi tace “jiki Alhamdulillah naji sauki, nagode da kulawa ka kawoni asibiti banda bakin maka godiya Allah maka Albarka” takalli Rashida dake tsaye wajen kofan tai folding hannu tace “baki iya gaisuwa bane ko akwai abu abakinki ne” dan juyawa tayi da kyar tace “ina kwana” baki Mama tasaki tana kallonta ganin baka yasa da kyar tace “mungode” dasauri Mama takalleshi tace “Ya sunanka ne?” Ahankali yace “Riyad sunana” daidai lokacin akai knocking tareda shigowa dakin wata ce tana sanye da uniform na ma’aikata tace “good morning Ma dazu nazo nakawo muku breakfast naga kuna bacci natafi dashi dan karyayi sanyi yanzu zanje nakawo muku” tawuce tafita daga wajen kofan akunbure Rashida tace “Mama kicemai yasa a sallamemu mutafi asibitin mu” dan juyowa yayi daga inda

Yake yazuba mata ido dauke kai tayi strictly yace “Dr yace 3days Mama zatayi anan and hakan ne zai faru” dasauri Mama tace “Riyad kaga ai dawainiyan zaiyi yawa ta ina zamu sami kudin biyanka? Dan Allah kasa asallamemu naje general dana saba zuwa kaji, Allah yamaka Albarka Allah yakara daukaka” daidai lokacin aka kawo abincin breakfast ne omlete da bread toast sausage tea dakuma bowl na fruits yarinyar ta saukar dama da Mama wajen ijiye abinci kan gado sannan takai dayan abincin kan table sannan takalli Riyad tace “Sir do you need anything”? “No thanks” yafadi atakaice, Mama ta kalli Rashida dake tsaye kikam har lokacin awajen kaman mai gadi tace “zokiyi kari kitafi school don’t even tell me bazaki ba” kaman zatai kuka tace “Mama ni banso naje wazai zauna dake natafi” “I will be here with Mama” dağa Mama har Rashida dukansu kallon Riyad sukayi, hakanan Mama kawai taji tanason natsuwan yaron, abin yana mata ma kaman tasanshi batason tai rubbing in his face hakan yasa tai murmushi tace “to kinji Riyad zai zauna yatayani hira zoki ci abinci kitafi school kinyi katti already banson kina fashi a school kije gida ki shirya kitafi” bataso taje school ba but abinda yafima damunta is wannan mutumin dayakeyi kaman irin ya sansu din nan ko su yan uwa ne saiwani shishigi yaje musu mutumin da shekaran jiya ta sanshi, batason tai gardama sabida Mama batada lafiya hakan yasa ta taho wajen gadon gefen Riyad ta ballama jakan abubuwan dayakawo harara karaf akan idanunshi sannan tadauki jakanta dake wajen ta taso tajuyo hada ido sukayi tadauke kanta tajuya Mama tace “abincin fa” akufule tace “ni bazan ci ba” tawuce wajen wardrobe na dakin taciro kayan jakan an Mama daya kawo ta maidasu ciki kudin taboye karkashin kayan sannan tawuce tai hanyar kofa tace “natafi” tabude kofan tafice ijiyan zuciya Mama tasauke tasa cokali ta a abinci tace “I have a very stubborn yarinya Riyad” dan murmushi kadan Riyad yayi baice komiba, Mama tai shiru kaman mai tunani tace “she’s all abinda na mallaka aduniyan nan” saita dauki fruits takai bakinta tafara taunawa sai kawai tafashe da kuka as if she’s holding on to something ahankali Riyad yace “Mama stop crying she will stop being stubborn soon duk yarinta ne, zata dena nan gaba, stop crying kinji Mama is not good for you zai hanaki warkewa” ijiye spoon din tayi takai bakin hijabinta ta goge fuskanta tace “ciwo na bana warkewa bane, HIV gareni Riyad” tadanyi murmushi tace “I don’t even know why nake fadamaka nasan kariga kasani Rashida tacemin agabanku abokiyar aikinta tace inada shi” tai shiru sai kuma ta zufar da iska dağa bakinta tace “I’ve caused Rashida pain tun tana ciki na, yarinyar nan tayi girma cikin bullying din society yar fasika yar mazinaciya yar me HIV so sometimes I don’t even blame masifa da fadan da stubbornness nata society shaped her to be that way dole tai finding means na yanda zatai surviving.
Chapter 23 · 0% Book details