← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 95

Sashe 7

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Sosai manager ke kallon zanen saikuma ta kalli Rashida tace “anya kene kikai zanen nan kodai satowa kikayi”? Zaro manyan idanunta tayi tace “tunda nake bantaba sata arayuwana ba idan baki yarda ninayi ba bani paper da pen da color namiki exactly irinshi agabanki” murmushi manager tayi takalli abin saikuma tace “zan saya akan 10k each sannan ki dingayi kina kawomin ko guda nawa ne zan saya” bakaramin dadi Rashida tajiba dudda zanen zane ne da har 100k zaa iya saya awani waje but bata damuba 10k is huge 30k ta kirgo tabata sosai Rashida taji dadi bata taba sanin zata iya saida zanenta ba kaman fa wasa taji ana maganan sayan frames tace ta iya manager tace takawo tagani jibi anbata 30k akan guda uku anatse tace “nagode Ma Allah kara arziki” dan tabe baki matan tayi tace “tafi kifara aikin ki” wucewa tayi tafita manager ta kalli frame din tace “zan gayawa Oga 150k each nasaya wayyooo this girl is talented bata sani ba inhar Oga yasosu zance muyi ma all rooms na hotel namu nabama yarinyar tamin I will be fucking billionaire nabata 10k each ni na karbi 150k for each awajen Oga wow look at her work”.

💫 SANYI DA ZAFI 💫
✍🏻M SHAKUR

EPISODE 6️⃣
Wallahi kanshi ma sarawa yafarayi jin maganganun da Mom kemai, first of all duk wani abun na sarautan su bayaso saisama baya iya zama agarin, baison hayaniya baison how they do things cus is always fighting, makirci and politics, and baijin tunda ya girma yatabayin cikakken 2months like good 60days agidan ba bini bini yabar country, lokutan salla ne yasan dole yake dawowa sabida yanda Baba ya maida abin mandatory yanason duka yaranshi to be home sabida hawan salla and other activities na al’adu, shi mutum ne da baisan mulki he prefer business nashi, he derive joy a business, it gives him purpose, for aure kuma dudda yasan culture nasu ne amaka aure abaka mata but shi kwata kawata baitaba sanin Mom zatamai hakaba cus Mom is highly educated and expose, itama bata cika biyema culture ba saisa ma take barinshi to live his dream life, ko kadan bai shirya aure ba cus bayason commitment for now, his plan is nan da 2yrs zaiyi aure yanzu kawai aure baya lissafinsa, dukawa yayi ahankali gaban Mom yadafa kafanta kaman zaiyi kuka yace “Mommmmm” ahankali itama Mom tana kallonshi tace “Riyaddddd! You don’t have to say abinda zaka fadi kasan nasanka sama da kowa aduniya ko?” Gyadamata Kai yayi Mom tace “I know how you despise sarauta, mulki infact bakamasan komi akaiba, I know for auren zakace baka shirya ba bakasan damuwan mace da sauransu” sai kawai takai hannuwanta tai cupping face nashi cikin tattausan lafazi tace “dama akwai abinda zan taba so aduniyan nan dabaza ka iyamin ba Riyad”? Ahankali Mom tace “I thought nine number 1 dinka like you always say”? Dasauri cikin raunin murya Riyad yace “Mom u are my number 1 kema kin sani” kai tsaye Mom tace “inhar nine number one din naka then karka karamin gardama kan maganan nan it’s an order allow me to do everything am I clear?” Yadade yana kallonta yanda take kallonshi babu wasa kan idanunta yasa ya sauke kanshi kasa alamun dai baiso but baice komiba, baya iyama Mahaifiyarshi gardama, cikin fushi Mom tace “kamin shiru? Ban isa dakai bane ko ban isa nace maka haka nakeso kayi kayiba”? Tai maganan tana shaking leg in anger, abu yahadiye awuyanshi har saida taga motsin adam apple nashi asanyaye yace “okay” tsayarda shaking leg din tayi tai murmushi sai kawai ta matso ta mannamai peck agoshi tace “I wish kowacce uwa zata sami d’a mai mata biyayya kaman Riyad dina data zama very very lucky, Allah maka albarka kaji, Haleema is a good girl tana matukar sonka tun tana yar yarinya, she will keep my son happy I’m sure of that, so karka damu, zancen sarauta kuma I will teach you everything and you will do well kaji”? Gyadamata kai yayi zuciyanshi duk ba dadi duka duka kwanan Babanshi nawa da rasuwa but kowa is after kujeranshi, look at matayensu kaman ba mazajensu ne suka rasu ba dukansu kokarin daura yaransu kan Sarautar suke sunma manta da rasuwan shima yanzu yazama sarkin one day haka matarshi zatayi kenan itama yana mutuwa all focus dinta will be yanda danta zai gajeshi bamatada lokacin yimai addu’a tashi kawai yayi yajuya yayi kofa.

Mom tabishi da kallo ranta fess, dolema Riyad dinta yadinga intimidating kowa, yafi duka yaran sarki kyau ga kwarjini ga haiba ga natsuwa, ga jan aji, ga kudi, ga rashin magana, ga rashin shiga mutane, gashi baida kallon mata shi kadai keda qualities na sarki and bazata hutaba saita maidashi sarki wannan alkawari ne!.

Dakinshi yashiga Munir dake danna laptop yabishi da kallo ganin yanda mood dinshi ya chanza tashi daya, Wucewa yayi yafada gado yakife cikinshi tareda lumshe idanu Munir baicemai komiba yacigaba da abinda yakeyi abinshi.

Yana fita Mom ta daga wayanta takira matan Waziri da ake kira da Mariya ringing daya ta daga wayan tace “ranki shi dade Uwardakina, Allah yaja zamaninki Umman Riyad” dan murmushi Mom tayi kafin cikeda isa da jiji dakai tace “dole gobe Haleematu zata koma makaranta ne”? Dasauri Mariya tace “ai Uwardakina ko makarantan kikace karta kara zuwa saita zauna” jinjina kai Mom tayi tace “tom inaga bazata tafi goben ba dan zan turo Riyad yazo ya ganta inaso nahada su aure inyaso bayan yaganta zata iya tafiya” wani ihu Mariya tayi cikin waya saikuma ta zube kaman tana gabanta tace “nagode nagode Uwardakina da wannan karamci naki, kidubi kowa na gidan nan amman kuka zabinma Yarima Riyad Haleematu nagode, namiki alkawari bazaki taba samin matsala damu ba, I will forever be loyal to you, Haleema zata bautamiki Uwardakina, kuma da yardan Allah kujeran sarautan nan ta Yarima Riyad ce ai naji jita jita, da yardan Allah shine magajin sarki” dan murmushi Mom tayi tace “Waziri ya shigo yakirani” tana maganan ta katse waya wani ihu Mariya tayi tamike da gudunta tafice zuwa dakin Haleematu kai tsaye tabude kofan yarinyar na zaune sanye da rigan bacci tana kokarin hada kaya Maman kawai ta dagata tana juyawa tana rawa abinma saiyasa Haleematun dariya tace “Mommy menene kike murna haka”? Cikeda jin dadi tace “yanzun nan Sarauniya Maryama takirani tace tanason hada aurenki da Yarima Riyad gobe ma zata aikoshi gidan nan” wani kalan zaro idanu Haleema tayi she can’t believe abinda taji tun tana yar yarinya takeson Yarima Riyad yahadu ne over wlh, lips nata rawa suka fara farinciki yahanata magana tace “Mommy mekikace? Yarima Riyad mene? Dan Allah maimaita”?Kyalkyacewa da dariya Mama tayi tace “dalla cewa nayi za’a aura miki Riyad zaki zama matan sarki dan ina mai tabbatar miki shi za’a bawa Sarautan” ihuuuu tayi tareda wani kalan tsalle ta rungume Mamanta sai kawai tahau tsalle sosai lekowa dakin Waziri da shigowan shi kenan yayi ganinsu yayi murmushi waya na kunnenshi Mama zatamai magana yadaga hannu yace “inajinki ranki shi dade” wucewa falo yayi yazauna Mama da Haleema suka biyoshi a speaker yasaka wayan dashi da Mom ke magana suna shirya komi kaman ba mutuwa aka musu ba, planning auren da yanda zasu sami kujeran suke hankali kwance.
**
Chapter 7 · 0% Book details