← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

EPISODE 38
Bude kofan dakin da suka sata ciki Ammi tayi tai shiru tana kallon Rashida da sai bayan su Riyad sun fada mata waye ita saita fara ganin yanayinta da mahaifinta Mujitappa dudda bawai tana kama dashine gabaki daya bane dan tana kama da mahaifiyarta but wlh tayo yanayin Mahaifinta sosai, gakuma kama na jini Allahu Akbar! Ammi saita fara tuna sanda mahaifiyarta ke kuka sosai tana cewa bata taba fasikanci arayuwanta ba, duk alokacin cikinsu babu mai iko ko wanda ya isa yaja damai Martaba a fada hakan yasa kowa yayi shiru, ijiyan zuciya Ammi ta dauka ta shiga dakin ahankali ta zauna bakin gadon tana kallon fuskan Rashidan da hawaye ke bin idanunta hannunta Ammi takai ahankali tadaura saman wuyanta wani irin sanyi ni’ima Rashida taji yasauka ajikinta kalan wanda takeji idan Mama ta tabata hakan yasa tabude idanunta ahankali batare data juyoba, ahankali Ammi tace “Rashida” tunda Rashida take arayuwa bata tabajin murya daya mata kusan shige dana Mamanta akunne ba saiyau hakan yasa tajuyo da jajayen idanunta ahankali takalli Ammi kaman yanda Ammi ke kallonta dudda yanda take cikin bakin ciki but saida taga kamannin matan da Riyad hakan yasa tagane mahaifiyar Riyad ce, ahankali Ammi tanuna kanta tace “sunana Ammi, I’m your new Mama take me as one kinji Allah jikan mahaifiyarki” hawaye taga sun taru sosai a idanun Rashida dayasa ahankali Ammi tasa hannunta tadagota takawota jikinta kankameta Rashida tayi kawai saita fashe da kuka sosai, Ammi bata hanata kukaba sai bayanta datake bugawa tace “Rashida bana fata wata rana na mutu yarana su kasamin addu’a sai kuka, burin kowace uwa shine yaranta suyita mata addu’a kidena kuka I know it’s painful but Mama tafi bukatar addu’a awajenki kinji” gyadamata kai Rashida tayi ita kadai tasan metakeji Ammi tace “gashi jikinki zafi tashi muje kiyi wanka I will call Dr tazo tadubaki” dagata tayi zuwa bayin dake dakin tabude ta shigar da ita itama ta shiga hannu tasa abayan zip na riganta taja mata shi kasa tace “bari nakawo miki soap da brush” fita tayi bata jimaba takawo soap brush sannan tafita ta tsaya bakin kofa tace “imaxa ina jiranki” tawuce tabude wardrobe na dakin taciro mata wasu simple black-shirt da skirt har kasa English shima mai slit ta back kafan ta ijiye mata akan gadon sannan takoma jikin bayin tace “imaza gani nan fa” ruwa Ammi taji na zuba hakan yasa ta tsaya almost 5min sannan tadan bude kofan kadan ganinta tayi tsaye gaban shower ruwan na dukanta da rigan da komi da sauri Ammi tashigo tana kashe shower tana kallon yanda take kuka kafin ahankali taja towel saida tafara kara mata sannan taja rigan kasa tadago ta kulla mata towel din ata gefen armpit sannan tadauki karamin towel tasa mata asaman gashinta daya jike sharkan ta kwashe takamota suka fito zaunar da ita tayi abakin gado takai hannunta tana share mata fuska tace “ya isa” tadauki rigan tasamata takai saida tagama samata sannan tasauke towel din zuwa waist nata skirt din shima takama kafanta tasa aciki tadagata taja skirt din har waist nata kafin taja towel din na saman kanta ma ta tsani kan kafin taja towel din tawuce takai bayi tadaga riganta dake bayin tasa a washing machine sannan tafito sauka tayi tana kiran Dr nata tashiga kitchen Ammi nada son girke girke da kanta dudda tanada masu aiki lafiyayyen tuwo ta debo mata da miyan kuka da man shanu tahayo sama inda ta barta anan tasameta Ammi tace “you will have to eat koba yawa okay” hannunta tasa ta gutsuro tuwon takai bakinta ahankali Rashida ta kalli hannun Ammi dake miko tuwon bakinta kawai saita fashe da kuka tana bude bakinta emotionally Ammi tai murmushi kadan tasamata sabida tagane Mamanta ta tuna mata sosai taci tuwon tana kallon fuskan Ammi, Ammi tabata ruwa tasha sannan takaita bayi tayo alwala ta daurata kan dadduma tace “yi salla bari nashigo da Dr” fita tayi daga dakin bata wani jimaba ta shigo tareda wata Dr zama sukayi saida Rashida ta idar Dr tace “sannu” dan dudduba Rashida tayi tace “bari namata allura da magani” allura tafara mata sannan aka bata maganin tasha zama kusada ita Ammi tayi takama kanta tasa ajikinta wannan dumin uwa dataji daga jikin Ammi
Chapter 52 · 0% Book details