← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 95

Sashe 20

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

EPISODE 1️⃣3️⃣ Gida tashiga around magrib agurguje tai alwala tashigo ciki Mama nakan dadduma hakan yasa ta tsaya kusada ita ta kabbatar sallan. Tana idarwa cikeda damuwa tace “Mama ruwa yashiga wayana taki aiki wlh” tai maganan tana jawo jakanta taciro wayan cikeda damuwa itama Mama tace “garin yaya meya sameta?” Cikin damuwa tana kara huhhure wayan tace “faduwa nayi ruwa ya kwaromin shine ruwan yataba har wayan” dasauri Mama tasa hannu ta karbi wayan itama tana huhhura duk wani huji na wayan ta maida battery din kozata kunnu amman bata kunnu ba hakan yasa ta tashi tawuce chan wajen yan kayan abincinsu tabude ledan shinkafa tasa wayan ta zuba shinkafa akai tace “bari mugani kozata kunnu idan bata kunnu ba saina tattara kudin dake wajena kije ki sayo wata wayan dashi, kina bukatan waya kodan school, Allah kiyaye bakiji ciwo bako”? Gyadama Mama kai tayi tace “banji ciwo ba” Mama tace “to ai mun gode Allah tashi kiyo wanka kici abinci” dasauri tace “Mama girki kikayi”? Gyadamata kai tayi tace “eh nayi shinkafa da wake da mai sa yaji” murmushi tayi tace “Mama banace ki dena girki ba” ture mata hanci Mama tayi tace “to banji maganan ki ba Anty Rashida” kwashewa da dariya tayi hakan bakaramin dadi yama Mama ba ganinta duk cikin damuwa sabida wayan tasan lissafi take ta yanda zata taba kudin saving dinsu tasai waya dashi kafin takara samin wani kudin fa, rashin lafiyan Mama fa, abinci fa, kudin wuta fa, tasan duk abinda take tunani kenan ganin tayi dariya yasa hankali ta ya kwanta, cikin shagwaba tace “kai Mama nine Anty Rashida” Mama ta kama haba tace “yooo ai hakane, Mama karki kaza, karki kaza, kullum command kike bani yarnan kinga ai kinzama Anty Rashidan” sake bushewa da dariya tayi kawai saita kwanto jikin Mama tace “Mama stoppp wlh ni ba Anty Rashida bane, Mama ina hanaki ne fa sabida karki fadi, kinga kinada yawan ganin jiri, kınada migraine kuma, Mama I have to take care of you gwara namiki komi ko ruwan dazakisha na ijiye kusa dake sabida karki wahala wajen daukowa” tabe baki Mama tayi tadagata daga jikinta tace “jeki wanka kizo kici abinci” tashi tayi ba musu ta rage kayan jikinta tadaura zani ta kwashe kayan da lab coat da kayan Mama data cire yau dasafe tafito saida ta fara wankesu tsaf ta shanya sannan tawuce bayi tai wanka tadawo Mama tabata abincin ci tayi bawani sosai ba batawani cin abinci abin yabi jikinta sannan takai kwanon waje ta kuskure baki ta dawo tahau salla kusa da Mama tana idarwa ta kwanta awajen ko 2min ba’ayiba tafara minshari Mama tai shiru tana kallonta sai kawai tasa hannu tadauki feet dinta ta daura kan cinyanta dudda uban tafiya akasa datakeyi bata da kaushi kafanta still looks very fine ga nails dinta farare kal masu kyau, ahankali take massaging kafafun ayanda ta gyara kwanciya kasan tanajin dadin tausan Mama is just looking at her babu salloli biyar dazatayi arana da zatakai goshinta kasa dabazatama Rashida addu’a ba, banda kiyamun Layli datakeyi kullum, kullum addu’an ta shine Allah yakawo ma diyarta karshen wahalan nan Rashida ita ke ciyar da ita, itace cinta shanta suturanta magungunanta da komi na rayuwan su Rashida ke nema, babu yanda zatayi ne dan batama da karfin aikin ne da itace zata fita ta nemawa diyarta abinci da komi ba diyarta tayi ba, kullum addu’an ta is Allah ya tsare yarinyar ya tsare imaninta kar wata rana tagaji da aikin wahalan nan tace zata shiga duniya tabi maza dan shine hanya mafi sauki da akebi asami kudi, addu’anta koda yaushe shine Allah yabata ikon kammala wannan karatun likitan, kowani shekara da hayya hayya take tara kudin school fees nata na last year bai musu wani wahala ba sabida tasami aikin hotel din nan ana biyan ta dubu 50k duk wata a nan ta tattara tabiya, fatanta shine Allah sa wannan shekaran na biyar kar kudin makarantan yayi yawa dubada yanda aka kakkara kudin makarantu, hawaye ta share ahankali daya zubo mata bata taba sanin dan Uwanta na jini zai iya juya mata bayaba sabida wannan cutan dudda da ranshi da lafiyanshi, bata da kowa sai Rashida, yau shekaru ashirin da uku kenan tana wannan wahalan tun Rashida na cikinta, ta haifo yarinya cikin wahala ta tashi cikin wahala sannan itama tana rayuwan wahala, batabama yarta komiba sai wahala, babu wanda ya yarda ya auri Rashida, ga yanda yar karaman yarinya ke aiki kaman namiji wata kalan uwace ita, hawaye ne suka kara zubo mata sai kawai ta jinginar da kanyon a bango takalli sama murya chan kasa that is very weak tace “Ya Allah idan mutuwata shine mafi alkhairi agareni dakuma y’ata, idan mutuwata zai cireta daga cikin wahalan nan datake ciki Allah ka kasheni, ka aurar da Rashida gidan dazata huta, karufama Rashida asiri, ka lullubeta cikin nimarka Ya Allah. Tadade ahaka yawanci tana boyema Rashida damuwanta da dama sabida kar yarinyar takasa karatu idan kanaso kaga Rashida ta birkice tarasa sukuni to Mama tace kaza namata ciwo tuni yarinyar zata rude, damuwa, tunani ga constant ciwon kai koda yaushe shiyafi damunta, saisa kullum tane asibiti BP ta is high, magungunan BP nema ke cinye musu kudi cus maganin HIV free ake bata a clinic dinsu. Ganin yanda bacci ya shigeta yasa bata tadataba tabarta tai baccin anan kan dadduma. Wuraren 5 Mama ta tadata da kyar ta tashi wanda hakan daman is daily battle nasu, gyaran gidan tayı tasa takai Mama tai wanka tai salla tazo ta dumama shinkafa da waken sannan tama Mama tuwo sunada miya daman kafin ta shirya cikin bakin abaya da stones nashi yagama fita tass but dudda haka ya mugun mata kyau abunka da fara tazo taje wajen wayanta taciro daga shinkafan tasa battery ta kunna amman still yaki kawowa Mama tace “bai kawo ba?” Gyadama Mama Kai tayi ahankali, dasauri Mama tazo karban wayan tayi tace “kodai ba chaji ne” tawuce wajen chazanta dake bango ta makala kusan 3min bai dauka ba, ahankali Mama ta tashi tace “bari nabaki dubu talatin din nan saiki sayo wata wayan kawai” dasauri tace “a’a Mama ki adana talatin din nan, bari zan kaita wajen yan waya a gyaramin zasu iya gyaramin” badan Mama taso ba dan wayan tariga tagama tsufa dukta farfashe tace “to shikenan bari na baki kudin gyaran” sip tabude taciro wani leda ta kirgo 5k tabata karba tayi sannan tayafa gyalenta tace “bye Mama” har zaure Mama tarakota tace “adawo lpy” dayake 9 ake fara clinic dinsu hakan yasa taje shagon Maman kuwa tayi aiki ta karbi 2k dinta sannan tawuce shan wajen gyara takai wayan ganin zai dauki lokaci tace “zata dawo da yamma” tashiga keke sai hospital nasu. she’s not really doing much a consulting room take zama attached to consultant din da aka assigning nata to him yana duba yara marasa lafiya yana tambayanta me aganinta take tunanin is diagnosis din tafadi, kokuma yace wani investigation yakamata ayima yaron tafado sunayen series of test da za’ayi ganin how brilliant d girl is tsohon likitan yace “i will comfortably leave the office for you tommorow” gyadamai kai tayi dan she hardly smile outside, haka dai tagama by 1 tawuce mosque tai salla ta linke labcoat tasa a bag sannan tafito tashiga keke sai hotel. Yau tadanyi latti sabida traffic sai around 2:30 tashigo hotel din ko kallon mutanen dake reception da lobby gabaki daya batayi ba da sauri sauri tawuce changing room nasu kofa tabude ahankali, ma’aikatan su tagani gudu uku a lobby suna chanza kaya da kallo suka bita batace musu kala ba tawuce locker dinta tasa password dinta tabude, daya daga cikinsu ne taja tsaki tace “mutum sai fadin dai, nagadai da mutum dan wani ne dabaizo hotel neman aikin shara da wanke bayi ba, tundadai duk ansan juna menene na jijji dakai kaman diyar wasu” ? Sauran biyun ne suka kwashe da dariya daya tace “dadine dake Hussy baki hadiye abu aciki” parking gashinta tashiga yi da ribbon tace “eh mana kullum fuskan mutum amurtuke ana fadin rai ana daga shoulder kaman yar shugaban kasa amman shine akazo aikin wanke bayi a hotel” wani irin buga marfin locker Rashida tayi saida yayi kara pammm!Tajuyo tai facing Hussy direct cikin zafin rai tace “dani kike maganganun nan?” Wani banzan shakiyin kallo Hussy tamata dan tadade tanajin haushin Rashida wai ace ma’aikata nawa a hotel din nan yarinya bata kula kowa, kuma kai kasauke kanka ka kulata taki kulaka back, bama wannan yafi bata mata rai ba yanda take nuna bamatasan anyi hallita irinsu a wajen ba ko ka kulata ita bazata kulakaba sai bakin taurin kai, jibidai yanzu datazo tasamesu ko Hi bazata iya gayamusu ba? Amman basu isheta kallo ba, cikeda tsana tace “naga dai ban kira suna ba, amman duk wanda ya tsargu dashi nake” wani irin kallo Rashida tamata kaman taci ubanta saikuma ta tuna nan wajen aikin tane, da kudin aikin wajen nan zata biya school fees and other things bari kawai ta barta today is her lucky day, sai kawai tajuya tasa hannu zata dauki uniform nata batare data kara magana ba, cikeda neman fada Hussy tai wani shewa tace “jakan ta tsorata” juyowa Rashida tayi da mugun zafin rai batai wata wata ba ta fizgo gaban rigan Hussy ta kifa mata mari a fuska ihu jikake tasss! Hussy tayi ihu ta chakume gaban rigan Rashida tace ni kika mara”? Sai dambe, dukanta Rashida take bana wasaba har gyalenta na fadi kasa bakin gashinta datai parking donut mai bala’in kyau ya bayyana, sauran yammatan biyu na kallo sunajin dadi ganin suna dakan juna dudda Rashida nacin uban Hussy amman kallon fada da dadi yake sukaki rabasu, ganin jini Rashida tafasa bakin Hussy yasa daya cikinsu ta tsorata tace “baruwana kar ayi kisan kai agabana” dasauri tabude kofa tafita da gudu dayan ma tabiyota hango Madam sukayi a lobby tana magana da receptionist kafin sukai wajen ma sukai ihu. “Madam ana fada” daidai lokacin Munir da Riyad na shigowa yana shaye da brown jumper yasa brown shade a idanunshi na CK dayamai kyau sosai, arude dayan tace “Ma come oo harda blood everywhere!” ganin Riyad yasa Madam tace “Sir welcome wai ana fada I
Chapter 20 · 0% Book details