← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 95

Sashe 26

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda yaje office nashi yayi shiru bakin dasukayi ma yawanci Munir ke kulasu, agogon hannunshi kiran Rolex ya kalla 5 tayi na yamma kaman an tsikaresh ya mike duk kallonshi sukayi “excuse me” yafadi tareda wucewa wajen kofa yafice Munir yabishi da kallo kafin yacigaba da abinda yake samin kanshi yayida shiga elevator ya sauka kasa, he doesn’t even know why he’s doing this but samun kanshi yayi da zuwa hanyar changing room din ganin kofan wangale abude yasa yadan leka ciki babu kowa wajen fuzar da iska yayi yajuyo yafito daidai Madam zata shigo hanyar chak ta tsaya ganinshi surprisingly tace “Yallabai wani abu kake bukata”? Kaman bazaiyi magana ba saikuma yace “where is she”? Kallon hanyan Madam tayi tace “wa she? Oh mahaukaciyan nan”? Dan lumshe idanu kadan yayi hakanan yaji kalman azuciyanshi yadai daure bai nuna wani abuba ya kalleta, dasauri tace “ta tatare kayanta ta kwashe komi na locker ta tatafi tabar aikin da kanta kafin mu mata official kora” yanda taga yahade fuska yasa dasauri tace “sorr….” Ahankali yace “sack the other gurl Hus….” Cikeda Mamaki Madam tace “Hussyn Yallabai”? Babu wasa akan fuskarshi yace “I don’t want her working for my company, just compensate for the injury, give the other gurl a call tadawo aiki” yana maganan yawuce baki Madam yakasa kulluwa tana kallonshi, yarinyar data barar da ita yake cewa akirata back, wacce aka jibga yayi sacking, dan ijiyan zuciya tasauke aranta tace “his company his rule!” Tawuce ta tafi office nata. Wucewa kawai yayi yabar wajen yafito, security daya budema wani guest kofa dazai shigo ne ya hango yallabai hakan yasa yashigo ciki da gudu daidai zai shiga elevator yace “Yallabai barka da hutawa dama wata mata ke nemanka awaje” wani kallo Riyad yamai irin wata wa? Shi kuwa? Dasauri security yace “tace wai itace Maman yarinyar da aka kora tazo tabada hakuri tana waje, she’s Rashida’s Mom Sir” hakanan Riyad kawai yaji gabanshi yafadi but yadaure yace “why is she sitting outside?” Dan sauke kanshi kasa Security yayi yace “uhmm Yallabai cewa akayi cutan kanj……” fuuu Riyad yawuce zuwa entrance door din kafinma abudemai kofan dayake glass door ne yana iya hangota yanda tazauna kan kujera tayi tagumi tana kallon waje daya cikeda tsananin damuwa and kana kallon matan kasan she’s really sick she looks so skinny and pale jiyayi zuciyanshi yamai ba dadi sosai yanda security sukai trashing nata awaje haka, dasauri yafice bayan an budemai kofan yayi wajenta direct yana zuwa kawai saiya duka cus bemasan mezaiyi ba, she’s the mother of the girl that save his life kome yayi bai biyataba, cikeda girmamawa yace “Mama” firgigit Mama tadawo daga dogon tunani datake tajuyo ta kalleshi, dasauri tace “Naam Bawan Allah kaina mai wajen nan nazo nabada hak…..” kafin takarasa maganan dasauri yace “Mama” hakanan Mama taji yanda yakirata yataba zuciyanta, yanda yakira sunnan just touched so many things a zuciyanta kawai sai hawaye, life and sickness nata have made her so emotional, muryanta na rawa tace “dan Allah dan Allah kuya kuri nasan Rashida da zafin zuciya ga fada ga taurin kai, kome akace tama yarnyar nan nasan tayi dan Allah kuyakuri kurufamin asiri kada ku koreta daga aikin nan dan Allah ku taimakeni” tai maganan tana jan kujeran baya zata duka dasauri Riyad yakama knees nata ahankali yace “Mama dan Allah karki rokeni, ban koreta ba zata iya cigaba da zuwa aiki” da sauri Mama ta kalli fuskanshi tace “da gaske?” Gyadamata kai yayi yace “eh” ijiyan zuciya Mama ta sauke tace “to inane gidansu yarinyar naje na bada hakuri” ahankali yana sakin knees nata yace “basai kin bada ba lafiyanta kalau Mama, is just normal misunderstanding da kananun maganan yara yajawo fadan kada ki damu kinji” gyadamai kai tayi tace “Allah maka albarka” murmushi yamata kadan baice komiba, Mama tace “bari natafi gida to Alhamdulillah nagode nagode nagode kaji” daga yanda take maganan kasan hankalinta ya kwanta gyadamata kai yayi, Mama tace “to sai an jima” “saida safe Mama” yafadi ahankali, Mama ta wuce cike da farin ciki tafara tafiya kadan kadan sabida yanda kanta ke sarawa, tayi tafiya daya biyu uku ana hudu kawai ta yanke jiki tafadi, Riyad na tsaye yanama security magana sukaji karan fadin abu juyowa sukayi ganin Mama yasa dawani irin gudu Riyad yayi wajenta suma security din haka dago kanta yayi yana tapping hannunta yana kiranta. “Mama Mama Mama” amman shiru dasauri yace “help me” daukanta sukayi yabude bayan motanshi yasata yakoma yashiga gaba yatada motar sai wani babban private hospital dayake zuwa anytime yake Kano yana zuwa aka karbi Mama sai emergency yawuce office na Dr dinshi ya shiga Dr ya sallami patient dayake tareda shi yace “Ranka shi dade mai Martaba” dan yatsine fuska yayi yace “don’t call me that I have a patient tana Emergency I want you to be on her case fast” tashi Dr yayi suka fito tare ya shiga emergency din, shi ya tsaya agaban wajen yarasa yanda zaiyi sai kuma yakoma office na Dr ya zauna, yana nan zaune yana jiranshi har aka kira magrib saiya tashi yafito yawuce mosque yana gani Munir na kiranshi yaki dauka salla yayi yafito yawuce ciki yakoma office na Dr yazauna sai gashi Dr yashigo dasauri Riyad yatashi yace “how is she ta farfado?” Gyadamai kai Dr yayi yace “da kyar muka samu ta farfado amman tana bacci” saikuma ya zauna ya kalli Riyad yace “kasan wacce ka kawo? Who is she to you?” Batare daya amsashi ba yace “does that matter? Meke damunta? How can I help?” Gyara zama Dr yayi yace “she’s HIV patient!” Yayi maganan yana kallon fuskan Riyad dayaga bai chanza ba saima yace “me da me take bukata yanzu”? Ahankali Dr yace “is like she’s on medication so bahsine abinda ke damunta ba bashine kuma dalilin yankewan jikinta tafadi ba, abinda yafi komi damunta is BP, BP ta yayi raising sama sosai I don’t think zan sallameta yau ko gobe ko jibi ma sef, sai ya sauko sannan zan sallameta, just get wanda zai zauna da ita and then drugs” yashiga rubuce rubuce duk Riyad na kallonshi saida yagama komi sannan yanunamai takardan, tashi Riyad yayi yazaro wallet dinshi ya ijiye akan table din cikeda izza yace “take any amount kake bukata for drugs, bills, pin is 6648” yana maganan yawuce yafita akasaitance yasauka kasa dakin dayaga an shiga da ita yawuce shiga yayi ahankali ya tsaya bakin gadon an cire hijabinta daga ita sai riga da zani da hulan dake kanta an samata drip, shiru yayi yana kallonta sannan yajuya yafice daga dakin yawuce yaje motanshi yashiga yadau wayanshi yana shirin kiran Munir wayanshi yashiga ringing Munir dinne yana dagawa kafin yayi magana yace “Munir open file na employees dina a desktop get info na Rashida I need address nata ASAP” kafin yayi magana ya katse wayan yayi shiru chan saiga Munir din yakira yace “suna Ranji, wajen tudun Murtala” baimasan inane wajen ba but haka ya katse wayan ya kunna google map yashiga driving…. Tunda tai magrib ta zauna tai shiru tana mamakin ina mama taje harta dau hijabi kota bita hotel dinne ko wani case dinne akeyi achan but karta kara bata ran Mama taje wajen hakan yasa ta daure ta hakura, kuma zai iya yuwa tadawo takai karanta wajen Baba liman ne dantana haka wani zubin hakan yasa ta zauna adaki zugum kaman wata marainiya idan aka kira isha’i bata dawo ba zatasa Hijabi taje ta nemeta…. Shigowa layin yayi ga majalissar maza gaban shaguna ana zance rage wutan motan yayi karya haskosu yana karasowa yakashe motan kawai ya bude ya sauko yazo wajen yamika musu hannu yace “Assalamu Alaykum” atare duk suka amsashi suna karban hannunshi ganin arniyan motan dayake ja, yace “dan Allah tambaya nake” dasauri sukace “Allah sa mun sani” anatse yace “gidansu Rashida nake nema” tsit wajen sukayi kaman ba su ba saikuma daya daga cikin samarin yatashi yace “bismillah yallabai zomu kebe mana” binshi Riyad yayi sujkaje wajen mota kaman mutumin arziki yace “nasan ba laifinka bane Rashida kam nada kyau Masha Allah yarinya kaman Balarabiya amma dai kyan dan maciji ne, yanda muke gayamaka dinnan haka muke gayama duk wani saurayi dazaice zaizo nemanta hakkinmu ne na yan unguwa, hakkin makotaka tunda su basu fadin gaskiya” tunda yafara magana Riyad yaji ranshi na baci amman ya daure dan he wants the address, mutumin yace “kagadai uwar yarinyar nan fasika ce garin kwashe kasheta ta kwaso kanjamau Rashidan ma muna kyautata zato tanada shi tun acikinta tasam….” “Zaka fadamin adreshin ko bazaka fadi ba”? Riyad tafadi sounding bitter and angry baki mutumin yabude zaiyi magana Adamu mai chemist da tun zuwan Riyad ya hangoshi daga chemist yace “kaje chan kasan layi zakaga gida mai jan kofa nan ne gidansu Rashida” kallonshi Riyad yayi yace “thank you” yawuce yakoma mota yatada mota yabar wajen, gaban gida mai red door yayi parking ya sauka ya tsaya gaban kofan yakai hannu yayi knocking, Rashida na zaune kan dadduma taji ana knocking hakan yasa ta tashi dasauri batare data cire pink hijab dinta ba tafito silipas ta zura gabanta sai faduwa yake ta taho zaure tana mamaki Mama ta kulle kofan ne dazu dan idan aka rufe yana shiga jam, ganin kofan abude ga wani arnen black car parked agaban gidansu wani mutumi a tsaye yajuyama kofan baya so bata ganin fuskanshi yasa ta fito kai tsaye cikin muryanta mai bala’in dadi tace tace “kaine kai knocking wa kake nema?” Har cikin zuciyanshi yaji sanyin muryanta hakanan, cikeda wani irin kwarjini yajuyo yana zuba hannun cikin aljihun rigan dake jikinshi, hada ido sukayi ta kalleshi ido cikin ido dan akwai wuta a kofar gidansu mamaki da tunani yacika kanta, ba mutumin nan bane mai hotel dinda take aiki ba? Ko idanunta gizo yake mata? How is he agidan su? Ganin ya tsaya yana kallonta bayako kyafta ido yasa tadan dauke kai tattare bakin hijabinta tashigayi tana tabawa saikuma takai hijabin bakinta, saichan tacire, saikuma chan ciki ciki kaman an sata dole ahankali tace “ina yini” he’s looking at her mostly sabida baisan mezai fada mata ba, chan yace “Mama wants to see you” hakanan gabanta yayi bala’in fadi dasauri ta kalleshi baki tabude zatai magana saita kasa
Chapter 26 · 0% Book details