← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 95

Sashe 59

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

EPISODE 50
” Takasa karasa maganan sabida kukan daya ciyota tace “that woman………” tanuna Jummai tace “she keep tormenting us tana zuwa gidanmu tana azabtar da Mamana itace da reason yan layinmu akasan Mama nada HIV kowa was stigmatizing ni d Mamana” duk yanda Rashida taso karta fashe da kuka takasa saida ta fashe da kukan tana pointing Jummai dake fiki fiki da ido tana addu’a inama wani abu yasa Muji ya sume karyaji abin da Rashida ke fadi tace “Mama was fine but wannan wicked matan tazo gidan mu ana gobe salla ta dagamana hankali tasa police suka kamani the fear, da shock da Mama ta shiga was the cause of her death, and you dare tell me na rayu dakai Riyad? Riyad do you know what a harsh life is? Do you know wat rayuwa da tabo da sheri da kazafi is? Do you know wat rayuwa is da cutan da bakasan yanda kasameshi ba and you have no way to prove innocence naka? Riyad do you know wat stigmatization is? Riyad kasan menene kunci bakin ciki damuwa da azaba? Riyad kasan zafin ciwo? Riyad kasan azaban da Mamana ta shiga da zata rasu tana ihu cikina jini na fita daga hanci da bakinta? All this abubuwan sabida gidan ku!” Tasake fashewa da kuka da kyar tace “wlh, wallahi! I know Mamana idan da tasan Kai dan gidan nan ne bazata taba baka aurena ba! Wallahi no condition zai taba barin Mama tabarni na auri Dan gidan nan cus gidan nan shine gidan dayama Mamana tabo dahar takoma ga Allah bai gogu ba, Riyad ko kaine last man aduniya i will never ever marry you! I hate you Riyad! Na tsaneka, I hate your family! I hate this house! I hate everything about you people, bazan taba hada jini da ku ba!”.
Babu wanda yakai Maman Kabeer enjoying this drama, ganin yanda Riyad ke kallonta ma speechless yasa tai ihu tace “kabani hanya nabar gidan nan!” Da kakkausan murya Riyad yace “you are not going anywhere” tashi Gwaggo tayi ahankali tazo kusada Riyad tana kallon Rashidan da tun dazu data kalleta taga jikanta, takalli Rashida taga Muji, daman kafin ta mutu zataga jinin Muji! Allahu Akbar! Baki tabude zatai magana saikuma ta kasa hannunta tadaga dake rawa sosai hawaye na saukowa daga kan idanunta zatakai hannun kan fuskan Rashida dasauri Rashida takoma baya tamata wani kallon uku saura kwata dayasa Riyad yakama hannun Gwaggo ahankali hakan yasa Gwaggo tafashe da kuka sosai tana wani irin kallon Riyad tana kallon fuskan Rashida data hade rai tajuyar da fuskanta ma dan bata kaunar kallon any of them, tace “jikana ne wannan? Riyad dama zan taba ganin jinin Mujitappa na? Riya…..” tari Gwaggo tafara dayasa kowa yataso Riyad ya zaunar da ita yana riketa, da sauri Ammi takoma Kitchen dan dauko ruwa ganin haka yasa Rashida tayi kofa da sauri tabude daidai Riyad na dago kanshi yace “Sarkin Gida kutareta” ahankali Muji ya karbi Gwaggo yakalli Riyad cikin soft voice yace “follow her” tashi yayi dasauri ya wuce waje inda Rashida ke rigima da fadawa dasauka zagayeta in circle batare dasun riketa ba tana nunasu da hannu tana ihu. “Kutashi daga gabana, kubarni natafi gidan nan, ihuuu ana kidnapping dina agidan nan, wallahi ko zaku kasheni bazan zauna agidan nan ba, bazan zauna ba” jama’a Rashida tashiga tarawa bayi da ma’aikatan gidan sai shigowa flat din suke, yana zuwa wajen fadawa suka budamai circle din yashiga ciki yana azuciye kawai yasa hannu yakama hannunta dasauri tajuyo tashiga kokawa dashi tana kokarin fizge hannunta tana bori tace “kasake ni let go off my hand, wlh bazan zauna agidan ku ba, I hate this house, I will never ever live here kun kashemin Mamana, stop touching me, I hate all of you” ganin yanda takemai tirjiya tagama ficewa hayyacinta yasa yadauketa chak azuciye fadawa suka warware rigunan su suna kare Sarkinsu suna binsu abaya,Riyad yayi gaba har zuwa flat dinshi yawuce wajen motanshi yabude ciki yasata tataso kaman zakanya yarufe da sauri yayi locking motan yakoma gaba yashiga yatada motan yaja motar yabar gidan. Gudu kawai Riyad yake zubawa akan titi yana kallon yanda Rashida ke kuka abayan mota, yarinyar is deeply hurt, duk yanda mutum zai gwada maka yanda abu ke damunsa idanba kaikeda rayuwan mutumin ba bazaka taba gane meyakeji ba. Sunyi tafiya mai nisa kafin su shiga GRA gaban wani mahaukacin gida fari yayi horn wani security ne yabude kofa ya leko ganin motar yasa yakoma ciki da gudu bude gate akayi Riyad ya shiga cikin gidan wow gidan ya mugun hadu sabon gidane daya gina to his taste wanda duk randa yayi aure zaisa matarsa ciki before zamanshi Sarki yabata komi.
EPISODE 51
Wasu manyan security ne guda biyu sukazo wajen motan da gudunsu dan gaidashi jin ihu yasa duk suka kalli motan daidai Riyad na bude kofa yafito yace “you can go” sannan yabude bayan motan yakalli Rashida dake kuka sosai ba takalmi ba dan kwali harda majina ahancinta tanamai wani irin kallon tsana tace “Wlh I will report you for kidnapping me cus ni ba yarinya bace that you can force me to stay with you, I know my right, I’m not your prisoner banayin auren,! Bazan aureka ba! Bazan zauna da family dasuka kashemin Mama ba, wlh ban yafe muku gabaki dayan ku, Riyad na rantse da Allah I hate you I can’t even stand looking at you” wlh kanshi har wani irin sarawa yake sabida ciwon kan fitinan Rashida, kaman kanshi zai rabe yakeji, ahankali yana kallonta yace “let’s go inside, na chanza miki gida tunda bakison chan” ihu tayi tace “not just gida kaima gabaki dayanka banson ganinka, I said i hate you Riyad bakaji bane? Let me go kasakeni! Ka sakeni! I don’t want you dole ne” hannunshi yamiko mata yace “let’s go inside” kabar da hannunshi tayi harsaida hannun yadaki kofan mota yasake kallonta, ganin bazata taba fitowa daga motan inba ta karfi ba yasa yashigo ya dauke ta by fire by force yafito yawuce cikin gidan da ita, woww falon kaman ba a Nigeria ba sama yayi da ita, yabude wani mad hadadden room yasauketa ciki ta zabura ta tashi tace “wlh bazan zauna agidanka ba” cikeda lallashi Riyad yace “Rashida please listen to me, dan girman Allah, I know you’re hurt! But dan Allah please listen to me” hannu tasa ta tureshi da duka karfinta ganin yana tahowa gab da ita, yayi baya cus da duka energy ta ta tureshi tace “don’t you dare come close to me, na tsaneka Riyad, na tsaneku duka” sarawan da kanshi yafarayi baisan sanda yadafa bangoba jin kaman jiri na neman kwasheshi, hakan yasa yajuya drawer dake gefe yabude yaciro bundle na key yayi kofa yabude, ganin tabiyoshi yasa ya kulle kofan yasa key yanaji tana ihu tana bugawa yawuce yasauka kasa ya dafe kanshi yazauna a last staircase yana dauke ijiyan zuciya kanshi kaman zai fadi kasa.
Chapter 59 · 0% Book details