← Book details Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 95

Sashe 85

Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

EPISODE 74
Cikin hausansa da bata fita sosai yace "¡iee to!
Kanta ya bugu sosai, ta zubar da jini sosai dudda ina bata ruwan ganye dake kara jinin amman dudda haka bai ishetaba jinin sosai batada karfi zatana dinga yawan sumewa, buguwan da akama kanta yasa ta mance komi amman bazata dauki lokaci ne zata warke, komi zai dawo mata, ruwan data shiga ciki yasa sanyi ya taba abin cikinta amman tagama magungunan danake bata za'a dace, shima kan za'a dace da izinin Allah" kowa shiru yayi suna kallonta barin Riyad daya tsareta da idanu yana kallon yanda tadauki naman takai bakinta ta tsotsa tafito dashi kuma ta ijiye sai chan tasa hannu ta dauki wara tana kallo sai ta ijiye saita dangwalo nono takai bakinta tana tsotsan yatsanta, ahankali Riyad yafara tafiya kowa binshi yake da kallo har zuwa inda take gently ya tsugunna gaban tabarman yana wani irin kallonta, wasa take da abinci but jin mutum agabanta da kamshin turare mai dadi daya daki hancinta yasa tafara kallon tundaga kafanshi yana sanye da bakin crocs da dark brown yadi mai bala'in kyau sannan tadago kanta ta kalleshi hada ido sukayi ta tsareshi da idanu kaman yanda ya tsareta shima da idanu, wani irin lankwasa kai tayi tana kallon fuskanshi kaman taga abinda bata taba ganiba tanabin tundaga idanunshi har zuwa dogon hancinshi da kallo down to his lips, wani irin kyau yamata wanda ya banbanta da sauran mutanen yan garin har kayan jikinshi ma, saikuma tadauki kwaryan naman dasauri tasa hannu taciro nama daya ta mikamai, kallon naman yayi sai kawai hawaye ya cika idanunshi, ahankali yasa hannu ya amsa murmushi tamai daya bayyana duka hakoranta jin sahun tafiya yasa dasauri tajuyo takalli sauran mutanen dasuka taho, Muji ta hango yana kallonta shima rikeda soda a hannunshi na Gwaggo dawani irin sauri tashiga kokarin tashi tasa hannunta duka biyun tana kama kanta alamun yana mata zafi tana yatsine fuska dasauri Riyad yatashi wucewa tayi dasauri tana tafiya ahankali kowa na kallonta har gaban Muji hannunta tasa da sauri ta karbi soda a hannunshi tashiga kokarin budewa takasa saikuma tasake kallonshi tabashi, karba yayi ahankali muryanshi har rawa yake yace "nabude miki? Okay zan bude miki" dasauri yabude mata karba tayi takafa abakinta tass ta shanye tana lashe baki tasake saka empty bottle din abaki tana girgijewa saikuma ta kalli Muji dayakai bayan hannu yana goge idanunshi ahankali tace "bani" da sauri takai hannunta takama nashi tana budewa tana neman drink din ashagwabe tace "banimmili" wih duk yanda Muji yaso yadaure saiya kasa yafashe da kuka, he can't believe for the first time yau yanajin dumin hannun yarsa da tun tana ciki ya kada uwarta, ganin yana kuka yasa ta tsaya tai shiru tana kallonshi saikuma tafashe da kuka takai nata hannun tana gogemai hawayenshi Buba yataba bayanshi alamun yayi shiru, daurewa yayi yadena yace "nadena kuka to kinason soda?" Yanuna goran hannunta gyadamai kai tayi da sauri tana dakatar da kukan yace "to mukaje mota zan baki" ahankali tace "mota"? Gyadamata kai yayi yace "eh mota" juyawa tayi tana fadin mota mota mota mota mota tawuce wajen tabarman taxauna ahankali, tana kallon Riyad data sakemai murmushi tace "mota, mota, mota, mota" saikumai tamai murmushi again, kafin tazo dasauri takama hannunshi tarike tana kallon agogon dake writs dinshi saikuma takalli fuskanshi tace "mota?" Hannunshi Riyad yakai ahankali for the first time yadaura akan fuskanta dasauri takalleshi ta tsare idanunshi da kallo dataga suna tara hawaye, tace "sunana mota".
EPISODE 91
Buba ne ya iya katse shiru da akayi ana kallonsu yace "yamma na gabatowa, Mun gode da taimakon dakuka mana, baxamu taba mantawa da taimako da hallacin ku ba" duka kudin dake aljihunshi yaciro, shima Muji haka, duk suka ijiye Moddibo yace "a'a" Buba yace "dan Allah ku amsa" Modibo yakalli matarsa yace "kawo kayanta Hawaro kawo magungunanta" shigowa sukayi suka kawo Ammi takarbi maganin Hawaro na mata bayani, gently Riyad yakama hannunta vace "muie gida" "gida?"Gyadamata kai yayi yatashi amman taki tashi, ganin haka yasa Muji yace "muje mota nabaki soda" yanuna mata goran sodan, da sauri ya tashi ta kalli Riyad tace "soda" gyadamata kai yayi yace "muje mubaki" yana rike da hannunta suka taho har zuwa wajen machine, ahankali Riyad ya kalli Mai machine yace "bani key saika hau na wani kabiyomu" dasauri Mai Machine din yabashi sukuma yan sandan sukace muje ku nuna mana inda kuka ganota, hawa machine din Riyad yayi yajuyo yakama hannunta yarike kafanta yayi guiding nata tahau hannayenta yakama yasa ajikinshi dasauri tai lamo abayanshi kamanyar baby tana shakan kamshin dayake dakemata dadi har zuciya, yadan kallonta sannan ya kunna machine din duk sukaja har zuwa wajen motocinsu suka sassauka da sauri Muji yabude mota yadauko drink yabata karba tayi sai tahau tsalle tace "yayyyyy" riketa dasauri Riyad yayi dasauri ta kalleshi saita bashi drink din karba yayi yana mata murmushi yabude bayan motan yace
"shiga" shiga tayi yazauna yabude yabata sannan yashiga shima ya zauna Munir da Sarkin Gida suka shiga gaba akaja motan sai Kano.
Ko nisa basu yiba ta Shanye drink din takalleshi tareda bashi goran tana turo baki kaman zatai kuka alamun she wants more, cikeda so yace "I will buy for you soon" tsayawa tayi ta kafe fuskanshi da idanu sai shima ya tsaya yana kallonta ahankali tasauke idanunta takalli agogonshi da sauri tadaura hannunta akan agogon tashiga shafawa hannunshi yasa sai ya kwance Rolex din yakama hannunta yashiga samata wani tsalle tayi tana kallon agogon sai rawa take da kafa chan kuma saita kwanto jikinshi tana hamma kallonta yayi yace "kinajin bacci?" Lumshe idanunta tafarayi, ahankali yakai hannunshi kan waist dinta dasauri ta kalleshi jinjikinta yamata wani iri daban da yanda takeji since, batare daya damuba yasata ajikinshi kaman yanda ake daukan babies da za'a shayar sai kallonshi take kafin gently ya rungumeta a kirjinshi ya kankameta yana sauke ijiyan zuciya lamo tayi ajikinshi within few minutes bacci yayi gaba da ita. Kiss Riyad ya manna mata gently a forehead kafin ahankali yadaura hannunshi saman cikinta Hakkika Allah shine mai azurta bawansa da haihuwa aduk sanya yaso yakumaga dama! Sex din dayayi da ita that was unplanned and out of anger but Rashida got pregnant dashi, he slept with Haleema on so many occasions cikinsu harda ranakun ovulation nata but shiru babu ciki. Allah is the greatest of all mankind!!!
Babban private asibiti suka wuce da ita har lokacin da sukakai bacci take, daukanta Riyad yayi zai daura ta kan gado da aka kawo musu tabude ido, rirrikeshi tayi tana dirkowa daga gadon tafashemai dawani irin mugun kukan shagwaba tana shishigemai jiki shikuma duk yawani daburce wucewa kowa yayi suka shiga asibitin aka barsu ganin da Riyad kawai jininta yahadu.
Ganin haka yasa Riyad cikeda lallabawa yace "why are you crying" kallonshi tayi saikuma tasa kanta a kirjinshi tana rike riganshi tashiga makemai kafada, ahankali cikin lallashi yace "let's go inside kanki za'a duba dake miki ciwo" yakai hannunshi yataba kanta wajen ciwon hakan yasa itama ta taba kan nata tana kallonshi gyadamata kai yayi yama nurses din alamu da hannu sutafi sannan yarike hannunta tabishi ciki har lokacin tana taba kanta yanda yayi har office na
Dr dayasa kawai suka wuce wajen MRI nan ma da ihu da kuka ta shiga akayi aka fito da ita aka debi jininta akakai lab, daza'a taba kanta nanne Riyad yaga tashin hankali ba karamin zafi kan yake mata ba tadinga inu ahaka aka cire all magungunan aka mata proper dressing dan local stites din yayi aiki nan da nan aka kawo result her head its fine kawai short term memory loss ne dazai dawo with help na medication saikuma she's truly pregnant Riyad sai kallonta yake tana wasa da agogonshi daya daura mata a hannu, she's truly pregnant!.
Chapter 85 · 0% Book details