Sashe 80
Sanyi Da Zafi Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
not just Bilal dazaran na haifesu ina bude musu savings account wanda idan sunyi girma zan basu su kama sana'a dashi, ranan juma'a da daddare yatasani gaba yanason nabashi nashi zaiyi business banso bashiba amman harda kukan sa shine na bashi da daddaren ranan bansan meyayi dashi ba" dasauri yakalli Bilal yace "mekai da kudin Bilal? Talk!" Baban yamai ihu dayasa sai jikinshi yafara rawa yadan kalli Riyad daya kasa ganeshi yama kasa tsayawa yamai cikakken kallo sabida kwarjini dayamai dan yasa rawani saikuma yace "Dad wata yar ajinmu nabamawa shima aro ne zata biyani, hauka nake zanma wata kyautan 22M azamanin nan" ahaukace Baban yace "bakaji maganan da Mai Martaba yayi ba iyalan Mai Martaba kabawa kudi!" Faduwa sosai gaban Bilal yayi yanzu mai Martaba ne dama shine Ogan Dady fa, shine mijin Rashida, dasauri ya kali me Martaba saikuma ya sauke kanshi akasa yace "wlh bata gayamin tanada miji ba kuma ni bama wani sonta nake ba Dad tausayinta kawai naji naga yanda take son.... ." "Sarkin Gida!" Riyad yakirashi azafafe da saida dakin ya amsa, dasauri Sarkin gida ya zube agabanshi hakan yasa Riyad yace "menene hukuncin wanda yaje yake neman iyalin Sarki?" Dasauri Sarkin gida yace "bulala dari bakwai! Kullum anamai dari dari har tsawon kwana bakwai a baya tare aiki amatsayin bawa, banda haka ai duk garin kano babu wanda ya isa ya nemi iyalin sarki koda sarki yarabu da iyalansa ne, bata isa tasake aure acikin kano ba saidai tafita taje chan wata kasar tai aure! Wannan shine sharadin auren sarakuna". Babu mutunci ko kawaici Riyad yace "a hukuntasa" dasauri Bilal yarike Babansa ganin fadawa sunyo kansa yace "Dad please save me wih, wih bansan wa take aure ba, Dad I just wanted to help the poor innocent girl tunda bata sonshi nasan nima da wuya nasan zaka banni na aureta, please kayakuri wh banasonta, waye ni dazan nemi iyalan Sarki ban isaba" kawai kallonshi Riyad yake he's not even Man enough yayi admitting yana sonta in trouble, how could Rashida be this gullible, this is a boy not a Man! Dagashi akayi yana mikama Babanshi hannu yafashe da kuka akai waje dashi. Daga Riyad sai Baban Bilal yarage da mutanen dake fifita shi, da hannu yama masumai fifita alamu sufita daga dakin, dasauri Baban Bilal yace "Mai Martaba temper justice with mercy dan Allah, wih Bilal yaro ne baida wayau he's 26yrs and last month ma yayi 26din, dan Allah amai afuwa ni wih zan cire shi daga school dinma wh, dama daga Sudan yadawo nan sabida yakin dasukeyi but namaka alkawari zan karbi transfer zan maidashi Egypt yaje yakarasa awajen dan Allah kayakuri he's just a child, dan Allah me Martaba dan Allah, namaka alkawari shi da Iyalinka ko hanya bazasu kara hadawa ba, Bilal yayi kuskure ina rokonmishi afuwa" kallonshi Riyad yayi saikawai yatashi yafice daga fadan yafito yanajin yanda ake ma Bilal bulala a bombom yana ihu ya kalli Sarkin gida yace "after 100 bulalan kabawa babanshi shi su tafi no need for the remaining 6days cane" yana maganan yawuce yafito daga bangaren Waziri yagani tsaye tareda amininsa suka kalleshi tareda dukawa atare sukace an gaida mai Martaba munzo wajenka ne" wucewa yayi yazauna wajen yar shakatawa sa yasa aka musu iso suka taho zama duk sukayi ya zuba musu idanu baice uffan ba, anatse Waziri yace "ahhhm Mai Martaba nasan an maka laifi" yadanyi shiru yace "dudda nai kokarin maka magana hakan be yu ba, still yauma bazan gajiba, burin kowani mahaifi yasa diyarsa agida mai kyau hakika nasan Haleema tai kuskure shirmene kuma da yarinta wanda har zata dauki wata ta maidata kaman ita take aure ga mijin nata bazata girmama shi ba" yasake shiru sannan chan yace "Haleema tagane kuskurenta Allah taimaki me Martaba, da ni da amini na nan Muntari munzo mu nema mata afuwa ne tadawo dakinta duk ku taru da amaryan taka ayi zaman Ipy" baiyi wani mamaki ba yasan by now maganan ya auro Rashida yazagaye fada dakuma wacece Rashidan. Anatse Muntari aminin Waziri yace "abata second chance dan Allah" shifa to be honest bayason Haleema he can't lie about it ne, forget about abubuwan datamai basune agabansa but wannan soyayyan baya jinsa game da ita, but then baitaso yaga Babanshi yarabu da kowace matarsa ba duk dadi duk runtsi ana tare banda haka he knows Haleema loves him kawai she prioritized Mom over him ne, he saw calls nata, messeges nata telling him sorry so he will give her second chance, idan she fails yarabu da ita gabaki daya, kallonsu yayi yace "tadawo dakinta!" Wani dadi sukaji sukahau mai godiya gaisawa yayi dasu yawuce Allah Allah yake yagama da mutane yaje yaduba Rashida fada yawuce. Suna shigowa gidan sama Ammi suka wuce da ita sharp sharp takira Jakadiyanta wasu itatuwa da ganyayyaki aka samo aka girka a murhu aka kawoma Ammi sama, ijiye kunya Ammi tayi a gefe tunda ba Mama Rashida ke dashi da zata mata ba itace Maman yanzu, tagasa Rashida da kyau ita kanta saida ta tausaya mata ta wahalu fa, sannan ta matsa mata jiki gabaki daya da towel dake mata ciwo, suka fito daidai Dr Ammi na zuwa dubata tayi tacema Ammi basai anyi dinki ba but taji ciwo sosai tacema Ammi please kar abari yasake mata wanitacema Ammi please kar abari yasake mata wani abu harsai ta warke sannan tamata allurai tabata magani harda na tsayar da aman duk tasha Ammi da kanta Ammi tasauka kasa tamata kunu takawo mata sha tayi kadan sabida yanda ta matsu sai bacci Ammi sai shafamata kai take dayake ajike tayi shiru tana kallonta on her hand, she's happy Riyad yayi consummating aurensu wih har ranta she's, azamaninsu da suna yara idan yarinya ta taso da tsaurin ido bata tsoron kowa ga rashin kunya akance amata aure zata natsu, murmushi Ammi tayi tabude balm tana shafa mata a gefen baki wat she's certainly not happy about is marin daya mata! Da kuma forcing nata dayayi no ba'a haka dudda tasan waye Riyad wih bakaramin abune aisa yadaga hannu ya mari Rashida ba ayanda yakesonta it must be big abu dudda taki bashi listening ear but tasan abu tamai dayakaishi ga marinta haka, ijiye balm din tayi har zuciyanta takeso Rashida taso Riyad itama suyi zaman su lafiya cus she knows and sees yanda Riyad ke sonta, ahankali tace "I pray Allah ya sanya miki son d'ana aranki Rashida, please love Riyad kinji he's a good boy" Ammi tayi maganan ahankali daga sama tanajin kamshin tsumin da Jakadiya ke hadawa, ahankali ta maida kanta filo ta kwantar sannan taja bargo taruta mata tafito tasauka kasa magunguna na gargajiya suka shiga dafamata harda gyaran jiki Ammi zata mata takuma gyarata da turare dan wih bazata bashi itaba saiyaga chanji zaici kaniyansa. Shigowa Jakadiya tayi dawani leda a hannu na magunguna dataje tasayo takawoma Ammi a kitchen tace "Uwardakina Sarauniya Haleema tadawo" dan kallonta Ammi tayi saikuma tace "Masha Allah, bani ledan kigani kin sami sassaken danace" karba tayi suka cigaba da aiki batare dadanace" karba tayi suka cigaba da aiki batare da Ammi tace wani abuba. After magrib Riyad yashigo gidan tareda Munir Ammi na zauna akan dadduma a falon tanajan charbi waje suka samu suka zauna har Ammi ta shafe ta kalleshi da sauri ya sauke kanshi kasa Ammi tace "banace karka sake ka shigomin flat dina ba" kanshi akasa yace "Ammi kiyakuri" shiru tayi sai chan tace "Haleema tadawo ko"? Aahankali kanshi na kasa still yace "yes" shiru tasakeyi sai chan tace "an ina kakeso Rashida ta zauna anan masarauta ko chan GRA"? Shiru yayi baiso ya ijiye Rashida a masarautan nan cus baiso wani ya cutarda ita, yarinyar has been through alot already he don't want any more drama a life nata, peace kawai yakeso yabata ahankali yace "GRA is her house Ammi" anatse Ammi tace "good! Sai magana ta biyu dazan maka karaba musu kwanaki?" Girgixama Ammi kai yayi, anatse Ammi tace "don't think sabida Mahaifiyar Rashida tarasu batada me tsayamata Riyad wih she has me! Mata biyu gareka even though she's here with me pending decision nata idan ta warke whether tana sonka ko bata sonka you have to raba musu kwanaki cus matarka ce, ranakun Haleema kaje kayi da ita ranakunta kayita walagigi a fada that's your punishment" danne dariya Munir yayi yanda yaji Ammi tace "walagigi" juyoda kai Ammi tayi karaf suka hada idanu da Munir tace "zan cimaka mutunci fa ina magana da yayanka kake dariya tashi kabarnan" Sadaf sadaf yatashi yayi sama kaman munafuki Ammi takalli Riyad da kanshi ke kasa tace "ka manta yarinyar nan na school ne kamata abinda kayi ko? Ai kaji dadi dan yanzu she will stay at home harta warke ana maganan nan da 2weeks ko 3 kenan, idan wani abu yasami karatunta just know cewa its on you!" Har lokacin kanshi akasa saikuma ta sassauta murya cikeda motherly love tace "yarinyar danakeso tasoka why will you hurt her like this eh Riyad? Metayi maka haka?" Ahankali yace "Ammi kiyakuri" shiru Ammi tayi tasan bazai taba gayamata abinda yahada su ba haryakai ga marinta hakan yasa tace "anyway kazama mai adalaci problems naka da Haleema sort them out, be a man manage family naka da kyau, ko kaje dakin matanka ko call them to turakanka banso na karaji kaman yanda kayi da kabar Haleema for months baka ganta ba bata ganka ba, idan namiji yayi tsaye kan mace shine zatasan eh inada miji and do the right thing, dan haka from now henceforth do your part kayi adalci kaji ko" gyadamata kai yayi Ammi tace "and make her cook for you daga yanzu bazaka dinga zuwa side dina cin abinci ba, the only day dazan daga maka kafa is ranakun girkin Rashida tunda tana wajena batada lafiya you can come here kaci abinci amman other days baka isaba kaji ko"? Gyadamata kai yayi Ammi tace "tashi katafi to" kasa tashi yayi kanshi na kasa tsaf Ammi tagane meyake nufi Rashida yake son gani tace "ni zaka firgitama yarinya takasa bacci taga dodo da daddaren nan ai ina Riyad! Tashi kabarmin daki koni yanzu kazaman mini ojuju calabar a idanu balle muku baiwar Allah Rashida, tashi kaje wajen matarka