← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 38

Sashe 9

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shigo gidan ya ga tsumma a kan igiyar shanya, bai kawo komai a ransa ba ya cire ya tsoma cikin ruwan Omo ya fara wanke machine É—in Abba da shi.

Kamar daga sama ya ji wata siririwar murya tana salati a bayansa ya juyo a ɗan firgice dan ya ɗauka ba kowa a gidan na su, biki ake a gidan su Addaye ƙanwar Abba, duk 'yan gidan suna chan.

"Lahaula... Sallalahu Alaihi wa Sallam. Tsumman abuna!" sai kuma ta riƙe baki tana zaro ido.

Ubaydullah yana riƙe da tsumman ya kalleta da mamaki ya ce "tsumman miye? Tukunna ke daga ina?" Bai yi aune ba Siririyar yarinya mai wushirya ta yi wuf ta karɓe tsumman daga hannunsa ta shige ɗakin Umma da gudu, bai ƙare mamaki ba sai daya ji ta bugo ƙofar ɗakin da ƙarfi.

Shi kam bai gane mi ya ke faruwa ba. Ya dai ƙarasa wanke machine ɗin hakanan.

Har ya gama abunda zai yi ya fita yarinyar ba ta fito ba. Sai bayan magariba daya dawo gidan ya tambayi ƙanwar sa Ummi wace baƙuwa su ka yi a gidan. Ummi ta sanar da shi 'yar Umma Kurma ce itace Asiya Shahidan ta da Abba ya basu labari.

Tun daga lokacin kuwa Asiya ke gudunsa har ranan da ya titsiye ta yana tambayarta miye dalilin ta na ƙwace tsumman ranan. Yadda ta dinga inda-inda ne ya sa ya fahimci tsumman miye.

Ƙannensa sun wuce nan ai dan tun lokacin da ya taɓa kama ƙanwarsa Ummi tana ɓoye tsumma cikin zani ya ɗaurawa kansa siyawa ƙannensa audugar mata tun ma yana shekaru shabakwai kenan balle yanzu daya ke shatara shigar sa Jami'a ya sake wayewa.

A ranan ya je ya siyowa Asiya auduga ya bawa Ummi ya ce ta nunawa Asiya yadda za ta yi amfani da shi.

A hankali-A hankali kafin ta ƙare hutun ta dena jin kunyar sa tana ɗan sakewa da shi. Tun tana zuwa hutu gidan har ya zamo lokacin da za ta shiga Jami'a ta dawo gidan su da zama gaba ɗaya.

Har yau idan yana son ya tsokali Asiya to kalmomi biyu kacal zai faÉ—a ya tunzurata *"tsumman abuna"*

Bai bar gidan ba sai ƙarfe goma saura minti biyar nan ma dan baya son tsallake dokar Abba ne wato baya son hiran ƙarfe goma.

Asiya na komawa ɗaki da ta duba wayarta ta ga saƙon KaSaSa a email ɗinta wanda waƙar da ta rubuta yau akan mutuwa ne, wanda tai wa Marigayi Gwamna Saminu Bacchi.

Bayan ta karanta kuwa sai da ta tuno mutuwa biyu da su ka fi girgizata a rayuwarta. Mutuwar Kakanta Gwani da kuma mutuwar ƙaninta ɗan shekaru biyu wanda ya rasu a bayanta.

Auri sakin mahaifinsu ne ya je ya auro wata mai juju. Dan idan abu ya haɗata da sauran matansa duka ta ke musu, shima kuwa da ƙyar ya sha a wajenta ranan da ya mareta ta kamashi da kokawa sai da ƙyar aka raba su. Ba dan an raba da wuri bama alamu sun nuna Ale Faruƙ ne zai sha kashi a wajen Indo, dan Indo irin matan nan ne ma su ƙarfi, ga jiki ga tsawo. Ale Faruƙ na sane da dukan miji da akace tanayi wanda ya rabata da sauran mazaje uku da ta aura a baya amma ya rufe ido ya ce Indo-ƙarfi zai aura.

Bayan faÉ—an ne kuwa Ale FaruÆ™ ya saketa ashe tanada ciki. Da ke ba ta da hankali yaron ko suna ba ayi ba ta zo ta ajiye shi gaban Tabawa mahaifiyar Ale FaruÆ™ wai ga tsiyar su nan.

Haka yaro ya taso ba gata. Tabawa ma da ƙyar ta ke kula da shi dan Ale Faruƙ baya kawo kuɗin madara sai ta tsiya-tsiya.

Da yaron ya fara wayo ba shi da wata gata a gidan sai ta Asiya. A haka ya taso a yarjale har Allah ya ɗau ransa lokacin yayi wani zazzaɓi mai zafi Asiya ta goya shi tana jijjigashi a bayanta saboda kuka dayake ta tsalawa har Allah ya karɓi ran sa. Shekarunta tara a lokacin amma har yau ba ta taɓa manta yadda abun ya faru ba. Ya jima da rasuwa a bayanta ba ta sani ba har sai da ta zo kwantar da shi lokacin za ta yi wanki dan ta ɗauka bacci yai sai ta ga idonsa a kafe ta fara jijjigashi amma inaa babu alamun motsi nan ta saka ihu ta fita tana ƙwalawa Tabawa kira...

***

"Seriously Justice ina tsoro. Kwana biyun nan bana iya bacci fa. This is so sudden for me"

Bayan Justice Yunus ya gama yi ma sa nasiha ta jan hankali ne ya ce "Shikenan na gode. Ka gaida Maman 'yan biyu"...

"Kai da waye a waya?"

Ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajensa tana zuba ƙanshi.

"Justice"

"Oh Galadima. Hope zai zo rantsarwar ka"

" i dont think so dan ya ce suna Las Vegas"

"Ayya! Allah ya dawo da su lafiya. Muma gashi babu halin tafiya tunda ga yadda lamarin Ubangiji ya kasance. Just like a dream"

"Just like a dream kam. Har yanzu ina jimamin mutuwar Gwamna"

"Haka Allah ya ke lamarinsa. Idan lokaci yayi babu makawa sai an tafi"

"Hakane. Muma duk lokaci mu ke jira"

Kallonta yai da kyau sannan ya É—aga gira sama ya ce " sai ina?"

"Zamu je shopping ni da yara. Duk cikin kayan su babu na zuwa swearing in naka a ciki. I think dole a chanja mu su wardrobe kwanan nan"

"Hmmm. I trust you Bilkisu" ya faÉ—a yana É—an jijjiga kai

"Miye?"

"Allah ya kiyaye hanya"

Kiss ta manna ma sa a baki kafin ta fice daga É—akin ya bi bayanta da kallo. "Mata kenan, wai duk cikin kayan da ta ke dasu babu na zuwa wajen rantsarwar sa da za ayi ranan Monday".

"Seriously Mommy i cant believe yanzu mune first family of the state" Nana ta faÉ—a tana dariya

"Well get used to it, dan yanzu aka fara governor's daughter"

Bilkisu ta faÉ—a tana murmushi.

Nana ta saka ihu.

Har su ka isa Kachallah House hiran yadda rayuwar su za ta kasance yanzu su ke yi.

Sai da su ka fara isa ɓangaren Hajiya Aisha wato mahaifiyar Bilkisu kafin su ka wuce gaida Dadda mahaifiyar Alhaji Sani Kachallah.

Ko da su ka gaisa Bilkisu ta tambayi ina Mahira ta ke, Dadda ta ce ta wuce Islamiyya.

"Yanzu yarinyar nan abinda za ta min kenan bayan na ce ma ta zamu zo"

"Inaga ta manta ne" Dadda ta faÉ—a tana tauna goro.

Ba su jima a gidan ba su ka wuce bayan sun barwa Dadda saƙo akan idan Mahira ta dawo ta je gida Bilkisun na nemanta.

***

Farar Shadda ya saka ɗinkin babbar riga haɗe da baƙin hula zanna, ya saka baƙin shoe ƙirar Loius Vitton. Ya duba kan sa a madubi ba ƙarya ya fito sosai. Sai dai a ƙarƙashin wannan kayan zuciyar sa ce ke bugawa da ƙarfi kaman za ta ɓula ƙirjinsa ta fito.

Lokacin da aka rantsar da shi a matsayin mataimakin Gwamna bai tsinci kan sa cikin fargaba da tsoro kaman na yau ba kodan yanzu matsayinsa ya chanja ne?

Ya fesa turarukan sa ma su ƙanshi guda uku sannan ya fito daga ɗakinsa ya wuce ɗakin Bilkisu. A tunanin sa ta gama shiryawa amma har lokacin ana kan yi mata kwalliya. Tamkar biki za a yi haka Hajiya Bilkisu ta nemo professional make up artist da za ta gyara ma ta fiska yau.

"Your excellency" mai kwalliyar ta faɗa tana wani ƙamewa.

Bilkisu ta ɗago ido ta ce " Darling ka gama shiryawa, yi haƙuri yanzu zan gama nima"

Tun kafin ta ƙarisa maganar ya riga ya fice inda ya wuce ɗakin yaran sa. An gamawa Nana da Airah kwalliya Mahira ake yiwa lokacin daya shigo. Fiskarta tamau alamun ba ta so a dole ake mata. Ya sani ta ɓangaren son ƙyale-ƙyale kam Nana ce ta ɗauko komai na Bilkisu amma Mahira bai dameta ba.

"Daddy Governor" Nana ta faɗa tana ƙarasowa wajen sa.

"Yi a hankali N Luv kar ki ɓata ma sa farin kaya" Airah ta faɗa daga inda ta ke zaune tana danna waya.

" Daddy selfie É—aya kafin ka tafi please"

Bai so ba amma dole haka ya tsaya Nana ta mu su selfie kafin ya wuce É—akin Junior inda tuni Hansa'u ta shirya shi dan lokacin da ya shiga É—akin ma yana buga game ne. Ya kama hannunsa su ka fice daga É—akin...

Kotu ya cika maƙil da mutane da kuma 'yan jarida. Bayan Alƙali ya shigo ya tsaya sannan Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ya shigo biye da bodyguard ɗin sa. Bilkisu kaman ta narke saboda farinciki ganin Mijinta a gaban Alkali wai za a rantsar da shi a matsayin Gwamna.

Lokacin da SSK ya dafa alƙur'ani ya maimaita kalmar da Alƙali ya faɗa wato*I...Saifuddeen Sa'ad Kachallah. Do solemly swear...* lumshe ido Bilkisu ta yi sannan ta kai dubanta ga ɓangarenta na dama inda Alhaji Sani Kachallah ke zaune ɗauke da Junior a cinyarsa. Irin yadda fiskarsa ke washe da farin ciki da annashuwa ko ita da ta ke Matar Saifuddeen albarka. Mahaifinta shine musabbabin saka Saifuddeen a harkar siyasa and yanzu ne zai ga alfanun sadaukarwar da yai a rayuwar Saifuddeen domin yanzu shi ɗin Gwamnan Jahar Congo ne....

***

Asiya ba ta yi tsammanin kira daga MD É—in su ba dan rabonta da shi tun ranan da aka bata suspension letter.

Sai da ta ƙarisa aikin da ta ke yi kafin ta wuce office ɗinsa.

"Sannu da aiki Sir"

"Yawwa Asiya. Ya aikin?"

"Alhamdulillah"

"Inada assignment da za ki yi. Idan kin carrying out na shi da kyau za ki dawo aikin ki na da"

Washe fiska Asiya ta yi ta ce "Sir wani assignment ne?"

Wata takarda ya tura gabanta ya ce "muna so ki yiwa Gwamna Interview"

Murmushin fiskar Asiya ya ɓace ɓat. Wata na biyu kenan da SSK ya zama Gwamna kuma har yanzu ya ƙi yin interview da kowani gidan jarida. Sau ɗaya yai press conference sati ɗaya bayan an rantsar da shi a matsayin Gwamna.

"Sir i think Hill TV ta nemi hira da shi kwanakin baya kuma ya ƙi"
Chapter 9 · 0% Book details