Sashe 6
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ai inaga ke ce dalilin wannan albashin, da safe da ki ka yi maganan albashin nan zuwa ƙarfe ɗayan rana mutane sun fara ganin alert. Ni nawa ya shigo ƙarfe uku da rabi ne lokacin ina Alwala a masallaci"
"Mugu ba. Yana tsoron kar ubangidan sa ya dawo ya samu bai biya albashi ba ya haushi da faÉ—a"
"Ikon Allah, yanzu ya biya albashin ma bai miki ba"
"Dama ya so yin kasuwanci da albashin mutane ne, Allah ya kamashi"
Ubayd ya girgiza kai kawai ya wuce É—akin Inna Yaha dan ya kai mata nata kayan.
***
Yau Gwamna ya dawo daga tafiyar da yai, kusan ya ƙara kwanaki biyu bisa ranan daya ɗiba zai dawo. A ranan ne kuma abubuwa da dama suka faru.
A chan gidan Yallaɓai Alhaji Kachallah ne zaune a falon gidan yana jiran fitowar Yallaɓai. Kusan minti ishirin da biyar yai yana zaman jiran sa kafin ya fito yana dogara sandar ƙarfe wacce ta ke ta ado ba wai dan yanada matsalar ƙafa ba.
Minti biyar ya ɗauka yana yiwa Yallaɓai bayanin abinda ke tafe da shi.
Ya ƙara da cewa " ina fata idan lokaci yayi ba za a juya min baya ba"
Yallaɓai yai murmushi ya ce "Alhaji Kachallah ka sani sarai bana magana biyu. Abu ɗaya ne zai sa na chanja maganata, idan har shi ya karya dokar wannan tafiya"
"Ina tsoron kada Mr Paul ya idda mugun nufinsa. Idan har kujerar mataimakin Gwamna ta kuɓuce mani, Yallaɓai za a samu matsala a wannan tafiya"
"Ka kwantar da hankalinka ba abinda Mr Paul zai iya yi"
Alhaji Kachallah ya miƙe ya ce "ni zan wuce"
Bayan tafiyar Alhaji Kachallah Yallaɓai ya dubi kujerar da Alhaji Kachallan ya tashi akai, itace dai kujeran da Mr Paul ya zauna akai jiya yana kawo ƙorafinsa akan a dakatar da tafiyar Alhaji Kachallah saboda akwai giɓi sosai a tafiyar ta sa.
"Ba shi da experience ko kaɗan a wannan harka Yallaɓai. Yanada sanyin zuciya idan aka ɗaura shi akan kujera zamu samu matsala da shi. Ya kamata a datse..."
Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu. Mr Paul yai tsit yana zazzare idanu.
Yallaɓai yai murmushin gefen baki, yana son irin wannan wasan...
***
Cikin shiga ta alfarma shiga ta ƙasaitattun mata Hajiya Bilkisu ta fito daga ɗakinta. Wani tsadadden leshi fari ta saka ɗinkin buba da zani, ta saka takalmi mai tsini kalar ja wanda yai dai-dai da kalar clutch bag ɗinta, ɗan kunne da awarwaro da kuma sarƙa,
Tana takunta ɗaiɗai har ta sauko ƙasa.
"Hajjaju Makkatun, Hajjan Gwamna, Hajjan mu" ta faɗa tana ƙyalƙyalewa da dariya tana ɗan tafa hannu.
"Hansa'u kenan"
"Hajja idan na girma ina son zama kaman ki"
Wani lokaci takan ɗan tausayawa Hansa'u. Wacce ta kawota ta gaya mata cewa auren wuri aka mata tana shekara goma shauku, ta wahala sosai a wajen Kishiyarta. Tana shekaru shabiyar mijin ya rasu. Ba a jima ba ta haihu ɗan bai zo da rai ba wannan psychological trauma ɗin shine ya taɓa ma ta ƙwaƙwalwa. Anyita magani ana tunanin Aljanu ne ko sammu amma shiru. Bayan shekaru ana jinya shine wata Gwoggonta ta kawota Birni dan ta koyi sana'a tunda ta ƙi auruwa. Hansa'u akwai aiki kam amma akwai shirme da shiririta dan har yanzu hankalin ta kaman na budurwar ƙauye ce 'yar shekaru shabiyar. Kusan ko da Hajiya Bilkisu ta girmeta to abinda za ta bata ba zai wuce shekaru biyu ba.
"Hansa'u Malamin Junior ya zo ko?"
"Eh Juno yana karatu da malamin sa a waje"
"Good, idan ya gama lesson ki tabbatar yayi wanka kafin ya ci abinci. Ni zan fita"
"Hajjan mu a kawo mana tsaraba"
Hajiya Bilkisu ta É—an yi dariya sannan ta fita daga gidan ta nufi motarta inda driver ke jiranta.
Kai tsaye gidan Gwamnati aka wuce da ita. Ba wannan ne farkon zuwanta gidan ba amma abin mamaki ba a bari ta ƙarisa falon First lady ba kamar yadda ta saba yi idan ta zo. Mai aikin gidan ta ce ma ta First lady na da manyan baƙi dan haka ta jira a falon baƙi kafin su tafi.
Da farko abin ya yiwa Hajiya Bilkisu banbaraƙwai saboda irin haka bai taɓa faruwa ba amma daga baya sai ta yi tunanin ko dai first lady na tare da surkuwanta ce. Ba abu ne ɓoyayye ba a wajenta irin takun saƙa da ke tsakanin First lady da Maman Gwamna. Rabuwa su ka yi da matarsa ta farko wacce sun yi kusan shekaru ashirin da biyu tare kafin su ka rabun, hakan kuma ba ƙaramin ƙona ran mahaifiyar Saminu Bacchi yai ba, Murjanatu itace uwar 'ya'yan sa guda shida amma haka ya rufe ido ya shure ya saketa ya auro Hajiya Sha'awanatu. Kusan shekaran su bakwai da aure amma har yanzun tsakaninta da Mahaifiyar Saminu Bacchi ba sa ga maciji.
Zaman jiran da ta ke gani ba zai wuce minti ishirin zuwa talatin ba shine ya zamana har ya wuce awa biyu.
Sau biyu tana turawa a duba ma ta first lady amma sai a ce tana tareda baƙi.
Tun Bilkisu na É—aukan abun ba komai ba har ya zo ya fara ba ta haushi.
Awa uku da zamanta a falon ta miƙe tsaye dan ta wuce gida zuciyarta cike da ƙuna. Barka da dawowa ta zo yiwa First lady ba wai zaman walaƙanci ba. Ko bakin ƙofa ba ta kai ba ta jiyo shewar first lady da wasu mata. Ta juya a fusace dan ganin su waye su ka fita mutunci a wajen first lady ɗin, lokacin da ta juya first lady ce ke saukowa ƙasa biye da ita kuma Hajiya Hadiza matar Senator da Hajiya Kaltume matar Commisioner.
Hajiya Bilkisu ta bi su da kallon mamaki. Saboda waÉ—annan matan First lady ta zaunar da ita na tsawon awa uku.
"Ba ki tafi ba?" First lady ta faÉ—a da mamaki
Hajiya Bilkisu ta buÉ—e baki cikin kaÉ—uwa.
"Bilkisu Kachallah. Ashe ke ce ake ta damun First lady wai tana da baƙuwa"
Hajiya Hadiza kenan da wannan magana.
"First lady saboda waÉ—annan kika shanyani kaman kayan wanki" ta yi maganar tana nuna su.
"Tabbas saboda su kuwa. Bilkisu na ji duk abinda kika yi tun kafin na dawo amma ki sani ba zan lamunci hakan ba. Taron matan Gwamnoni aka ce za ayi ba na matan mataimakan Gwamnoni ba. This is the last time da za ki sake haÉ—a taro idan bana gari"
"Sai da muka gaya ma ta ta bari ki dawo kafin ayi taron nan amma ta ƙi. Wallahi matar Gwamnan Ekiti sai da ta gasa mana magana a wajen taron nan, kin san yarabawa ai"
"Ni! Ni ki ke wa munafurci Hadiza?"
Hajiya Hadiza ta juya kai tana tura baki.
"Ki tsaya iya matsayinki Bilkisu sai a samu zaman lafiya" First lady ta faÉ—a a fusace
Hajiya Bilkisu ta haɗiyi wani abu daya tokare mata maƙoƙoro.
"Nagode First lady. Dama na zo yi miki barka da dawowa ne amma na ga alama ba ki cancanci gaisuwar ba. Mu kwana lafiya"
Hajiya Bilkisu ta juya da sauri ta fice daga gidan.
A cikin mota danne ƙirjinta ta yi saboda yadda ya ke bugawa yana sukanta. Ba ta iya ɓacin rai ba dan tana farawa zuciyarta ke fara ciwo. Shekarun baya ance tanada hawan jini shiyasa ta ke kaffa-kaffa da duk abinda zai ɓata ma ta rai.
Bayan ta koma gida ba wanda ta kula ta wuce ɗakinta ta sa key sannan ta kwanta akan gado har lokacin ba ta cire hannu a ƙirjin ba dan ji take idan ta cire zuciyarta zai iya bugawa. Ƙarshe ta tashi ta ɗauko maganinta ta watsa a baki ta haɗiye zuwa minti shabiyar maganin ya fara aiki dan bugun ƙirjinta ya fara raguwa.
Idan ba ƙaddara ba da First lady da Hajiya Hadiza da ita Hajiya Kaltumen dukkan su babu sa'anta cikin su. Idan ba muƙami da mazajen su ke riƙe da shi ba babu wadda a cikin su ta taka ƙafarta wajen gata da daraja. *Bilkisu Sani Kachallah* ce fa. Waye bai san tarihin ahalin gidan Kachallah ba. Familyn Kachallah su ne da Jahar Congo gaba ɗaya.
Bilkisu Kachallah ba za ta iya tuna lokacin da bacci ya É—auketa ba. Ta dai farka tsakar dare ta ganta kwance da kayan jikinta sai alokacin ta tashi ta cire kayan ta saka na bacci sannan ta dawo kan gadon ta zauna dan bacci ya washe a idonta, tunani kala-kala ta zauna yi har Asuba.
***
Shahidah na bacci wayarta ya hau ƙara. Ta sa hannu ta jawo wayar da ke gefen gado saura kaɗan ya faɗo ƙasa.
"Hello" ta faÉ—a da muryan bacci
"Mine kin tashi kuwa? Na kusa isowa fa"
"Ka manta anyi suspending É—ina jiya"
"Subhanallahi! Ok ok barin zo in gaida Abba sai na wuce office..." ai bai ƙarisa bama Asiya ta kashe wayar saboda baccin da ke cinta.
Da sassafiya Bilkisu ta shirya ta sauko ƙasa. Daga wajen dining room wanda ke haɗe da babban falon ƙasa ɗan ta Junior ya ƙwala ma ta kira "Mommy" ta juya da sauri tana maƙalawa fiskarta murmushin bogi wanda ya ɓoye ɓacin rai da ta ke ciki.
"My boy"
"A'a Nana yaushe kika dawo. Zunairah ya Maman ki?" Ta jera maganar tun kafin ta iso wajen su
"Mommy ina za ki sani kuwa. Jiya ina miki magana haka kika shareni kika wuce sama. Daga baya na je na yita buga ƙofar ki amma shiru ba ki buɗe ba"
"Sorry Dear, jiya na gaji ne dayawa"
"Miyasa Junior ke cin abinci shi É—aya ina Hansa'u?"
"Hansa'u" ta ƙwala ma ta kira da ƙarfi
"Mommy Airah ce ta aiketa ta kawo mata boiled egg"
"Ok girls barin fita, idan Daddyn ku ya tashi ku ce ma sa na tafi Kachallah House"
Bayan tafiyar Hajiya Bilkisu sai ga Hansa'u ta fito da wani bowl ɗauke da ƙwai guda uku ta ajiye a gaban Zunairah.
Zunairah ta zaro ido ganin ƙwai da ɓawonsa a jiki sai tiririn zafi ya ke
"And what is this? N Luv kinga shirmen wannan crazy old fool É—in ko?"
Nana ta kalli Hansa'u ta ce " yanzu Hansa'u ita ki ke so ta cire ɓawon ƙwan kenan?"