← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 38

Sashe 14

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da aka katse shirin aka saka talle COS ya zame jiki ya wuce office ɗinsa. Abu ɗayane ya zo masa wato Asiya taji abinda ya faɗa idan ba haka ba babu yadda za ayi ta kawo maganar mutuwar tsohon Gwamna. Tunda aka bashi matsayin Chief of staff lokacin Gwamna Saminu Bacci ya saka CCTV a office ɗinsa saboda shiga masa office da akayi ba da izininsa ba aka bincika masa wasu takardu. Ya kori sakatariyarsa a lokacin amma ya sani ba da saninta aka yi hakan ba, bai jima ba kuwa ya gano wanda yai hakan. Babu wanda ya san yanada ɓoyayyiyar camera a office ɗin nasa. Kasantuwar Sakatariyarsa Jennifer bata desk ɗinta sanda ya shigo ya ƙara tabbatar masa da cewa Asiya ta ji wayar da yai tun ma kafin ya duba CCTV footage ɗin. Bai sha mamaki ba da yaga Asiya laɓe a bakin ƙofarsa da 'yar ƙaramar na'ura da yake da tabbacin recorder ce lokacin daya kalli footage ɗin.

Asiya tana waya da Ubayd wani security ya iso ya ce ta biyo shi. CY da Sunusi suka zaro ido tareda tambayar lafiya. Bai ce musu komai ba yai wa Asiya jagora suka bar wajen. Asiya ta tsorata amma ta dake bata nuna ba saboda kar ta bada kanta, yau duk yadda za ayi sai dai ayi amma bazata taɓa fito da recorder ɗin nan ba.

Office É—in Chief of Staff ya kaita kamar yadda tayi hasashe. Tayi mamaki da taga Sakatariya a office É—in farko wanda É—azo da ta zo babu ita. Lokacin da ta shiga office É—insa Mr Lamara Damana yana tsaye ya haÉ—e gira.

Jakarta security ɗin ya ce ta miƙo tana miƙa masa ya zazzage kayan ciki a walaƙance. Powder, lipstick, hankerchief, jotter, biro da earpiece ne a ciki. Wayar hannunta security ɗin yace ta kawo ta miƙa masa ba musu tana kallon COS da shima ya zuba mata ido yana mata kallon tsana.

Wata na'ura da ke detecting devices security É—in ya bi ya zagaye jikin Asiya da shi amma bai detecting komai ba.

COS yace ya miƙa masa wayar Asiya sannan ya basu waje. Bayan fitan security ɗin COS ya kalli Asiya ya ce "na san ba a waya kika ɗauki maganarba dan haka ki fito da recorder ɗin"

"Ikon Allah, ina tunanin ka manta cewa ni 'yar jarida ce, wannan cin zarafi da kake min zai ja maka matsala" Asiya ta faÉ—a a kausashe.

Wani murmushin gefen baki COS yai wanda idan ba lura kayi ba baza ka gane murmushin yai ba saboda yadda gefen bakin ya tattare kamar mai shirin kuka.

"Asiya Shahidah FaruÆ™ Baba. Na san kina sane da haÉ—arin da ke tattare da wuce gona da iri a cikin aikin ku"

"Are you threatening me?"

"You know better"...

Lokacin da ta isa wajen su CY ko magana ba ta musu ba ta wuce gaba suka bi bayanta suna tambayar miya faru. Sai da suka shiga mota Asiya ta karɓi jakar camera da ke hannun CY ta buɗe wani ƙaramin zip ta ɗauko recorder a ciki ta damƙe shi a hannunta, yadda ta damƙe shi har sai da hannun ya fara rawa. CY kallonta yake yi cike da tambayoyi a harshensa amma ya yi gum da bakinsa tunda tace musu kar wanda ya mata magana.

Maimakon office gida tace Sunusi ya sauketa. Tana shiga ɗaki ta samu Umma na wanki a tsakar gida, ganin Ummanta duƙe tana wanki ya tuna mata da washing machine da ta ce zata siya tun watan daya gabata. Rashin lokaci ya sa take bada kaya a wanke mata sai ta haɗa dana Umman amma tunda Umman ta ce ba ta son a fita mata da kayan wanki waje ya sa duk weekend indai tana gida take wanke kayan mahaifiyarta.

A tsanake ta gaisheta tace mata ta zo ɗaukan abune dan kar ta firgitata. Tana shiga ɗaki kai tsaye laptop ɗinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin tura abinda ta naɗa zuwa Laptop ɗin. Maganganun COS sun ɗan razanata amma idan ta tuna itama tanada abinda zai iya wargaza mulkinsu sai ta tausashi ranta.

Kafin ta gama abinda take wayarta ta shiga ruri. MD ne ta sani kuma ba zata kulashi ba sai ta gama abinda takeyi. A ƙalla ta kai awa ɗaya da rabi a gida kafin ta shirya ta koma office.

Ta É—auka MD zai mata faÉ—a kaman yadda ya yi a waya amma sai ta ji ya tausasa kalmominsa gareta "Asiya ban san mi kika naÉ—a a gidan Gwamnati ba amma ina so ki sani cewa zaki iya taka Gwamna ki kwana lafiya amma Lamara Damana ba zai barki haka ba"

"MD kana so kace..."

"Asiya na san kinada ƙoƙari sosai wajen dukkan ayyukanki amma ki sani ana iya barin halak saboda kunya"

Za tayi magana ya É—aga mata hannu sannan ya cigaba " already mutane sun fara reacting wa interview da kikayi amma nan da kwanaki kaÉ—an komai zai lafa, saidai idan kika sake bijiro da wani abun Asiya ba ke kaÉ—ai fitinar za ta shafa ba idan ba ki ji ta ma'aikatarmu ba to ta iyayenki fa?"

Jikinta yai sanyi ta kasa cewa komai.

"Asiya you are a field reporter not investigative reporter, kada kiyi aikin da ba naki ba. Faɗa da 'yan siyasa ba abu ne da ake ƙareshi ta daɗi ba"

"Sir, kana nufin na watsar da gaskiya na rungumi ƙarya kenan?"

"Ban san mi kika sani ba Asiya amma koma minene ki yiwa Allah ki haƙura dashi saboda mutuncin ki. Lamara Damana ba mutumin da za ki iya ja da shi bane"

"Shikenan na ji"

Bayan Asiya ta bar office ɗin. MD ya sauke ajiyar zuciya. Kashedi Chief of staff ya masa ɗazu daya bugo akan in har aka fitar da wata magana da ta shafeshi Hill TV za ta rasa matsugunni a Jahar Congo. Ba wannan ne matsalar ba. Jin ya ambaci sunan Asiya ya sa shi fahimtar dalilin dayasa Asiya ta yiwa Gwamna tambayoyin da tayi, duk da bai san takamaimai mi Asiyar ta jiyo ba amma yanada yaƙinin abune da ya shafi mutuwar tsohon Gwamna. Duk wanda ya ke bibiyar siyasar jahar ya san cewa Lamara Damana shine shugaban munafukan gidan Gwamnati masu hana ruwa gudu. Mr Damana ya fara aiki daga Sakatare ne a hankali ya dinga shiga cikin manya ya zamana anyita ƙara masa matsayi har ta kai lokacin Gwamna Saminu Bacchi aka bashi muƙamin Chief of Staff. Tunda aka koma mulkin farar hula babu Gwamnan da Mr Damana bai yi aiki da shi ba.

"Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta naɗi abinda yafi ƙarfinta, idan ya fito waje bana tunanin za ta sake yin rahoto da bakinta" kashedin COS na ƙarshe kenan.

Yana son Asiya tun farkon zuwanta ma'aikatar lokacin da tazo yin bautar ƙasa. Ya nemi soyayyarta ta ƙi shi, wanda yanzu ya riga ya haƙura tunda yaji ance an kawo kuɗin aurenta.

Duk da COS bai buɗa ba ya fahimci mi yake nufi sarai dan ba yau ya fara aikin jarida ba. Ba zai taɓa mantawa da wani ogan sa edita Mr Simon da suka fara aiki tare lokacin yana Lagos ba, shima kamar Asiya taurin kai ne da shi, indai a wajen bayyana gaskiya ne to baya jin tsoro. Ranan da gidan jaridarsu ta wallafa shafi akan wani asiri da Mr Simon ɗin ya jiyo na wani fitaccen ɗan siyasa ranan bai kwana duniya ba domin yana hanyar dawowa daga office motarsa tayi bindiga ta kama da wuta.

Ba zai manta da wani abokinsa Ja'afar ba. Ja'afar Bello investigative reporter ne daya binciko yadda wata Matar Minister ke safarar 'yan mata karuwanci zuwa ƙasashen waje. Yanada isassun evidence a kanta har an fara shari'a haka kawai aka nemi Ja'afar Bello aka rasa, ko sama ko ƙasa. Yanzu shekaru shatara kenan babu labarinsa.

Yana tsoron kada taurin kan Asiya ya jawo mata fitina.

Asiya koda ta koma office tunanin maganganun COS da ta MD ta dinga yi, a wani ɓangare kuma tana tunanin bazata taɓa bari Gwamna Saifuddeen yaci bulus ba. Ta sani cewa abinda ta naɗa bai kai evidence da za a iya kama Gwamna ba amma idan har maganan ta fito zai jawo cecekuce har a fara bincike, koda ya sha yanzu lokacin zaɓe abokan adawa za su yi kamfen da maganar su hana mutane zaɓanshi, ko kuma idan har akabi komai da gaskiya to dole ne ayi impeaching ɗinsa. Babu abinda take ganin yanzu zai faranta mata rai a rayuwa sama da taga an tsige Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah ...

***

A office Asiya ta dinga jayayya da zuciyarta akan ko ta bi shawaran MD tayi shiru da abinda ta ji ko kuma dai ta fitar da shi ta tada fitinar da zai jawa Gwamna matsala. Shawara ta yanke akan idan Ubayd ya zo hira za ta nemi shawaransa ta ji mi zai ce. Daga baya ta kasa haƙuri har zuwa lokacin ta kira numbarsa tace ya hau whatsapp akwai abinda za ta gaya masa. Sai bayan minti shabiyu ya hau saboda yana duba wani patient ne a lokacin da sukayi waya.

A tsanake ta masa bayanin komai da kuma abinda MD ya faÉ—a mata. Bai tsaida ita ba har sai da ta gama bayani ta ce miye shawaransa gareta.

" Asiya Shahidah na roƙe ki da girman Allah ki haƙura da abinda kike shirin yi domin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. For God sake! we are getting married soon. Kina so rikicin siyasa ya jawo miki wata fitinar ne? Idan har abinda kika ji gaskiya ne then you are not safe Aseeya ba ke kaɗai ba hatta 'yan uwanki ba su tsira ba. Asiya ina za ki iya rikici da Lamara Damana?, Please ki mayar ma sa da recorder ɗinnan ki nuna masa ba za ki taɓa fitar da maganan da kika ji ba"
Chapter 14 · 0% Book details