Sashe 30
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tayi maganar kaman mai shirin yin kuka. Malaysian gown ne data gani a Amazon watanni kaÉ—an da suka wuce. Simple gown ce ruwan madara da aka yiwa design da duwatsu ruwan gwal. Model É—in data saka kayan ta yi rolling da gyalen kayan ta saka crown a kanta kamar sarauniya. Asiya alokacin data ga kayan hango kanta ta yi sanye da irin kayan tana zaune kusa da Ubayd a ranan da za ayi kamunsu.
Su Queen Bee sun yaba da gown É—in, sai dai kamar yai kaÉ—an ace Matar Gwamna guda ta sanya gown irin wannan da kuÉ—insa ba zai wuce dubu hamsin ba. KuÉ—in shipping dana kayan duka-duka dubu arba'in da huÉ—u Asiya ta siya a kuÉ—in Nigeria.
Lokacin da Queen Bee ke mata rolling gyale wasu mata suka shigo wai suyi sauri motoci sun fara isowa, Gwamna ya kusa ƙarisowa.
Asiya tace ba make up, amma duk da haka sai da Queen Bee ta shafa mata powder, ta sa mata mascara ya ƙara fito da dogon gashin idonta, sai kwalli da man leɓe, shikenan.
Ɗankunne da sarƙan diamond da aka haɗo a cikin kayan duk ba wanda Asiya ta saka. Hannunta dai zoben Azurfa ne da Ubayd ya siya mata sai kuma awarwaro na Azurfa shima da Maama ta bata da jimawa.
Takalmi flat ta saka ruwan gwal sai Queen Bee ta bata wani purse ruwan gwal shima. Ba su yi amfani da ko É—aya daga cikin kayan da Bilkisu Kachallah ta aiko musu ba.
Hajiya Umma ce da kanta ta shigo yanzu dan duba shirin na su tunda Gwamna yace mata zasu iso nan da minti uku zuwa biyar.
Asiya tayi kyau sai dai ga wanda ya gaji arziƙi zai ga kamar shigar bata dace da irin wannan taro ba.
"Hajiya kayan da aka kawo bai d..."
"Kar ki damu, Bilkisu ai da gayya ta aiko miki kaya. Kinyi kyau sosai, ni dai roƙona kar ki bata dama akan ki domin yau ranan ki ne"
Asiya tayi murmushi. Ba wai dan taji daÉ—in abinda Hajiya Umman ta faÉ—a ba sai dan kawai dama abinda tayi niyyar yi kenan. Yau zata fara haÉ—uwa da Bilkisu Kachallah kuma sai ta nuna mata cewa ita É—in ba hajar Kamfen ba ce. Tana cike da ita da abinda ta fitar na cin zarafi data mata, iyayenta da kuma Ubayd. Da sannu zata bata kashinta a hannu.
***
Gwamna ne da matarsa Bilkisu zaune a bayan lemosine wanda motar Alhaji Sani Kachallah ce aka fito da ita takanas saboda tafiyarsu wajen dinner.
Gwamna bai shirya yin hidima ba bayan reception da aka yi jiya suna dawowa daga wajen ɗaurin aure. Akwai abubuwa dayawa a ƙasa da suka fi hidiman bikinsa mahimmanci. Bilkisu ta riga ta shirya komai ba tareda ta tuntuɓeshi ba, abokinsa kuma ɗanuwansa Abdullahi ya takura masa akan sai yaje dinner ɗin sannan a ƙarshe kuma Alhaji Sani ya kirashi ya faɗa masa manyan mutanen da zasu halarci dinner ɗin.
Ya sani sarai Bilkisu neman suna take da abinda ta shirya, fatansa kawai ayi taro a watse lafiya.
A dai dai sashen Alhaji Sani Kachallah motarsu ta tsaya.
"Here's the plan, zaka zo tareda ita, ni kuma zan tareku a bakin ƙofa daga nan sai mu wuce wajen zamanmu. And, ka gayawa 'yar kurma ta yi murmushi saboda hotunan da za a ɗauka"
Bai amsa mata ba sai kawai ya shiga kiran numban Hajiya Umma.
Ana buÉ—ewa Bilkisu Kachallah mota ta fita tana murmushi ta wuce inda jerin wasu motoci ke jiranta, Saudah Kachallah na bakin wata mota tana zuba mata murmushi na jinjina.
Hajiya Umma da Queen Bee ne suka fito da Asiya daga cikin gida, dake daga ɓangaren da suke zuwa inda motar Gwamna ke jiransu akwai tazara ko ina suka wuce sai guɗa da kirari ake mata ana taka musu baya. Sanda aka kai wajen motan Gwamna mutanen da suka rako Asiya sunyi Ishirin. Wani security ya buɗewa Asiya mota Hajiya Umma ta yi kane-kane a wajen saboda masu ribibin son ganin Gwamna. Sai da ta tabbatar Asiya ta zauna da kyau kafin ta rufe ƙofar tun ma kafin security ɗin yayi.
Kallo ɗaya ta masa ta kauda kai gefe. Yana sanye da farin babbar riga. Fari na ƙarawa baƙinsa haske, yana ƙara fito da kyaunsa. A kallo ɗaya data masa wanda hankalinsa ma na kan waya sai taga ya mata kwarjini, duk wani haushinsa da take ji sai taji wani nitsuwa ya sauka mata.
Ba ta san dalilin da ya sa ta ɗago dan sake dubansa ba, sai dai rashin sa'a lokaci ɗaya suka kalli juna. Ƙirjinta ya shiga lugude musamman da zuciyarta ya ankarar da ita cewa ita ɗin matarsa ce.
"Ina fata babu ruwan zafi a purse ɗinki?" Yai maganar yana nuna purse ɗin data riƙe.
Bakinta ya kafe na wasu sakanni, ta kasa bashi amsa har sai da ya sake cewa "Abubuwa sun faru a ƙurarren lokaci Asya. Amma a hankali zaki fahimci banyi komai dan na cutar da ke ba"
Maganar da ya faÉ—a ya tunzurata. Tace
"Mai girma Gwamna, a sannu zaka fahimci cewa bana barin sai ta kwana"
Daga haka ba wanda ya ƙara furta komai.
Suna isa hotel ɗin da aka shirya taron kafin a buɗe ƙofa Gwamna ya kalli Asiya yace "banda rawa" kafin Asiya ta bashi amsa aka buɗe masa ƙofa.
Tana jira a buɗe sashinta ta fita sai taga Gwamna ya ɗan rankwafa ya miƙa mata hannunsa.
Ta so ta buge hannun amma ta sani idon mutane akansu yake, duk abinda za tayi dole tayi takatsantsan. Ba mamaki akwai 'yan jaridar ƙwaƙwaf da ke ankare da samun hoto mai jan hankali.
Bata sani ba ko tunaninta ne, ko kuma dai gaske ne amma taji wani shock ya ratsa ilahirin jikinta sanda tafin hannunta ya shiga cikin nashi. Ko kaÉ—an hannunsa babu taushi da aka sani da hannun maza. To ina zai yi taushi kullum cikin AC.
Lokacin da ta fito maimakon ya sake hannun sai ya ƙara damƙe shi da kyau, a haka suka shige cikin hotel ɗin, Securities sun saka su a tsakiya suna basu kariya.
*to yanzu dai zamu dakonci shigowar Mai girma Gwamna Alhaji Professor Saifuddeen Kachallah da Amaryar sa Hajiya Asiya Kachallah. Dan haka kowa ya tashi tsaye a nuna musu soyayya*
MC kenan da wannan magana.
Daga inda suke tsaye suna jira a buɗe ƙofa Asiya ta ja tsaki jin sunan da MC ya kirata, kwana ɗaya da ɗaura aure amma har an fara laƙa mata Asiya Kachallah.
Daga bakin hall ɗin 'yan mata da maza ne masu ji da kansu suna tsaye daura da juna kowa ɗauke da ƙaramin kwando na alfarma da aka cika da flowers.
Security biyu da suke gabansu Asiya suka juyo garesu suka sara musu sannan suka koma gefe dan basu waje.
Bismillah Asiya ta furta a bayyane hakan ya sa Gwamna ya juyo ya kalleta kan kace me an musu hoto yayi goma.
Hannunsu sarƙe cikin na juna Suka fara takawa a hankali. Waƙa na tashi yayinda 'yan mata da samarin nan ke barbaɗa musu flowers a duk inda zasu taka.
Daga inda Bilkisu Kachallah ke zaune wani abu mai tsini ta ji ya soki zuciyarta. Abu biyu ne ya zo mata lokacin da ta kalli Asiya da Saifuddeen suna takowa fiskarsu É—auke da murmushi.
Na farko dacewa na ban mamaki da suka yi wanda tamkar an halicci Asiya dan Saifuddeen ne dama. Shi baƙi dogo, ita fara doguwa. Ita ga ushirya daya ƙara hasko da kyaunta, shi kuma dimple ɗinsa daya bawa fiskarsa kyau da kwarjini na ban mamaki. Asiya bata saka kayan data aika mata ba, hakan na nufin babu abin yaɗawa gobe kenan, asalima kayan da ta saka da kuma kwalliyar da ba ta yi ba zai ja a yabeta a kafafen yaɗa labarai.
Na biyu kalaman malamin taurari Tsu Zhang ne ya sake dawo mata. *akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki, haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki*
Murmushin yaƙe tayi a ranta ta furta "in dai ni Bilkisu Kachallah ina raye sai na juya ƙaddararki, tauraronki ba zai taɓa haskawaba. Saifuddeen nawa ne ni kaɗai, idan na gama dake har Saifuddeen ya shige cikin ƙasa babu macen da zata sake karambanin shiga rayuwarsa"
Kamar wacce aka tsikara sai ta miƙe da sauri tana faɗaɗa murshinta kamar bakinta zai taɓa kunnenta. Tana isa gabansu Asiya ta buɗe hannu ta rungumesu duka biyu nan da nan mutane aka sa tafi, hasken camera ta ko'ina sai wawal-wawal kake gani a hall ɗin.
Lokacin da ta sake su ta kama hannun Gwamna, ɗaya hannun kuma ta sa yatsa tana ƙoƙarin taro ƙwalla.
"Ikon Allah" Asiya ta faÉ—a a zuciyarta.
Dukkansu uku sai da suka zauna a mazaunin da aka tanada musu sannan mutane suka zazzauna banda ɗaiɗaikun manyan mutane irinsu Alhaji Sani, Umaru Kwom da Yallaɓai da basu tashi ba tun farko.
Kujerar Gwamna ce a tsakiya, gefensa na dama ta Bilkisu, gefensa na hagu kuma Asiya. Bilkisu Kachallah ta kalmashe ƙafa sai wani bushashatul wajahi take yi kamar itace Amaryar.
MC ya shiga yabon Bilkisu na yadda ta ajiye kishi gefe ta rungumi Amaryar mijinta. MC da azarɓaɓi harda cewa Bilkisu Kachallah tana koyi ne da matan Manzon Allah wanda suke kishi da ilimi. Asiya da jin haka ta ja tsaki.
Babu wanda zai ce Amarya bata fito ba. Babu kwalliya na hauka, babu takalmi mai tsini, babu sarƙa na Gwal ko Diamond, babu babu babu. Amma duk da haka Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta burge kowa, shigarta mai sanyi ne daya fito da sahiihin kyaunta, babu ƙyalƙyalin shirme.
Queen Bee ce ta bada tarihin Asiya yayinda Alhaji Abdullahi babban abokin Gwamna ya bada tarihin Gwamna.
Lokacin da aka zo yanka cake su duka ukun suka haɗa hannu suka yanka. Gwamna ya fara bawa Bilkisu cake ɗin a baki, zai kuma yankawa ta karɓi wuƙan ta yanka ta kai cake ɗin saitin bakin Asiya tana murmushi...