Sashe 2
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba yau Ubayd ya fara ganin report ɗinta ba. Infact akwai ranan da ya ke wajen ma ta ke ba da rahoto a gaban camera ɗin kuma bata taɓa jin irin haka ba. Idan ba Ubayd ba waye? Certainly not Umma da Abba saboda su kam tun ma kafin ta fara aikin sun kasance confidante ɗinta. Ta iya tuna ranan da aka ƙara mata matsayi ta zama field reporter sai da ta kira suka boosting confidence ɗinta kafin ta fara aikin.
Idan ba Ubayd ba idan ba Abba da Umma ba, to WAYE? Ta faÉ—a tana kallon motar su da su C Y ke faman saka kayan aikin su ciki...
***
GOVERNMENT OFFICE, CONGO STATE,
dif...dif...dif... ƙarar da yatsar sa ke bayarwa kenan lokacin da ya ke buga table ɗin gabansa da yatsarsa manuniya. Tunda aka fara rahoton ya ke kallo bai ɗauke idon sa ba sai da mai ba da rahoton ta faɗi sunan ta sannan aka ɗauke wajen zuwa announcer da ya ke chan studio yana ƙara commenting akan abinda ya faru a ƙauyen.
Ya bibiyi labarin ne saboda shine abu na farko mai mahimmanci da ya aiwatar a wannan shekara wanda har an kusa cin rabi cikin ta.
Mutane dayawa kallon hoto su ke ma sa. It has being a challenge lokacin da aka kira shi da gaggawa aka sanar da shi faɗan daya taso a ƙauyen Kayal ɗin. Gwamna baya ƙasar dan haka shine ya ke da damar ba da umurni a aiwatar da duk abinda ya dace gameda matsalar.
Tuni ya rattaba hannu a takarda wajen tura jami'an tsaro ƙauyen domin daidaiton lamurra a wajen. Ya ji daɗi da reporter ɗin ta yabawa Gwamna duk da dai shi da yai aikin ba Gwamna ba ne, da alama ko dai ta manta cewa Gwamna baya gari ko kuma dai ta furta Gwamna ne a matsayinsa na wakilin Gwamna ɗin.
Gidan Talabijin na HILL TV ba ta Gwamnati ba ce shiyasa ya damu da ganin rahoton daga tashar maimakon CONGO NEWS wacce ta ke gidan Talabijin na gwamnati ba lallai a yaɓawa Gwamnati baƙin fenti ba idan har ba su yi abinda ya dace ba sai ma ayi ƙoƙarin kare su.
Bai ida wannan tunanin ba wayar sa ta hau ringing. Mr Governor ya gani ɓaro-ɓaro a screen ɗin. Da sallama ya amsa wayar cikin muryarsa mai sanyi.
Daga ɓangaren Gwamna kuwa ko amsa sallamar bai yi ba ya ce ma sa maganan Albashi da zai sa hannu akai ya bari sai ya dawo tukunna.
Deputy Governor ya ce "Mr Governor nan da kwana shida fa kenan "
"To mutuwa za su yi kafin kwana shidan?"
Bai ce mishi komai ba har ya gama magana ya kashe kiran.
Yayi tunanin ya kira ne domin yai ma sa magana akan faɗan da aka yi a ƙauyen Kayal may be ma ya yaba ma sa akan ƙoƙarin da yai wajen daƙile faɗan da wuri amma shi damuwar shi kada ya saka hannu a bawa mutane Albashinsu har sai ya dawo. Yau Albashin ya shigo daga gwamnatin tarayya, kwanan wata ya kama ashirin da bakwai idan aka ƙara kwana shida zai zama uku ga wani watan kenan, mutane za su ji jiki.
Minene amfaninsa idan har a matsayinsa na mataimakin Gwamna ba zai iya aiwatar da komai na cigaban al'umma ba idan Gwamna baya nan. Ya tabbata kenan shi hoto ne.
***
Lokacin da Asiya su ka koma office har anfara kiraye-kirayen sallar Maghriba. Tana shiga office ɗin su aka sanar da ita saƙon MD da ya ke nemanta. A gajiye ta wuce office ɗinsa, ta sani ƙorafi ne zai yi ba komai ba. Tunda a wajensa kullum ba ta iya aiki ba.
"Miye matsalar ki ne Asiya?. Today's report was full of crap, sati biyu Gwamna baya gari amma kina ta faɗin Mai girma Gwamna ya turo jami'ai, Mai girma Gwamna ya damu da talakawansa. Give credit to whom credit belongs. Kina ganin da Gwamna Saminu Bacci ne zai tura jami'an tsaro cikin ƙanƙanin lokaci haka? I'm dissappointed in you"
Ita kwata-kwata ta manta da cewa Gwamna baya ƙasar to ko yana nan ai Deputy Governor hoto ne. Ba abinda ta taɓa jin ance yayi sai shegen yin ado kaman mace. Indai SSK ne ko mace sai albarka wajen iya ado.
Chief Editor na su da ke zaune a office É—in ya kalli Asiya ya ce " miya faru na ga rahoton ki na yau ba wani armashi, ba ki da lafiya ne?"
"no Sir, Ummata ce ba lafiya" Asiya ta faɗa ranta a ɓace.
"Allah ya bata lafiya"
Ta amsa ma sa da Amin. Da hannu ya ma ta nuni da ta fita daga office ɗin. Bayan ta fita Chief Editor ya kalli MD ya ce " mutumina ka mata a hankali. The girl is good ba wanda ya fi ƙarfin kuskure"
"Idan har bama nunawa jama'a goodness na Mataimakin Gwamna kullum kallon hoto za a dinga ma sa. Wallahi da shine Gwamna da jahar nan ta fi haka cigaba cikin shekaru ukun nan. S S Kachallah mutum ne da ya san darajan É—an Adam, he's a man of vision and mission"
"Ni zan gaya maka halin Prof Kachallah tunda ya koyar dani lokacin ina Masters ..." daga nan su ka buge da hiran mataimakin Gwamnan.
Asiya na fita daga office ɗin MD ƙasa ta koma wajen office ɗin su ta ɗau jakarta ta fito. Wani mahaukacin yunwa ke cinta ga gajiya a haka tafito daga farfajiyar gidan Talabijin ɗin. Da Ubayd na gari da shi za ta kira ya zo ya ɗauketa amma yanzu sai dai ta nemi abin hawa. Tana tsaye C Y ya fito da tsohuwar baƙar roba-roba ɗin sa.
"Ke kalar mota ce da na miki lift zuwa gida" ga faÉ—a yana dariya.
"Ƙaniyarka C Y, kana nufin tafiya za ka yi ka barni kenan"
ÆŠan dawowa yai da baya ta hau mashin É—in sannan ya ja suka tafi. Suna tafiyan suna taÉ—i saboda Clement Yohanna (C Y) akwai surutu shima kamar Asiyar shiyasa ma tasu ta zo É—aya.
A ƙofar gidan su ya sauketa yana faɗin ta gaida ma sa da Umma.
Da sallama ta shiga gidan na su, Inna Yaha na faman jan ruwa a rijiya amma ba ta amsa sallamar ba. Ko ba ta leƙa kitchen ba ta san sai yanzu za'a ɗaura abincin dare ko kuma yanzu aka fara girkin.
Sannu da aiki ta mata duk da ta san ba amsawa za ta yi ba. Wucewa ta yi É—akin Ummanta wadda shine É—aki na biyu cikin É—akuna uku da su ke jere waje guda. A kan sallaya ta samu Umman ta idar da sallah tana jan carbi, ta san ba za ta amsa gaisuwarta ba har sai ta gama azkar É—inta shiyasa ma ta wuce wajen wardrobe ta buÉ—e ta fito da wata doguwar riga mai laushi, rigar guntun hannu gareta. Kayan jikinta ta cire ta saka doguwar rigan. Lokacin da ta zauna bakin gado tana naÉ—e wandon jeans É—in da ta cire ne Umma ta fara mata magana da yaren Kurame inda ta ke tambayarta ya aiki, obviously ta ga rahoton da Asiyan ta kawo É—azu a TV. Itama Asiyan ya jiki ta mata tareda tambayarta ko ta sha magani.
Ƙarfe bakwai da rabi da minti takwas bayan ta idar da sallan Isha Cornflakes ta haɗa da madara ta fara sha tanayi tana danna wayarta. Kiran Ubayd ne ya shigo wayarta amma har ta katse ba ta ɗauka ba saima tsaki da ta yi. Bayan ya jera kira biyu ba a ɗauka ba sai a na ukun ta ɗauka amma ba ta yi magana ba.
"My Aseeya" ya faÉ—a da murya mai sanyi.
Tasirin da sunan yai ma ta ne ya sa ta yin guntun murmushi.
"Tuba na ke ranki shi daÉ—e. Na san na yi laifi amma a bani dama na faÉ—i uzuri na"
Still shiru ba ta ce komai ba
"Mine kina ji na?"
"Mine"
Asiya ta ɗan jinginar da kanta jikin gadon Umma sannan ta ce "ni mi zan ce tunda Matan Lagos sun ɗauke mun kai. Yau tun da sassafe da muka yi waya ba ka sake waiwaya na ba sai yanzu. Na san ka kalli report ɗina na yau amma ko ka kira ka tambayi lafiyata, you dont even care ko na dawo lafiya ko ban dawo ba, kawai kai..." haka ta yi ta rantings har sai da ta gaji da kanta ta yi shiru, a lokacin ne kuma Ubayd ya samu damar lallaɓata dan ya san halin kayan sa indai tana kwarwa to ba a katseta har sai ta gama.
Bayan ta karɓi haƙurin sa ne suka bige da hiran masoya ba ta ma ji shigowar ƙaninta Aliyu ba sai kawai gani tayi ya ɗauke kofin cornflakes da ke gabanta ya fara sha. Tana ma sa magana da hannu amma inaa bai kulata ba sai ya ma koma gefe ya shanye cornflakes ɗin tas.
Bayan ya gama kuwa ya dangwarar mata da kofi a wajen yai gaba. Shigowan Umma É—akin ne ya sa ta yi sallama da Ubayd akan za ta kirashi anjima.
Da hannu Umma ta gaya ma ta cewa ta je ta samu Abbansu a falo yana nemanta.
Sanda za ta wuce falon Abban ta kula da Inna Yaha da ke ta kwaran-kwaran a kitchen tana rabon abinci, babu wuta kuma torchlight da ta ke amfani da shi ya dafe ba haske sosai. Ba ta taɓa gajiya da mamakin halin Inna Yaha.
Asiya ta yi sallama bakin ƙofar falon Abba. Abba ya ce ta shigo.
Abba dattijone da kallo ɗaya zaka ma sa ka san ya doki shekaru sittin da biyu zuwa da biyar. Fari ne sosai a lokacin ƙuruciya amma yanzu ya fara dafewa, fiskarshi da kanshi yana yalwacce da gashi wanda kusan ya riga ya zama fari gaba ɗaya sai tsilli-tsillin baƙi da ba za a rasa ba.