Sashe 33
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yadda ka san sassaƙa Bilkisu akayi haka ta daskare akan kujera ta kasa motsawa. Ba ta hango wannan ba, ba haka ta shirya ba. Da ƙyar ta iya tashi lokacin da aka kirata ta zo ta rufe taro da addu'a. Asiya ta yi murmushi lokacin da taji Bilkisu tace ayi salati wa Annabi amma ba ta buɗe baki anji salatin ba, sai ta rufe ido tana muimui da baki kaman Akuya na cin ciyawa...
***
A wani ƙaramin ɗaki kuma wata mace ce sanye da riga da zani da ɗankwali dukkansu daban-daban. Kallo ɗaya zaka mata ka kirata 'yar ƙauye, sai dai yanzu da take gaban wata na'ura tana magana da harshen faransanci dole ka kirata gogaggiyar 'yar boko, yadda take magana da harshen ka ce a birnin Paris aka haife ta.
Cikin bayaninta take bayyana cewa har yanzu bata samu ƙwaƙwƙwaran hujjar da take nema ba, amma kuma tanada yaƙinin za ta samu nan bada jimawa ba. Babu tantama matar da take bincike akanta tana kasuwancin miyagun ƙwayoyi, amma saboda matsayinta ba za a kamata ba sai da hujja mai ƙarfi. Hujjar take nema sama da shekara ɗaya da take aiki da ita.
"Ba matsalata Bilkisu Kachallah ba, matsalata Madam Bintu ce ka sani. Dan haka ba ruwana da matar da Gwamna ya aura, that's his business"
Mutumin da take magana da shi yace "akwai jami'ar DEA da zata zo daga America kan batun safarar miyagun ƙwayoyi, idan ta iso zan haɗaki da ita. Agent Dahlia tanada interest sosai akan case ɗin nan, kuma na san za ta taimaka sosai"
"Yes Sir" daga haka ta rufe na'urar ta ɓoye shi a ma'ajiyarsa...
"Hansa'u...Hansa'u...Hansa'u"
Masu aiki uku ne a gaban Bilkisu Kachallah amma ba su take nema ba. Hansa'u ta iso da gudu tana faÉ—in "Hajjaju nah ki gafarceni, sallah nake"
Bilkisu ta ce " Sallan Uwarki, matso nan" Hansa'u ta matsa kusa da ita kafin ta gama matsawa ma Bilkisu ta É—auketa da mari tana faÉ—in " dan Ubanki kashe min É—a zaki yi? "
"Hajiya wane Ubana" Hansa'u tayi maganar tana sosa kumatu
"Uban me ya hana ki sawa junior inhaler a aljihunsa?"
Ta sani lokacin data shirya Junior ta saka masa inhaler a aljihun wandonsa sai dai in cirewa yai, amma a yadda Bilkisu Kachallah ke tiriri ba zata saurari bayaninta ba sai dai kawai ta bada haƙuri.
"Tuba nake Hajjaju, mantawa nayi"
Bilkisu ta sake kai mata duka tana faÉ—in "idan haka ya sake faruwa sai na yanka ki a gidan nan"
Abu biyu ne ya haɗuwa Bilkisu, na farko ta ƙumso baƙin ciƙin Asiya, na biyu kuma ta shigo falo ta samu ɗanta na kokawa da numfashi babu kowa kusa da shi. Saboda mijinta da ɗanta na da lalurar Asthma ba a rasa inhaler a jakarta. Hakan ya sa ta ciro ta jakarta ta matsa masa a baki.
Hansa'un dai aka saka ta goyi Junior ta wuce da shi É—aki.
Da dare da Gwamna ya dawo gidan Gwamnati saboda kwanan Bilkisu ne. Bilkisu ta same shi ta fara sauke masa fushinta.
"Saifuddeen sati É—aya da zuwanta amma har ka fara nuna banbanci. Ta ya zaka siya mata sabon mota bayan akwai mota a gidan da za ta yi amfani da shi.
I thought you said you married her for political reason, miyasa kake wanka tare da ita? Have you slept with her?"
Gwamna ya fara rage kayan jikinsa ya manta da ita a É—akin. A gajiye yake baya son abinda zai É—aga masa hankali.
"Saifuddeen ka gaya min gaskiya, ka..."
"Wanda suka kawo miki gulmar za ki tambaya bani ba"
"Ita da bakinta ta faÉ—a min yau kun yi wanka tare"
Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya fasa yai murmushi ya wuce banɗaki. Kafin ya kulle ƙofa Bilkisu ta faɗo ciki tana faɗin da ita zai yi wanka.
Lokacin da Sakatare ya nuna masa video na abinda ya faru a wajen taron da Bilkisu ta shirya ya jinjinawa Asiya saboda tarko Bilkisu ta ɗana mata lokacin da ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi. Ya sani ta so Asiya ta harzuƙa ne ta faɗi baƙaƙen maganganu a wajen ko ma ta zagi Bilkisun da wani abu, sai kuma Asiya ta nuna mata cewa ita ɗin 'yar jarida ce.
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
16
Asiya da Sumayya na cin abincin dare Sha'awanatu Bacchi ta kirata. Jinjina ta mata kan abinda ya faru a wajen taro, ta bata shawaran kada ta taɓa bari Bilkisu Kachallah ta taka ta sannan idan tana son samun matsayi sama da Bilkisu dole ne ta koma gidan Gwamnati. Asiya ta mata godiya ta ajiye wayar tana murmushi.
"Anty Ale ya kira wayarki É—azu da kika shiga banÉ—aki"
"Kin É—auka?"
"A'a"
"Good"
"Anty, har yanzu fishi kike da shi?"
Asiya ta ajiye cokalin hannunta tace "taya ba zan yi fushi ba Sumy. Bayan kuɗin da Mutumin nan yake da shi, bayan kuɗin daya karɓa a wajen 'yanuwan Gwamna, kwanana huɗu da aure ya kirani yana cewa na nema masa kwangila a wajen Gwamna. Wani uban ƙwarai zai yiwa 'yarsa haka. Dan ba a chanja Uba ne da tuni na chanja shi"
Sumayya ta sa dariya.
Basu gama cin abincin ba Nana ta kira Asiya. Ko a ina ta samu numbarta oho.
"Antyna ina gayyatarki birthday na da za'ayi ranan Friday. Dan Allah ki zo"
"Wai ni yarinyar nan mi kika É—aukeni ne?"
"Please Sweet Anty"
Asiya ta yi shiru na 'yan sakanni kafin ta ce "zan zo"
Tana ajiye wayar tace "inaga Gwamna mahaukata ya ajiye a gidansa"
Sumayya ta kwashe da dariya ta ce "Anty ai harda ke"
"Zan saɓa miki Sumy. Ni sa'ar ki ce"
"Anty ke fa kika faÉ—a da bakinki"
"Da matarsa da 'yarsa duk basu da kai, ranan da ta zo nan kinga yadda take girgiza kai kaman notinan kanta sun kunce, ni cewa ma nayi kan roba gareta"
"Kai! Anty"
Asiya ta sa dariya.
***
"Babu birthday wannan karan. In fact har na bar kujeran nan babu birthday, babu anniversary, babu wani celebration da za ayi sai dai biki ko suna"
"Wasa kake Saifuddeen. Mun yiwa Junior nashi farkon shekara ita kuna Nana sai kace ba za a mata ba. Ina ruwana da abinda mutane za su faÉ—a. Mu fa ba matsiyata bane, babu abinda muka rasa kafin ka hau kujeran nan dan haka dole ne mu kashe kuÉ—i wajen taya first born É—inmu murnan cika shekara shabiyar a duniya"
" lokacin da Mahira tace ba ta son birthday ta gudu wajen Dadda, wani abu ya sameta da ranan ya zo ya wuce ba tareda anyi komai ba"
"Darling Mahira daban Nana daban"
"Dukkansu 'ya'yana ne Bilkisu. Kuma yadda ba ayi na Mahira wannan shekaran ba, ba za ayi na Nana ba"
Bilkisu ta matso kusa da shi, ta riƙe hannunsa tana murzawa a hankali, ta sassauta murya tace " na san baka son abinda zai jawo maka magana a gari, nima bana son haka. Ka yi haƙuri muyi mata small get together birthday party, acikin gidan nan, daga ƙawayenta sai 'yanuwa. I promise babu, 'yan jarida da za su zo. Na yarda Mahira ba ai mata birthday ba wannan shekaran, amma kasan itace tace bata so, Nana kuma tana so. Ba kuɗin Gwamnati zamu yi amfani da shi ba ka sani. Na maka alkawarin ni zan ɗau nauyin komai daga aljihuna"
"Still dai..."
Shhhh ta faÉ—a tana rufe masa baki da yatsunta biyu. Ta sani an gama kenan, Saifuddeen mijinta bai iya dogon jayayya ba...
Ranan Alhamis Gwamna Saifuddeen Kachallah ya wuce Birnin tarayya wani taro da za su yi na Gwamnonin Arewa.
Ranan Jummu'a kuwa Bilkisu Kachallah ta shiryawa 'yarta bikin birthday.
Babu taro sosai saboda taron strictly na wanda aka gayyata ne.
Ana tsakiyar taro Asiya ta zo, Nana na ganinta lokacin za ta yanka cake ta je da gudu ta rungumeta. Bilkisu Kachallah ta hangame baki tana mamakin 'yarta.
Asiya ta karɓi ɗan ƙaramin akwatin gift da ke hannun Sumayya ta miƙawa Nana ta ce "Happy birthday"
Nana ta sake rungumeta tana faÉ—in "thank you, thank you"
An ci, an sha, an bada kuma an karɓi kyaututtuka. Ana daf da za a rufe taro Asiya ta tafi.
Da Asiya ta dawo gida, dare ta bi tana tsara labari a laptop É—inta, da ta gama ta turawa Mr Bassey tareda hotunan data É—auka.
Washegari jaridar Climax ta fito da labarin birthday É—in 'yar Gwamna. Hoton Nana sanye da wata matsatstsiyar doguwar riga kanta babu É—ankwali shine a shafin farko na jaridar, an rubuta *Gwamna Saifuddeen Kachallah ya zubar da miliyoyi wajen yiwa 'yarsa birthday*
A ƙasan labarin kuwa irin ɓarnar kuɗi da akayi aka lissafo, tun daga decoration, abinci, cake, souvenirs dama kayan da Nana da Bilkisu Kachallah suka dinga chanjawa a wajen, duk an bayyana. Daga ƙarshe aka ƙiyasta jimillar kuɗin da aka kashe zasu kai miliyan arba'in.
Lokacin da Bilkisu Kachallah ta ga jaridar Climax cilli tayi da wig É—in kanta tana faÉ—in koma waye yai rubutun nan sai ta sa an É—aure shi. Ta kira wani numba tana faÉ—in a nemo mata wanene ke da jaridar Climax, sannan tana son sannanin É—an jaridar daya yai rubutun nan.
Duk wanda suka zo bikin sai da aka karɓi wayoyinsu saboda ba a son ɗaukan hoto. Mai hoto ɗaya ne ta yadda ya ɗau hotuna a wajen, cousin ɗin Nana ne ɗan Anty Rufaidah, babu yadda za ayi ya siyar da hotunan Nana wa 'yan jarida. Koma waye ya fitar da hotunan nan sai ta sa an hukunta shi.
Gwamna Saifuddeen na É—akin hotel da suka sauka Chief of Staff ya nuna masa jaridar Climax a wayarsa.
Gwamna ya haɗiyi yawu da ƙyar. Ba abinda aka rubuta ne ya dameshi ba sai ganin duk cikin hotunan Nana da aka ɗaura babu wanda tayi shiga na mutunci aciki. Ya cizi leɓensa na ƙasa yana inama Nana a wajen Dadda ta taso kamar yadda Mahira ta taso a wajenta, ƙila da duk wannan ba zai faru ba. Da farko Bilkisu ya ɗaurawa laifi daga baya kuma ya gane cewa shine silar komai, ya barwa Bilkisu ragaman tarbiyyan 'ya'yansa bayan ya san irin tarbiyar da itama ta taso a kai.