← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 38

Sashe 3

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta gaisheshi ne ya ke tambayarta gameda ƙauyen da su ka je yau ɗauko rahoto. Bayan sun yi alhinin abinda ya faru tare ya sanar da ita musabbabin kiranta da yai. Magana ce akan admission da ƙaninta ya samu a Congo University wanda ya dage akan ba zai zauna a hostel ba sai dai ya dinga jeka ka dawo, shawaran Asiya ya tambaya ko dai ya siya ma sa babur kaman yadda Habib ɗin ya buƙata ne?.

Abba ya jima da retire har yanzu kuɗin pension ɗin sa su ke lallaɓawa. Ba dan Allah yayi ita da Umma suna sana'a ba da abubuwan ba za su zo da sauƙi ba. Ubayd ma yana nasa ƙoƙari akan mahaifinsa sosai.

Bikinta da na Faty da za ayi Abba ke yiwa taru dan haka maganar siyan Babur bai taso ba. Za ta yiwa Habib magana, gigin samartaka ke É—ibanshi yana ji yanzu ya gama sakandare zai shiga Jami'a.

Bayan ta bar wajen Abba ɗakin su ta koma inda Umma ke faman tura tuwon da aka miƙo ma ta. Sau ɗaya ta kalli tuwon ta kauda kai. Ga abinci ba za ayi da wuri ba gashi ba zai taɓa yin daɗi yadda ya kamata ba.

Kafin ta kwanta sai da su ka sake yin waya da Ubayd sannan ta kira Queen Bee su ka yi maganar Salon É—in su...

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

02

***

A chan wani ƙaton gida da ke GRA wasu manyan mutane ne guda huɗu ke zaune a wani katafaren falo daya amsa sunan falo saboda girma da kuma irin kayan alatu da aka zuba a ciki.

Ɗaya daga cikin su wanda kusan shi za a kira da babban su ya kalli wani da ke sanye da farar shadda da farin hula ya ce "Kachallah kana ganin za mu samu abunda mu ke buƙata a wajen sa?"

Kachallah ya ce "inada yaƙinin haka Yallaɓai. Shi mutum ne mai biyayya"

Wani mai baƙin suit ya tari bakin Kachallah da cewa "inada shakka akan wannan"

"Mr Paul mi kake so ka ce, ba dai kana nufin za a rusa tsarin wannan gwamnatin ba..."

"Mr Paul, Alhaji Kachallah wannan ba abun ɗaga hankali ba ne. Har yanzu akwai sauran lokaci dan haka zamu cigaba da saka mishi ido kafin lokacin ya cika. Ko mi ka ce Yallaɓai?"

Yallaɓai ya kalli Mutumin da yai magana sannan ya maida dubansa ga Alhaji Kachallah da Mr Paul. A hankali ya fara shafa gemun sa yana yi yana murmushi. Murmushin Yallaɓai na da ma'anoni daban-daban amma a wannan lokaci dukkan su sun yarda cewa yana nufin su kwantar da hankalin su ne, wato akwai nasara a dukkan tsare-tsaren su.

***

LADIES HALAAL SALON & SPA waje ne da ya amsa sunan sa, domin kuwa dukkan abubuwan da ake gudanarwa a wajen suna ƙoƙarin tafiya da tsarin da bai kaucewa tsarin musulunci ba. Waje ne da Asiya-Shahida, Queen Bee da Alhaja Oyiza su ka buɗe saboda samawa mata wajen kula da jikin su. Ma'aikatan wajen dukkan su mata ne. Cikin ayyukan da su ke gudanarwa a wajen akwai wanke gashi, drying da kuma stretching, suna gyaran farce (menicure and pedicure). Ana kitso da kuma ƙunshi sannan watanni biyar da su ka wuce da su ka dawo sabon shagon su da ke anguwar GRA suka fara gyaran jiki da spa treatment a wajen (wanda ya haɗa da body, hair and foot massage, facial treatment da sauran su)

Shigowar Shahidah sashen da ake yin gyaran gashi da kitso ya sa wajen yai wani irin tsit. Precious da ke yiwa wata mata kitson wig ta tsaya da kitson tana kallon Shahida jikinta na ɓari.

Matar ta É—an É—ago ta ce "ya ki ka tsaya?"

Tunda ba sa saida gashin wig kenan matar ce ta zo da abinta. Shahida ta faÉ—a a ranta.

Precious ba ta san ma Shahida na cikin shagon na su ba da ba za ta yi gigin fara yiwa matar nan kitson wig ba. Ta san dokar shagon su amma wannan matar Comissioner ce, duk da ta hannun Queen Bee ta zo ta tabbata za ta raɓi maiƙo a jikin matar, shiyasa da matar ta nuna kitson wig za a mata ba ta iya yi mata musu ba.

Shahida ta ƙaraso gaban matar sannan ta kalli Precious ta ce " ina bawa mutane dama ɗaya tak a rayuwa, na ƙarshe kenan da za ki sake taka mana dokan wannan shago. Ki maida mata kuɗinta ta bar mana waje"

"Malama ban gane mi ki ke cewa ba. Da alama ba ki san ko ni wacece ba ce"

"Duk wanda ya shigo wannan waje domin a masa wani abu a nan to sunan sa customer. A dalilin an ɓata miki lokaci za a maida miki kuɗin ki dan haka ki wuce wajen da su ke yin irin wannan kitso a ƙarasa miki a chan"

"What nonsense" matar ta faɗa a fusace tana miƙewa tsaye.

"Idan kin fita ki É—an É—aga idon ki sama za ki ga sunan wannan waje. Saka gashin wig baya cikin services na mu"

Daga haka Asiya-Shahida ta bar wajen. Tana jin matar tana ta zage-zage amma ko ajikinta. Ta yiwa matar farin sani. Habiba sunanta a ƙasan layinsu ta taso. ta tsula bariki sosai kafin ta auri kwamishinan ilimi shekaru uku da suka wuce.

Dole ta yi magana da Queen Bee ta jawa Precious kunne tunda ita ta bata aiki. Idan irin haka ya cigaba da faruwa Salon É—in su zai zama babu wani banbanci tsakaninsa da sauran gama gari...

**

Shahidah na zaune tana zanawa Amarya Layla lalle a hannu ta ji matan da ke wajen sun saka ihu.

Basma ta ce "Jennifer ƙara mana volume mu ji mi ya ke cewa"

Kafin ta gama maganar ma ta riga ta ƙara volume ɗin.

Muryan daya doki kunnen Asiya ne ya sa ta jan dogon tsaki ba shiri.

"Yanzu dan Allah saboda wannan wawan ku ke ta ihu"

Banza su ka yi da ita suka cigaba da yaba mutumin da ke magana a cikin TV.

"Ki ga idon sa dan Allah, ko idon kaɗai Allah ya bashi wallahi an zuba ma sa baiwa" wata daga cikin ƙawayen Amarya da ake wa Lalle ta faɗa.

"Allah ya shiryeku gaskiya. Mutum tsohai-tsohai da shi ku dinga wani drooling akan sa kaman wasu ƙwailaye"

"Ke dai 'yar baƙin ciki ce Asiya. Allah ya isan ma SSK ɗin mu za ki kirashi tsoho"

Kafin ta yi magana kuwa Asabe ta ce "ni kin san Allah yanzu haka idan da za ace na zaɓi tsakanin SSK da kuma Ubayd ɗinki Asiya Wallahi Tallahi SSK zan zaɓa"

Asiya ta fusata ta kaiwa Asabe duka Asabe ta kauce tana yi ma ta dariya. Ranan har Asiya ta gama yiwa Amarya Lalle ba ta dena diri ba. Hayaƙi ne kawai bai fito daga bakin Asiya ba saboda yadda ta dinga faɗa akan an haɗa masoyinta Ubayd da SSK...

**

"Gashi nan ai ya ƙi biyan albashi ya bar mutane da yunwa. Idan ka yi magana kuma a fara ganin baƙin ka mtsww"

"Mine kina da abun dariya Allah. Tunda mu ka zauna a nan ba hiran da mu ka yi sai ta SSK. Ki rage ƙiyayyar ki gareshi please. Abun ya fara yawa"

"Amma Ya Ubayd..."

"Yanzu dai a ajiye maganar sa a gefe tukunna. Albishirin ki"

Asiya ta haÉ—e rai ta juyar da fiska gefe.

"My Aseeya haka zan tafi gida ba tareda kin min murmushinkin nan mai sanyaya min zuciya ba"

"Ka je SSK ya maka murmushin tunda ka damu da shi"

"Mi zan yi da murmushin ƙato bayan inada kyakykyawar budurwa a kusa da ni"

"Dama ina so na miki maganar gida ne amma tunda kinyi fushi shikenan"

"Dan Allah an gama gyara kitchen É—in?" Ta faÉ—a cike da excitement.

"Wagga Bafulatana ba ta da kunya samsam"

"Eh É—in" ta faÉ—a tana murguÉ—a ma sa baki.

"Kinga É—an bakin nan da Allah zai kaimu wata biyar da kwana shauku da na jima da maganin sa"

Asiya ta yi saurin sunkuyar da kai tana rufe bakinta da tafin hannu tana murmushi cike da jin kunyarsa.

"Na rufe bakin ko?, gara ma ki sani a matse na ke wallahi. Abba dai ya cuceni daya saka bikin nan da nisa haka. Tunda Mustafan Faty bai gama shiryawa ba da anyi namu bikin idan ya so sai ayi na su daga baya"

"Ya Ubaydu wai ka je inji Abba" muryan ƙaninsa Musa ya doki kunnen sa.

"Musa kana so in zaneka ko? Za ka faÉ—o kanmu ba sallama sai kace wani dabba"

Musa ya fece daga wajen da sauri tun kafin Ubayd ya damƙeshi dan ya san halin yayan na sa sarai.

"Barin je wajen Abba"

"Idan ka je ka kai ma sa ƙorafin ka ƙila ya chanja ra'ayi"

"Ahaf ashe ba ni É—aya na matsu ba kenan"

Ba ta amsa ma sa ba ta wuce É—aki da sauri.

Murmushi yai mai daÉ—i yana addu'ar Allah ya kai shi lokacin da Asiya Shahidah za ta zama mata a gareshi.

Asiya na shiga ɗaki ta faɗa kan gado. Murmushi ta ke yi tana jin tsananin shauƙin son Ubayd. Ba za ta ce a matse ta ke ba amma harga Allah ba ta so aka saka bikin su wata shida ba, ta ɗauka wata uku ko huɗu Abba zai sa. Koda yake duk dalilin Mustafah wanda zai auri Faty aka kai bikin da nisa saboda ya ce bai gama shiri ba. Suma ɗin cikin wata shida kam sun gama shirya komai.

Ƙaran shigowar notification ta ji a wayarta da ke gefen gado, da sauri ta jawo wayar dan ta san ba zai wuce saƙon favourite poet ɗin ta ba ne wato KaSaSa. Ai kuwa tana buɗewa taga saƙon email ɗin daga KaSaSa ce. Tunda ta subscribing a website ɗin ta koyaushe ta ɗaura sabon poem za ta gani a email ɗinta.
Chapter 3 · 0% Book details