← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 38

Sashe 27

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Alhaji Sani ya fito daga mota har ƙasa Ale ya durƙusa yana kwasan gaisuwa fiskarsa washe kaman an masa albishir da Aljannah. Jiki na rawa ya masa jagora da tawagarsa ta mutum uku zuwa falonsa. Sai da suka zazzauna ya sake risinawa ya gaida su. Alhaji Sani da wani tsoho da yake tunanin zai kai shekaru casa'in sun girmeshi sosai amma sauran biyun ɗaga cikinsu zai kai sa'an Bellonsa sai ɗayan kuma dai zaiyi sa'an ƙaninsa Zakari.

Ƙokarin fita ya nemo musu ruwa yai amma Alhaji Sani ya dakatar da shi yace idan akwai wanda zai kira ya kira domin sun zo neman auren 'yarsa ce.

Ale Faruƙ ya ɗau waya ya fara kiran Baffa Malam yace ya zo maza-maza akwai manyan baƙi na jiransa. Bai san wacce cikin 'ya'yansa ake so ba amma cikin 'ya'yan dake gabansa mata da suka kai aure ba suyi aure ba, su biyar ne. Asiya data haura ishirin, Nafisatu da Ɗayyiba da suke shatakwas sai Sumayya data ke shabakwai sannan Baraka dake shashida. Koma waccece a cikinsu Alhaji Sani na nunawa to ya bashi ita ne kawai, babu mahalukin daya isa ya hana. Gwani ne ya isa ya dakatar da shi akan lamurran 'ya'yansa kuma Allah ya jiƙan rai ya jima acikin ƙasa.

Malam Audu maƙocin Ale ne ya fara isowa kafin Baffa Malam da Baffa Zakari wanda dama jiran baƙin suke dan tun jiya da dare Abba ya kira Baffa Malam ya sanar dashi abinda Gwamna yace da kuma matakin da shi ya ɗauka na janye neman da ɗansa ke yiwa Asiya. Baffa Malam da Baffa Zakari sun tattauna tsakaninsu kuma sun zuba ido ne tun jiyan suga yadda komai zai wakana tunda magana irin wannan Ale ne zai yanke hukunci ba su ba.

Minti bakwai da zuwan Malam Audu suma suka iso, dake kujerun sunyi kaɗan A ƙasa suka zauna tunda uban gayyarma a ƙasa suka sameshi. Duk da Alhaji Mustafah Kachallah Baffa a wajen Alhaji Sani ya nemi su Baffa Malam su zauna a kujera, Baffa Malam da Malam Audu ne kawai suka zauna a kujera.

"Na bayar" Ale Faruƙ ya faɗa tun kan Alhaji Mustafah ya ƙarisa bayaninsa.

"Idan hakane zamu ajiye sadakin yarinyar da kuÉ—in mun gani muna so idan yaso a hankali sai a kawo sauran abubuwan. Sannan kuma idan babu matsala muna so nan da sati biyu ko uku a É—aura auren"

"Wallahi ko yanzun nan kuka ce a É—aura mun shirya"

Baffa Malam ya bi Ale da ido. Kuɗi ai ba hauka bane. Tunda ya shigo falon ya lura da yadda Yayan nasa ke yi kaman wani wawa a gaban waɗannan mutane. Ya yarda suna da kuɗi sunada matsayi, suna da daraja a idon al'umma. Amma ba wannan bane zai sa kuma su basu wuƙa da nama a lamarin auren 'yar su. Sunada 'yanci ai. Ya dai yi shiru ne kawai saboda sanin halin Yayansa da yai, abune mai sauƙi a wajensa idan yai magana ya fara masa gori cewa ai shine Uban Asiya.

Miliyan É—aya cash aka ajiye musu. Sadaki dubu É—ari biyar sauran dubu É—ari biyar kuma kuÉ—in na gani ina so kamar yadda suka faÉ—a.

Su Baffa Malam ne suka raka baƙin waje yayinda Ale ya shige ƙuryar ɗakinsa yana neman wajen yiwa kuɗin mafaka.

Sanda ya fito zai bisu ya ci karo da kayan da aka jibge a ƙofar falon, tarkacen kayan gaisuwane su buhun gishiri, buhun suga, kwalin sabulai, kwalin minti da cingam, damin goro kusan kashi goma da kuma ƙwaryan Zuma guda uku.

Ya haɗiyi yawu ya yi waje da sauri lokacin har motocin baƙin sun riga sun juya...

***

"Ba zaku maidani mahaukaciya ba Baffa. Ta ina za'a karɓi kuɗin aurena bayan akwai maganar aurena da Ya Ubayd. Baffa kaima ka koma son abin duniya ne kaman Baba?"

"Zauna Asiya"

"Noo Baffa. Ka gayamin gaskiya, kuÉ—i da mulki sun fara tsole muku ido kuma?"

"Ki zauna aka ce miki ko" Baffa Zakari ya daka mata tsawa.

"Wannan abin yafi ƙarfinmu. Amma duk abinda kika gani ya faru da bawa to rubutacce ne daga Allah. Ki yi haƙuri ki rungumi ƙaddara. Insha Allah zamu cigaba da yi miki addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi a rayuwarki"

"Shikenan dan kunga Gwani baya raye sai ku yanke hukunci bisa son zuciya. Baffa wannan son zuciya ne, da ku da Baba duk dukiya ce ta tsole muku ido. Ba zan auri kowa ba sai Ya Ubayd"

Daga haka ta bar musu É—akin da gudu.

Ranan ƙarfe bakwai na yamma a gidan Abba ya mata. Tayi ta kiran nambobin Ubayd amma duka a kashe su ke. Hankalinta ba zai iya ɗaukan wannan abin ba. Ta yarda da ƙaddarar data faɗa mata na abubuwan da suka faru da ita cikin kwanakin nan. Yanzu ma maganarta ya ja baya a duniyar yanar gizo an koma gulmar wani ɗan film da aka ce yana luwaɗi.

Umma ma kamar kowacce Uwa ta damu da halin da 'yarta ta shiga musamman data ganta a fige kamar kazar sadaka.

Ta yi iya baƙin ƙoƙarinta wajen nuna mata cewa hukuncin da aka yanke mata ana mata zaton alkhairi ne ba sharri ba.

" Addu'a shine abinda ya rage miki yanzu Asiya ba kuka ba"

Maganar Mama kenan lokacin da ta riƙe mata ƙafa tana kuka akan ta tayata roƙon Baba da Baffaninta.

Itama Umman sunan addu'a take kira mata. Addu'a, Addu'a, Addu'a. Ta fa gaji da jin wannan suna.

Lokacin da tace zata fita, Umma cewa tayi sai dai dole su tafi da Gwani ko Aliyu. Dake Aliyun ne ke kusa shine ya rakata gidan su Umma Hussaina.

Rabonta da gidan ma zai iya kaiwa shekara.

Ta tsammanci samun Ubayd a gidan amma aka ce mata yayi tafiya.

Ta jima tana zaune a ɗakin Umma Hussainan kafin daga baya ta haƙura ta miƙe ta tafi ko sallama bata yiwa Umma Hussaina ba.

Damuwa kan chanja tunanin mutum matuƙa. Wasu lokutan Asiya sai ta shirya zata gudu sai ta fasa, wani lokaci kuma tayi tunanin ta kashe kanta ma kawai ta huta. A wasu lokutan kuma tayi tunanin samun bindiga ta je ofishin Gwamna ta bindige shege kowa ma ya huta. Wani lokacin kuma tayi tunanin ta haukace kawai saboda a dakatar da komai. Wasu lokutan ma zuciyarta na riya mata cewa ƙila ba Ale Faruƙ bane ubanta. Abin da ya fi riƙe mata rai ma bai fi yadda Ubayd ya ɓace mata ba, ga numbarsa da har yanzu bata shiga.

Ta fara tunanin ƙila Gwamna ne ya sa aka ɗauke shi, an ƙi faɗa mata ne kawai.

Sati ɗaya tayi a gidan bata san inda kanta yake ba. Abba da Umma kullum suna nuna mata ta saki ranta komai zai zo ya wuce amma zuciyarta bai shirya ma yarda da zancensu ba balle har ya amince da shi. Ubaydullah shine masoyinta na farko kuma na ƙarshe, ita tunda ta taso ma bata taɓa son wani ba, ko crush na primary ko secondary school bata taɓa ba. Ubayd ta fara so tun lokacin da ya ɗauka mata tsumman abunta, tun lokacin bata san so ba.

Saboda Ubayd bata taɓa bawa wani damar shiga rayuwarta ba. Ko lokacin da take Jami'a da tayi tashe, samari ke mata chaa babu wanda ta taɓa buɗewa ƙofa. It has always being Ubayd and will always be.

Yayinda Asiya ke fama da damuwa, a chan gida kuwa Ale FaruÆ™ ya kasa ya tsare wajen ganin wannan biki ya tafi yadda ya kamata. Sati ukun nan gani yake kaman ba za su iso ba. Tun yanzu ya fara kiran kansa sirikin Gwamna har tambayar siriki yai da turanci aka ce masa Inlaw amma idan shi ya faÉ—a sai kaji kamar 'yanlo yace.

Yi masa kirari da sirikin Gwamna kaga ya É—au kyautan dubu ya baka mutumin da É—arinsa idan ba a mace ba baya iya bayarwa.

Tuni yasa aka yiwa gidansa sabon fenti. Matansa da sauran yaransa duk ya musu ɗinkin biki kala biyar biyar hatta yayyen Asiya da ke gidajen mazajensu ya aika musu da nasu kayan. Wannan kashe kuɗi ko a sallah albarka. Shi dai yanada abu ɗaya gidansa ana cima mai kyau amma wani siyan kayan sawa ko na ado to ko a sallah sai anyi da gaske, yawanci ma iyayen 'ya'yan ke musu. Haka batun makarantar boko idan ka wuce sakandare sai fa ka tallafawa kanka. Mace ɗaya ce tayi karatu a 'ya'yansa mata bayan Asiya, itama kuma a gidan mijinta tayi. Adda Hadiza kenan da ta karanci ɓangaren midwifery.

***

"It was for political reasons Bilkisu"

"Shine sai dai naji a bakin Babana"

"Sanda kika dawo bana gari kuma wannan magana bata waya bace"

"Saifuddeen ka rasa wacce zaka aura sai 'yar Kurma jikar maiƙusumbi" ta tintsire da dariya. "I'm sure ba wai zaka nemi haihuwa da ita bane ko? dan ba zan juri ganin 'ya'yan guragu, kutare da makafi a gidan nan ba"

Gwamna yai seƙeƙe yana kallonta. Ita ce dai da take zuwa gidan marayu tana ɗaukan hotuna da naƙasassun yara.

"Na ɗauka baka ƙyamar nakasassu Bilkisu"

"Oh please Saifuddeen. Ka sani sarai campaign nake yi"

Ido ya zuba mata ya rasa ma mi zai ce. She never seizes to amaze him.

"And Darling, ka sani zan haƙura ne kawai saboda lokacin campaign ya kusa, bana son abinda zai ɓata maka ƙuri'u. Abu na ƙarshe kuma shine ka nema mata wani gidan dan a nan" ta juya yatsarta manuniya "ni kaɗaice Matar Gwamna"...

2g Novels

Home / THE GOVERNOR'S WIFE / THE GOVERNOR'S WIFE 13
THE GOVERNOR'S WIFE 13
2g novels THE GOVERNOR'S WIFE

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

*Assalamu Alaikum*

*Barkanmu da warhaka. Babu kalmar da zan iya baku haƙuri da shi daya wuce na haɗa ku da Allah. Dan Allah kuyi haƙuri.*

*Ban so na kai waÉ—annan ranaku babu update babu bayani ba. Amma akwai dalilin daya sa na yi haka.*

*Kwanan baya nayi rubutu ina son na yi copy and paste sai nayi deleting nashi. I was blocked, for days na kasa sake typing. Daga baya nace ni da update sai na kammala typing part 1. Na dena hawa online ne saboda bana son distraction.*
Chapter 27 · 0% Book details