Sashe 4
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta karanta poem ɗin ya fi sau biyar kafin ta miƙe ta je ta ɗauko littafinta da ta ke rubuta duk poetry na KaSaSa a ciki, ta rubuta sabon poem ɗin da aka turo. Idan Ubayd ya zo sallama dole ne ta karanta mishi poem ɗin dan ya taɓa zuciyarta sosai. A zuciyarta ta ce Allah ya zubawa KaSaSa baiwar kalamai.
***
Motoci guda biyar ne su ka shigo wani katafaren gida, irin gidajen nan ne da ƙusosin gwamnati da manyan 'yan kasuwa kaɗai ke iya mallakan su a wannan ƙasa, shi ɗan talaka sai dai ya gani kawai ya buɗe baki ya cika zuciyar sa da buri sannan ya kaɗa kai yai gaba, amma gidan yafi ƙarfinsa.
Motocin sun tsaya ne a farfajiyan gidan. Motar da ke tsakiya wacce ta fi kowanne kyau wani bodyguard ya buɗe ya fito daga gaban motar da sauri sannan ya buɗe ƙofar baya.
Ƙafafuwansa da ke sanye da designer sneakers ruwan toka ƙirar Dior ne suka fara sauka ƙasa kafin sauran jikin ya biyo baya. Dogo ne da tsayinsa zai kai kamu ɗaya da ɗigo takwas a ma'unin meter (1.8m) kusan a ido za ka ƙiyasta tsayinsa da ta shahararren ɗan film ɗin ƙasar India (Bollywood) wato Amitabh Bachchan.
Baƙi ne sosai irin baƙin da ya fi kama da na larabawan ƙasar Sudan. Sai dai na shi baƙin ya haɗu da hutu da jin daɗi sai ya zama har wani sheƙi ya ke yi yana ɗaukar ido. Idanunsa sun fi ko ina ɗaukar hankali a jikin sa. Fari fat da ɗigon baƙi wanda yai kamar an ɗiga baƙin tawada a cikin ruwan madara. Zara-zaran gashin ido da kuma gira da ke cike da baƙin gashi su suka haɗu suka ƙara ƙawata manyan idanunsa. Baƙin saje da ya haɗe da fiskarsa zuwa gemu da gashin baki suka bawa fiskar kyau da kamala.
A zahiri kallon yaro ake ma sa saboda kyaun jikinsa da ke ɓoye shekaru ,da kuma yadda akoda yaushe ya ke shiga irin ta Matasa. A ranakun Jummu'a da lokutan zuwa wajen taro na musamman kawai ya ke shiga irin ta Malam Bahaushe, amma fiye da rabin shigar sa shiga ce ta mutanen ƙasar waje. Ba abun mamaki ba ne ka ga SSK sanye da Tshirt da jeans a office tun ma kafin ya shiga siyasa har zuwa yanzu kuwa da su ke kan Gwamnati.
Kasancewar ya samu sa'ar karatu da wuri ya amshi Phd É—in sa yana shekaru ashirin da bakwai ne yayinda ya kai matsayin Professor a shekarun sa talatin da biyar, kusan shekarun da ake É—iba ma sa kenan idan an kalleshi wanda a zahiri an zaftare ma sa kusan shekaru goma kenan cikin shekarun sa.
Yanzu ma SSK na sanye ne da riga mai dogon hannu kalar sararin samaniya, irin yadda sama ke kasancewa a ƙarshen yammaci kafin dare kamar wajajen ƙarfe biyar da rabi zuwa shida ɗin nan, musamman a lokacin sanyi. Wandon jikin sa ta jeans ce kalar light blue, yana sanye da agogo da kuma zoben azurfa a yatsarsa ta tsakiya da ke hannunsa na dama.
Tuni bodyguard ya amshi jakar hannunsa bayan ya sara ma sa yana ƙame jiki tareda faɗin "Excellency"
Mataimakin Gwamna kenan *Professor Saifuddeen Sa'ad Kachallah* ingarman namiji mai cikar zati da haiba wanda a yanzu ya ke riƙe da jahar saboda Gwamna baya gari.
Kai tsaye cikin gidan sa ya wuce wanda ya gina da halaliyarsa tun ma kafin ya shiga siyasa dan ya ƙi komawa gidan gwamnati. Daga falon farko ba kowa sai dai yana iya jiyo hiran matarsa a ɗaya falon da wasu matan. Ya haura matattakala da zai kai shi sama inda ɗakunan gidan su ke. Ɗakin ƙaramin ɗan sa ya fara leƙawa. Yaron ɗan kimanin shekaru shida na zaune akan gado yana buga game a laptop ɗin sa. Sa'ad Saifuddeen Sa'ad Kachallah kenan wanda kowa ke kiransa da Junior. Ya kissing goshin yaron yana tambayarsa ko yayi homework ɗin sa yaron ya amsa da eh. Ya shafa kan yaron sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin. Bai leƙa sauran ɗakunan yaran na shi ba saboda kwana uku da su ka wuce su ka tafi hutu. Babbar 'yar sa Nana Khadija ta tafi gidan ƙanwar matarsa yayinda Aisha da su ke kira da Mahira ta tafi wajen Dadda wato kakar sa.
Wanka SSK yai sannan ya sanya farar jallabiya ya fito saboda kiran sallah da ya ke jiyowa daga masallacin kusa da gidan sa.
Hajiya Bilkisu na zaune a falonta tareda wasu mata guda uku. ÆŠaya matar Comissioner ce, É—aya kuma matar wani Senator ce, sai É—ayar kuma tsohuwar comissioner of Health ce wato Dr Madam Helen Audu.
"Yanzu dai ina so komai ya tafi dai-dai gobe, kar ya zama saboda first lady ba ta nan sai mu kasa gudanar da taron yadda ya kamata"
"Hajiya Bilkisu kar ki ji komai, ai abinda ki ke yi a wannan jaha ko firstlady albarka" inji matar senator
Bilkisu ta yi ƙasaitacciyar murmushi ta ce "indai akan cigabar jahar nan ne dole na yi ƙoƙari wajen ganin komai ya tafi dai-dai"
Madam Helen ta ce "Hajiya Bilki ni zan wuce"
"Nagode Mommy, sai mun haÉ—u goben" Hajiya Bilki ta faÉ—a da sigar girmamawa saboda Madam Helen ta girme ta sosai, idan ba ta yi sittin ba to za ta kusa kaiwa hakan.
Bayan tafiyar Madam Helen da kusan minti shabiyar sannan sauran matan su ka tafi sai a lokacin Hajiya Bilkisu ta samu damar sauke nannauyan ajiyar zuciya tana tararradin yadda gobe zai kasance. Wannan ne karo na farko da za ta gudanar da babban taro ita kaÉ—ai. Taro ne na matan Gwamnonin Arewa wanda tun kafin tafiyar Firstlady aka tsara shi, ita ne ta kawo shawaran kuma Firstlady ta amince da shi sai dai rashin Firstlady a gari ya sa aka yi tunanin É—aga taron har sai ta dawo amma Hajiya Bilkisu ta nuna ba sai an É—aga ba za ta wakilci Firstlady a wajen taron.
Bayan tafiyar matan nan ta lalubo wayar ta ta cigaba da bibiyar yadda za a sauki baƙin gobe ba tareda an samu matsala ba.
Lokacin da ta samu nitsuwa ta haura sama É—akinta ta wuce ta yi wanka ta saka kaya sannan ta fara sallah, ta haÉ—a sallar La'asar, Maghriba da Isha wanda zirga-zirga bai sa ta samu yinsu akan lokaci ba.
Ƙarfe goma da kwata ta shiga ɗakin mijinta wanda ke kishingide akan gado yana danna waya yana murmushi.
Zuciyar Bilkisu sai da ya kusa bulloƙowa waje saboda tsallen da yai, kamar walƙiya ta zo ta ɗauke wayar hannunsa tana huci tana duba abinda ya sa shi irin wannan murmushi haka. Shafinsa ne da ya ke rubuta poems ya ke dubawa, ba mamaki yana dariya ne saboda yadda mabiya shafin ke alaƙanta shi da mace.
Saƙon wani fan ɗin sa ta gani da ya ke cewa shi a duniya ba macen da ya ke so kamar KaSaSa.
"Darling har yanzu ba za ka ce mu su kai namiji ba ne ba mace ba" sai kuma ta yi saurin gyara maganarta da cewa "gara su cigaba da yi maka ganin macen, kafin yanzu mata su dinga damunka da waya"
Mayar ma sa da wayar ta yi tana murmushi " My Darling ka san ina kishin ka dayawa"
Bai ce ma ta komai ba ya cigaba da duba saƙonnin masoyan na sa.
"Ka ci abinci?" ta tambaya lokacin da ta kwanta gefen sa.
"Na leƙa ɗakin Junior ya riga yayi bacci, i guess tare ku ka ci dinner kenan"
Still bai amsa ma ta ba.
Ta sani idan SSK yana harkan rubuce-rubucen sa baya taɓa ba da hankali a wani abun daban, shiyasa ta haƙura da maganan ta manna ma sa kiss a kumatu tareda faɗin goodnight ta ja bargo ta kwanta. Gobe babban rana ce a gareta shiyasa dole daren yau ta samu isasshen bacci.
A wajen SSK ba komai ya hanashi kula matar ta sa ba sai ganin cewa ɓata lokaci ne a gareshi ya faɗa ma ta kuskurenta. Shi ba ma'abocin yawar magana ba ne hakan ya sa tun farkon auren su ya ke ɗagawa Bilkisu ƙafa, sai dai maimakon abubuwan su ragu sai ya zama ƙaruwa kawai su ke yi.
Irin rayuwar da yai buri idan yai aure ba ita ce rayuwar da ya ke yi yanzu ba.
A wassu lokutan yakan yi tunanin idan da Misturah ya aurah abubuwa ba za su zo ma sa haka ba. Kafin ya faÉ—a soyayyar Misturah ta kasance abokiya a gareshi wacce ya ke iya gayawa damuwar sa, wacce ya ke iya neman shawara a gurinta kuma ya samu shawara mai kyau.
Duk da sun taso gida ɗaya babu wannan kusancin tsakanin sa da Bilkisu. Har yau da su ka kusan cika shekaru shabakwai da aure ba zai ce ya gama sanin halin Bilkisu ba haka nan itama yanada yaƙinin ba ta san wanene Saifuddeen ba. Suna rayuwa ne tareda shamaki kamar labule a tsakanin su. Tun kafin ya zama Mataimakin Gwamna baya samun kulawar daya dace a wajen Bilkisu sannan daga shiga gwamnati abubuwa suka sake taɓarɓarewa.
A lokutan dayake cikin ƙunci ya ke buƙatar nitsuwa daga matar sa. A lokutan da kansa ya ɗau zafi daga harkokin gwamnati ya ke buƙatar samun mafaka a wajen matar sa. A lokutan ne za ka ga Bilkisu ta shagalta da harkokin siyasa ko kasuwanci.
Tunda ta sako maganar taron matan Gwamnoni da za ayi baya tunanin ta sake saka shi a lissafinta. Idan har ta tuntuɓeshi to tana neman shawara ne bisa jadawalin da ta tsara na abubuwan da za a gabatar ranan.
SSK ya juya ya kalli Bilkisu da ta ke gwarti alamun baccinta yayi nisa kenan.
Kafin ka yi aure duk irin waɗannan ƙananan abubuwa ba ka saninsu sai kun zauna tare na wani lokaci.
Akwai lokutan da idan zai kwanta sai ya saka auduga ko earbud a kunnensa saboda yadda Gwartin Bilkisu ke hana shi bacci, a hankali har jikinsa ya saba da hakan.
Aure sai da haƙuri, abunda ake gayawa sabbin ma'aurata kenan. Alokacin ba sa gane me ake nufi da haƙuri har sai sun kwana biyu da aure.