Sashe 17
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ko kin san Lamara Damana yayiwa Abba kashedi da kashe ni da ke da su Habibu? Ko kin san saboda hakane ya je ya samu MD É—inku akan ya sallameki?. Ofcourse ke ba ruwanki tunda kinada irinsu Umaru Kwom da zasu goya miki baya idan wani abu ya same ki.
"Asiya end this thing once and for all Dan Allah. In har da gaske kina sona ki ajiye maganar nan, idan ta kama ma ki rubuta cewa abinda kika faɗa ƙarya kikeyi indai hakan zai kawo maslaha to kiyi. I'm having bad feeling about this Asiya"
Bai jira amsarta ba ya fice daga falon ya barta tsaye tana hawaye.
Da Abba ya dawo daga sallar Isha ya kirata ya sanar mata Gwamna zai zo wajenta anjima. Bata nuna masa cewa Ubayd ya gaya mata ba saima haƙuri data shiga bashi kan abinda ta jawo masa...
***
Daga office bai wuce gidan Gwamnati ba asalin gidansa ya wuce ya chanja kaya daga office suit zuwa riga da wando da face cap duka baƙaƙe ya haɗa da baƙin glass saboda yaiwa fiskarsa kariya dan kar a ganeshi. Daga nan ya ɗauki tsohon drebansa yace ya kaishi layin 'yan dabino. Sakatare ya riga ya kira dreban ya masa bayanin gidansu Asiya dan haka bai tsaya ko'ina ba sai ƙofar gidan.
Lokacin da aka tsaya yayi kusan minti biyu kafin Gwamna ya kira numbar Abba ya sanar dashi gashi a ƙofar gida. Ko minti ɗaya bai cika ba Abba ya buɗe ƙofar falonsa dake fiskantar ƙofar gida ya fito jiki na rawa. An riga an kashe wutan ƙofar gidan shiyasa da akwai ɗan duhu. Yana ƙarasowa Gwamna ya buɗe ƙofa ya fito kafin kace me sun shige falon Abba.
Sai da Gwamna ya zauna kafin Abba ya zauna yana risinawa duk da zai bawa Gwamnan shekaru kusan goma shatakwas amma girma girma ne.
A tsanake suka gaisa kafin Abba yace masa bari ya kira Asiya.
Asiya na É—akin Umma ta takure waje guda Abba ya shigo da sallama.
"Yana jiranki"
"Abba" ta faÉ—a a hankali kamar mai ciwon baki
Abba ya samu gefen gado ya zauna ko kallon Asiya bai yi ba har ta fice daga É—akin sanye da dogon hijabin sallarta.
Ƙanshin turarensa ya game falon dan tana buɗe ƙofa ƙanshinsa ne ya mata marhaban. Kallon tsana ta bishi da shi har ta zo ta zauna daura da shi. Har lokacin data zauna bai ɗago ya kalleta ba, idonsa na kan wayarsa. Ganin bashida niyyar magana yasa Asiya tace " akwai abinda nake yi kafin na fito, zan koma"
Har ta fidda ran zai amsa tana shirin miƙewa ta bar masa falon taji yace "miyasa kike zargina? Mi kika sani?"'
Da ita mai ashariya ce da ta ɗura masa ƙazamar ashar a wajen.
"Ji wani tambayar rainin hankali a nan. Your excellency na san komai, na san abinda ka aikata amma kuma zan yi shiru ne kawai saboda Abbana. Sannan ka sani akwai Allah "
Lokacin daya ɗago ido bataga ƙwayar idonsaba saboda face cap ɗinsa ya tare.
Sai dai duk da haka sai da taji bugun ƙirjinta ya chanja.
" na yaba da jajircewarki sai dai zargi babu shaida matsalace Asya. Umaru Kwom zai yi amfani dake ne ya yar, you are too young for that
"Idan kinada shaida akan abinda kike iƙirari kuma, kina iya gabatar min yanzu"
Wani abune yazo ya tokare mata maƙoƙaro dai-dai lokacin da take ƙoƙarin kurma ihu. Ita Gwamna zai rainawa hankali bayan shi ya aiko akazo aka ɗauke recorder da laptop ɗinta.
Bata san ya akayi ta samu ƙwarin gwiwa ba, ƙila tsanarsa da tayi ne ya bata wannan ƙwarin gwiwa, ƙila kuma saboda marin da Ubayd yace anyiwa Abba ne.
Jug É—in ruwa da aka ajiye a tsakiyar centre table ta É—auka ta buÉ—e ta watsawa Gwamna a fiska.
"Wannan shine shaidar ka, Azzalumi"
Tana tsaye riƙe da jug ƙirjinta na bugawa da ƙarfi kamar zai ɓallo, ta kasa ko motsawa a wajen.
Ya kai sakan arba'in kafin Gwamna ya iya cire hular kansa ya buɗe manyan idanunsa. Loƙacin da ƙwayar idonsa ya shiga cikin na Asiya tsabar tsoro saida fitsari ya tsirto wa Asiya.
Yai shirin buɗe baki yai magana amma ya fasa kawai sai ya miƙe tsaye, bai gama miƙewa ba Asiya ta fece da gudu ta bar falon...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
08
"Jiya na yi bacci da wuri ban san yaushe ka shigo ba"
Gwamna bai kulata ba ya cigaba da kurɓan shayin dake hannunsa a hankali
"gobe zan wuce China, idan na gama siyayya a chan zan wuce Dubai"
"Na É—auka wata uku uku kike zuwa sari" ya faÉ—a yana kallonta
"Manager yace ana buƙatan sabbin kaya, ka san latest goodies nake shigowa da shi"
"Ok"
Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abinci a hankali.
Jiya bai shiga gidan da wuri ba sai kusan ƙarfe biyu saura na dare. Baccin awa biyu yai ya sake miƙewa dolene ya je office da wuri saboda wani exco meeting da zasu yi ƙarfe takwas na safe. Har yanzu bai bar mamakin abinda Asiya ta masa ba. Gaskiya yarinyar tanada ƙarfin hali.
Jiyan Asiya na fecewa yai murmushi dan abin dariya ya bashi. Yana fita cikin sauri ya je ya shige mota Dreba ya wuce da shi gidansa. A nan ya chanja kaya ya ɗan huta kafin ya shiga rubuta waƙa, kafin ya ankara ƙarfe ɗaya tayi dan haka ya tattara komai ya koma gidan Gwamnati. Sai daya leƙa ɗakunan yaran kafin ya je ya kwanta. Ya lura da cewa Nana da Zunairah sun rugume juna cikin bargo amma bai ɗauke shi komai ba. Mahirah kuma da alama karatu take bacci ya ɗauketa dan ga littafin nan gefen gado yana shirin faɗowa. Ya ɗauki littafin mai suna Americanah ya ajiye a gefen side drawer yai murmushi domin Mahirah ce ta ɗauko son karatunsa, bayan ya kashe wuta sannan ya wuce ɗakinsa inda Bilkisu ke kwance ta jima da barin nahiyar Africa...
Ta sani abinda tayi bai dace ba, shiyasa lokacin data fito banɗaki ta shige da gudu. Bata fito ba kuwa sai da Inna Yaha ta fara ƙwanƙwasa ƙofar. Lokacin data isa ɗakin Umma, Abba baya nan dan haka ta fara ƙoƙarin chanja kaya ƙirjinta na wani irin dokawa kamar wanda tayi tsere.
Washegari kasa zuwa gaida Abba tayi tana zaune a ɗaki ta kasa leƙa ko ƙofar ɗaki tunda tayi Alwalar Asuba.
ÆŠumamen da ke gabanta ma turashi gefe tayi dan ba iya ci zatayi ba.
Shigowar Abba ɗakin da sallama yasa ta miƙewa a firgice, tun jiya take jimamin shirun Abba.
Shiga ta musamman yai, yasa babbar riga kamar mai zuwa É—aurin aure.
"Ina kwana Abba" ta faÉ—i tana rusunawa
"Lafiya Asiya Shahidah"
"Abba kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi na watsa masa ruwan ba"
"Ba tarbiyyan gidan nan bane. Ba kuma tarbiyyan Gwani bane Allah ya jiƙan rai. Girmama na gaba koda ba Shugaba bane tarbiyyan musulunci kenan, tarbiyyan da nake da yaƙinin mun miki kenan Asiya. To amma..."
"Abba ka yafe min"
Shi kansa Abba tun jiya ya kasa yarda Asiya ce tayi haka sai yanzu da ta jaddada masa. Jiya ya ji gudun Asiya zuwa banɗaki bai kai minti ɗaya ba kuma ya ji ƙaran tashin mota hakan ya sashi zuwa falon nasa da sauri.
Jug ya fara gani a ƙasa, wajen da Gwamna ya zauna kuma akwai alaman ruwa a wajen. Ya duba ƙasan wajen nan ma akwai ruwa a malale. Wajen baiyi kamada kwaɓewar ruwa bisa tsautsayi ba yafi kama da cewa watsashi akayi.
Kasa gaskata cewa Asiya ce ta aikata hakan yayi. Ya so kiran Gwamna amma rasa abinda zai faɗa masa ya sa ya fasa kiran. Ya kwana da tunanin mi zai yi, daga baya ya yanke shawaran zuwa wajen Gwamna ya bashi haƙuri. Lokacin daya tura saƙo wa Gwamna da bai ga reply ba tsoro ya shige shi. Bayan kamar minti arba'in Gwamna ya masa reply akan ya zo ƙarfe goma da minti shabiyar.
"Zan je na bawa Gwamna haƙuri dan gidana ba gidan da ake walaƙanta baƙo bane balle baƙo kuma shugaba. Kamar yadda na faɗa kiyi duk abinda kika ga dama"
Yana juyawa yai kiciɓis da Umma. Allah Sarki ta jima a wajen amma dake bata ji bata san mi suke tattaunawa ba. Ta shiga tambayar Abba miya ke faruwa amma yace mata kar ta damu idan ya dawo zai mata bayani.
Bayan fitar sa Umma ta tsare Asiya da tambayoyi. Daga ƙarshe dai sai da Asiyar ta faɗa mata abinda tayi. Umma ta kama baki tana zaro ido...
Abba na fita waje Ubayd na ƙoƙarin tsaida motarsa. Bai gaya masa abinda Asiya tayiwa Gwamna ba ya dai ce ya zo ya raka shi wajen Gwamna.
Haka suka wuce gidan Gwamnati kowa da abinda ke ransa.
Daga waje Ubayd ya nuna ID card É—insa amma duk da haka sai da masu gadi suka kira suka tabbatar da ana tsammanin zuwan su kafin aka barsu suka shiga ciki.
Wani security ya musu jagora har ofishin Sakataren Gwamna bayan ya sanar da Gwamna zuwansu sannan yace su shiga ciki.
Kwarjini Gwamna ya ƙara yiwa Abba. Kunyarsa ta gama cika shi lokacin da Gwamna da kansa ya miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya jagorance su zuwa wajen kujeru inda yake zama ya tattauna da baƙinsa.
"Ranka shi daɗe, ba zan iya bayyana maka yadda raina ya ɓaci jiya ba. Ina roƙon ka dan Allah kayi haƙuri ka yafe mata. Asiya..."
"Ba komai Malam Nuhu, ya wuce a wajena. Infact na yaba da ƙarfin gwiwarta. Sai dai ina tausayin mijin da zata aura kar watarana yai laifi ya sha ruwan zafi" yai maganar yana dariya
Abba ya dara yayinda Ubayd ya sunkuyar da kai yana kallon fiskar wayarsa wanda hoton Asiya ne a wayar, bai É—ago ba sai da yaji Abba yace " ka ji abinda Gwamna yace ko Ubaydullahi, sai ka zage damtse"
Gwamna ya kalli Ubayd sannan ya kalli Abba hakan yasa Abba yai saurin cewa "É—ana kenan Ubaydullahi wanda zai aureta nan da watanni kaÉ—an masu zuwa"
"Allah ya musu jagora"