Sashe 24
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan tafiyar Saifuddeen ita da mai shagon suka yi gulmar shi inda Baƙar budurwar ke cewa Saifuddeen irin sabbin ɗaliban nan ne masu rawan kai da burga.
Kwanansa biyu da fara aiki inda ya ke É—aukan É—alibai 'yan aji uku da 'yan aji huÉ—u sai kuma masu yin masters.
Bai saba cin abinci a waje ba amma takanas Dr Hassan da office É—insu ke kusa yazo ya ja shi akan suje cin abinci.
Canteen É—in da suka je na wasu yarabawa ne, daga bakin wajen an rubuta *Iya Bola's Food*
Ba laifi wajen ya haÉ—u akwai tsafta amma duk da haka dan ta Saifuddeen ne ba zai ci abinci a wajen ba.
Bayan an serving ɗinsu abinci suna ci ya hango baƙar yarinyar ranan tana serving wasu abinci. Dr Hassan ne ya fara cinyewa inda ya ce da Saifuddeen zai wuce aji yanada ajin ƙarfe biyu. A lokacin bai san halin Dr Hassan bane ya jawoka cin abinci yatashi ya bar ka ka biya masa. Saifuddeen ya cigaba da cin abinci ahankali, lokacin daya gama ya zauna saboda wajen da ake biyan kuɗin a cike yake da ɗalibai, gaskiya wajen ana ciniki.
Yana zaune baƙar yarinyar tazo kwashe masa kwanuka.
"How much?" Ya faÉ—a a hankali
"400"
Arhan abincin da ya ji ya sashi ce mata na duka biyu yake nufi. Ta kalli ƙwayar idonsa sannan ta kauda kai tace " still 400"
Chanjin naira ɗari zata bashi amma yace ya yafe mata ya miƙe ya bar wajen ya bar Mistura da buɗe baki.
A ranan daya sake zuwa wajen shi É—aya ya zo Mistura na ganinsa ta zo wajen da sauri
"Mr keep the change what can i serve you?"
" jolof rice and fish"
"With Dodo abi with chips?"
"What's Dodo?" Ya faɗa bil haƙƙi saboda bai sani ba.
Baƙar yarinyar ta ƙyalƙyale da dariya harda kama baki.
"Oga Ajebo, dodo is fried plaintain"
" Ok with Doodoo" ya ja sunan kamar dodon tatsuniya.
Lokacin da ta kawo abincin ta tambayeshi ko a aji É—aya yake sannan a wani faculty.
Jin yace shi ba É—an aji É—aya bane ya sa ta tambayi ajinshi. Yai shiru yana kallonta saboda kamar kowa itama tunanin É—alibi take masa. Ko ranan daya fara shiga aji ma É—alibansa kallon raini suka masa sai da suka ji yace shi zai É—aukesu darasi sannan jikinsu yai sanyi.
Lokacin da ta kawo masa abinci ta tambayeshi sunansa. Ya amsa da cewa
"Saifuddeen"
"Misturah, 400 lvl Economics. Tunda ka ƙi faɗamin wani aji kake, i can bet cewa ba zaka wuce 100lvl zuwa 200lvl ba"
"Miyasa kika ce haka?"
"Kana yi kaman wani JJC"
Saifuddeen yai murmushi ga mamakinsa sai ya ji tace " kana da kyau and i love your smile"
"Misturah...Misturah..."
"Maaa" ta amsa tana barin wajensa da sauri.
Cikin sati biyu da yai yana zuwa wajen sai gashi ya san komai nata. Shi kansa ya rasa dalilin daya sa ya zama regular a wajen kuma in har bata wajen ba zai ci abinci ba sai ya tabbatar tana nan kuma ita tayi serving É—insa.
Iya Bola mai saida abincin Ƙanwar Mahaifin Misturah ce kuma a wajenta ta taso tun tana shekara takwas. Ita ce ta ɗauki ɗauyin karatunta har yanzu da take final year.
Bai sanar da ita ko shi waye ba saboda ya sani yadda ta sake jiki da shi idan har ta san lecturer ne ba zata kula shi ba. Da bakinta tace masa bata mu'amala da malamai.
A sati na biyar da fara koyarwarsa aka bashi ajinsu Misturah. Farfesan daya ke ɗaukansu ya tafi wani conference na sati uku a ƙasar America.
Dr Kachallah ɗalibai da Malamai ke kiransa kuma sunan ba baƙo bane a wajen Misturah dan taji labarin tsaurinsa a wajen ɗalibai 'yan Pol science.
Lokacin da course rep É—insu ya gaya musu cewa Dr Kachallah ne zai É—auki darasin Prof Badmus ta ji daÉ—i saboda ta tsani Prof Badmus, kowa ma a ajin ya tsaneshi domin yadda fiskarsa ke da muni haka zuciyarsa take. Yanada tsauri, baya sassautawa É—alibai ko kaÉ—an gashi ba wai ya iya koyarwa bane dan ba a gane darasinsa.
Abinda Misturah ta sani gameda Dr Kachallah shine shi ɗin sabon Lecturer ne kuma yaro, dan sun ji ƙishin-ƙishin ɗin ko shekaru talatin bai kai ba sai dai akwai kwanya.
Lokacin daya shigo tana ƙoƙarin karanta wani journal ne da ya ke da nasaba da project topic ɗinta. Nitsuwar da ajin yai ya sa ta ɗago idonta car acikin na Saifuddeen da ke tsaye a wajen podium na ajin.
Da muryarsa mai sanyi yai bayani akan shi zai cigaba da É—aukansu darasin Prof Badmus kafin ya dawo.
Sunan daya rubuta akan allo ta ƙurawa ido, da manyan baƙi ya rubuta *SAIFUDDEEN SA'AD KACHALLAH*
Sun gane darasin da yai musu sosai, sai dai matsalarsa É—aya wato yawan jefo tambaya idan yana bayani. Haka kawai sai ya nunaka ya tambayeka wani abu sannan baka isa kace baka sani ba dan shi a ajinsa babu kalmar i don't know. Ya fi so ko baka sani ba ka yi abinda bature ke cewa attempt, dole sai ka faÉ—i amsar a naka fahimtar.
Misturah kam kasa nitsuwa tayi dan gani take idonsa na kanta ko kuma idan yai tambaya ya nuna mutum yace YOU gaba ɗaya sai ta ji ƙirjinta ya buga dan gani take kamar ita zaice.
Basu taɓa fahimtar darasin Prof Badmus irin na yau ba. Daga su 'yan Economics har 'yan Political science da suke yin darasin tare kowa ya yarda akwai banbanci a koyarwar Dr Kachallah data Prof Badmus nesa ba kusa ba.
Daya gama darasi ya bada damar ayi tambaya yawanci matan ajin suka dinga É—aga hannu suna masa tambayar shirme dan dai kawai ya kulasu.
Kamar kullum bayan yayi sallar Azahar Iya Bola's food ya wuce ya samu waje ya zauna yana jiran Misturah sai dai ko mai kama da ita bai gani ba. Kwana uku ya jera yana zuwa wajen baya ganinta. A rana ta huÉ—u sai ya zo da wuri ya kuwa ci sa'a tana nan.
"Sir mi za a kawo maka?" Tayi tambayar kamar a yau É—in ne ta fara ganinsa.
"Misturah ya kamata muyi magana..."
"Munada Semo, sakwara, Amala, Eba, white rice, jollof rice..."
Miƙewa yai ya bar mata wajen, ta bi bayansa da kallo cike da mamaki.
Daga ranan bata sake ganinsa ba dama gudunsa ta fara yanzu kuma sai ta fara dakon zuwansa amma shiru. Idan yazo ajinsu kuwa ko gefen da take baya kallo hakan yai matuƙar damunta. Wasa wasa gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta.
Bayan sati É—aya da yin hakan ta kasa É—aukan shirunsa, ta kasa É—aukan sharewar da ya ke mata.
Ta nemi inda office É—insa yake ta je ta sameshi dai dai zai fita ya tafi gida.
"Sir kayi haƙuri ranan..."
"No no no, ba laifin ki bane. I should have told you the truth tun ranan da kika tambayeni a wani aji nake"
"Kenan baka fushi dani?"
Sai da ya É—au jakarsa sannan ya ce " na baki space ne saboda kince bakya son kowacce mu'amala da malaminki. A da ni ba malaminki bane amma yanzu..."
Sai bayan sati huɗu daf za a fara exams da Prof Badmus ya dawo ya karɓi ajinsa tukunna Misturah ta sake jiki da Dr S S Kachallah. A lokacin da su kayi hutu lokaci zuwa lokaci ya kan je gidansu. Tun Iya Bola na mata faɗa akan mu'amalarta da Saifuddeen har tazo ta haƙura tunda ta nuna mata cewa ba soyayya suke ba sannan kamalar Saifuddeen ya sa Iya Bola ta fara yarda da shi. Gaba ɗaya kasancewarsa ɗan babban gida bai sa mishi girman kai ba.
A wajen Misturah ne Saifuddeen ke iya sakewa ya faɗi son ransa yai abinda ya ga dama. A wajenta ya koyi cin abincin da yake da nasaba da ƙabilun kudancin ƙasar. A wajenta yake iya sakewa ya fayyace mata damuwar ransa, a wajenta ya samu ƙwarin gwiwar fitar da rubutunsa na waƙoƙi wanda ada sai dai ya rubuta ya zuba su a wardrobe. Dalilinta ya wallafa littafin rubutattun waƙoƙi da pen name Jabir Al Jabir yayi amfani da sunan na shekaru biyu kafin daga baya da suka rabu da Mistura ya koma amfani da suna KaSaSa.
Sai da Misturah ta gama aji huÉ—u tana jiran sakamako kafin Saifuddeen ya bayyana mata cewa yana sonta. FaÉ—uwa ne tazo dai dai da zama dan a wajen Misturah kam tun kafin ta san shi malami ne soyayyar Saifuddeen ya shiga zuciyarta.
Duk da ya san ba lallai bane a amince masa ya aureta kasancewa shi ba Bayarabe bane amma kuma ya ɗaura aniyar sai inda ƙarfinsa ya ƙare akan neman auren Misturah. Lokacin daya faɗawa Sikiru mijin Iya Bola cewa yana son ya turo magabatansa bai yi mamaki ba da yace masa sai ya nemi izinin 'yanuwansa a chan gida.
Letter Sikiru ya fara turawa chan garinsu ya musu bayanin waye Saifuddeen amma da aka dawo da amsa sai ya ga cewa wai basu amince Misturah ta auri bahaushe ba.
Mamaki ya kamashi dan da alama basu fahimci wani Kachallan yake nufi ba. Haka ya shirya ya wuce garin Akure. Lokacin daya fayyace musu asalin wanene Saifuddeen Kachallah mantawa sukayi da batun kudu da arewa suka ringa kiran ai Nigeria ɗaya ce kuma ya kamata a daina nuna banbance-banbancen ƙabila ko yanki. Cikin kashi ɗari na danginsu kashi tamanin da biyar sun amince da auren bayan sun ji kuɗi da mulkin gidan da Saifuddeen Kachallah ya fito.
Bayan Saifuddeen ya samu amsar daya ke so daga wajen Sikiru sai ya gabatar da buƙatarsa na son auren Misturah wajen Alhaji Sani. Ga mamakinsa sai yace masa ko zai auri wata mace to bayan ya auri Bilkisu ne, dama jira yake ta ƙarisa jarrabawarta na ƙarshe ta dawo ya haɗasu aure.
Ba zai taɓa iya yiwa Baba musu ba shiyasa ya amince da hakan. Sun taso da Bilkisu kuma tsakaninsu akwai jituwa sai dai bai taɓa sawa ransa zai iya auren mai irin halayen Bilkisu ba. Girman kai, Shagwaɓa, kasala, zafin rai da ma ra'ayin ƙin talaka sune halayenta da suka sha banban da tashi. A matsayin 'yar uwa yana sonta amma a matsayin matar aure gaskiya...