← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 38

Sashe 8

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka Gwamna Saminu Bacchi ya haÉ—iye sauran maganar sa saboda haÉ—e bakin su da Sha'awanatu ta yi.

Washegari da safe Gwamna ya tashi da wani irin ciwon kai da ciwon ƙirji, ciwon ne ma ya tashe shi daga bacci tun ƙusan ƙarfe huɗun Asuba.

Wasa-wasa har ƙarfe shida jikin ba sauƙi duk da kuwa ya sha magungunan sa.

"Za mu wuce Asibiti ne ko a kira maka likita?" First lady ta tambaya cike da fargaba.

"Ki kira Likita" ya faɗa da ƙyar saboda yadda ƙirjinsa ke takure.

Bai kai awa ɗaya ba saiga likitan sa ya iso koda ya duba shi cewa yai jinin sa ne ya hau sosai idan akwai wata damuwa da ke ransa to yai ƙoƙarin kauda ita dan abunda ya sa a ransa ka iya jawo ma sa bugawar zuciya.

Shi dai ya sani bai sa komai a ransa ba. Ba a fara campaign ba balle ya ce shine ke É—aga ma sa hankali. To kodai Barasar daya kwankwaÉ—a jiya da dare ne? Duk da likitan sa na chan Germany ya hana shi shan barasa. Duk da kuwa ya san ba zai iya dena sha ba, sai dai ya rage sha ba kamar da ba.

Allura da Likitan ya ma sa ya taimaka ma sa sosai dan har ya samu yayi bacci. Lokacin da ya farka kusan ƙarfe goma shaɗaya na safe.

Sha'awanatu ta taimaka ma sa yai wanka ta kawo ma sa abinci har kan gado amma bai iya ci ba sai shayi kawai ya sha.

Ƙishirwar giya ce ta dameshi dan duk da yana jin jiki yayi amanna idan ya ɗan kurɓi kaɗan zai samu sauƙi. Fita yai daga ɗakin Sha'awanatu ya wuce na sa ɗakin a nan ya fito da kwalbar giya ya kwankwaɗa ya girgiza kai ya sake kurɓan kaɗan sannan ya mayar da sauran ma'ajiyar sa.

Shiryawa yai ya fita saboda akwai meeting da zai yi da wasu contractors ƙarfe biyu na rana.

"Yanzu yadda baka da lafiya haka za ka fita?"

"To ya za ayi dole ne mu yiwa talakawa aiki"

"To. Amma ka dai yi tunani akan abinda na ce"

Dariya Gwamna ya fara yi sai kuma ya dafe ƙirjinsa saboda yadda ya ji ƙirjinsa na suya kaman an saka masa wuta.

"Your excellency jikin ne?"

Kafin ta ƙarisa maganar Excellency ya kai ƙasa.

"Your excellency, miya faru? Ƙirjin ka ne?"

"Waye a nan? a kira likita. Excellency... Saminu...Saminu ka tashi"

Lokacin da aka garzaya da Gwamna Asibiti ya riga ya cika likita ya ce zuciyar sa ce ta buga (cardiac arrest)...

***

Mataimakin Gwamna na zaune a office Chief security officer ya kira shi, kiran da ya É—aga ma sa hankali sosai dan kuwa a kiÉ—ime ya fice daga office É—insa ya wuce Asibiti.

Mummunan labarin da aka gaya ma sa a waya shi ya tarar a wajen domin kuwa Allah yayiwa Gwamna Saminu Bacchi rasuwa.

A chan Kachallah House kuwa Alhaji Sani Kachallah ne ke waya da mijin 'yar sa wato Saifuddeen wanda ya jaddada ma sa mutuwar Saminu Bacchi.

"Mi aka ce ya kashe shi?"

"Baba ba zan iya cewa komai ba yanzu"

Alhaji Sani Kachallah ya ce "ba komai zan kiraka anjima". Yana kashe wayar ya shiga kiran numbar Yallaɓai.

A chan gidan mataimakin Gwamna kuwa Bilkisu Kachallah ce zaune a falo tana cin gasashshiyar kifi da soyayyen dankalin turawa haÉ—e da lemo mai sanyi.

"Hansa'u, Hansa'u " Hansa'u ta fito da gudu.

Miƙo min remote ina son kallon news.

Hansa'u ta miƙa ma ta remote ɗin Bilkisu ta chanja channel daga Zee world zuwa Congo news...

***

Asiya Shahidah na zaune a sabon office É—inta tana aiki akan computer abokin aikinta ÆŠahiru ya shigo office É—in da sauri.

"Shahidah kin san labarin dana ji kuwa daga fitata a office É—in nan?"

"Miya faru?"

"Yanzu Abigail ta ke kawo rahoto cewa Gwamna ya rasu"

"Wani Gwamnan?"

"Gwamnan Congo mana"

"Innalillahi! Dan Allah?"

"Allah kuwa"

Asiya Shahidah ta miƙe ta bar office ɗin da sauri...

Kusan awa É—aya da rasuwan sannan Mataimakin Gwamna kuma acting Gwamna ya bada sanarwan mutuwar Gwamna Saminu Bacchi.

*"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun. Haƙiƙa dukkan mai rai mamaci ne. Muna yiwa Jahar Congo ta'aziya bisa rasuwan Mai girma Gwamna Alhaji Saminu Bacchi wanda Allah yai wa rasuwa yau shabakwai ga watan Nowamba. Haƙiƙa wannan jaha ta yi babban Rashi"* hawayen da ya zubo ma sa yai saurin sa hankerchief ya goge sannan ya cigaba da bayani

*" Insha Allahu za ayi jana'izar sa a gidan gwamnati da ƙarfe biyar na yamma"*

Asiya Shahidah da ke kallon news É—in a talabijin da ke office É—in su CY ta ce "Ikon Allah har da kukan munafurci kaman bai ji daÉ—in abinda ya faru ba, Shege. Ai yanzu kam jahar nan ta shiga uku a hannun wannan Wawan"

A ɓangaren Yallaɓai kuwa yana gama kallon bayanan da SSK yai ya danna remote ya kashe T V sannan ya kai duban sa ga Kachallah ya ce

"To kyan alƙawari dai cikawa. Ina fata Saifuddeen zai bamu haɗin kai"

"An gama Yallaɓai"

Yayinda wasu ke cikin baƙin ciki da rasuwan Saminu Bacchi wasu kuma na nan suna planning yadda za a juya Gwamnati.

Duniyar kenan. Tunma kafin a sa shi cikin ƙasa har an riga an cire shi daga lissafi.

Da 'yan siyasa za su dinga tunawa da cewa akwai ranar da dukiya ko matsayi ba zai amfanesu ba ƙila da za su tausayawa talakawan su.

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

04

"Rayuwa kenan. Yau kam Saminu Bacchi sai kwanciyar kabari"

Abba da ya kashe rediyon sa ya faÉ—a.

Ubayd ya ƙara da cewa "Ya tafi ba abunda ya ɗauka kuwa"

"Muna addu'ar Allah ya taya Saifuddeen riƙo Amin"

Ubayd ya ce Amin. Shiru ne ya biyo bayan haka na É—an mintuna kafin Abba ya É—aga kai ya ce " 'yata ta dawo kuwa?"

"Ƙila aiki ne ya tsaida ita"

"Ka je ka dubo min ita"

Bai musa ba ya miƙe yana karkaɗa key ɗin mota.

Lokacin da motar sa ta sako kai farfajiyar ma'aikatar su Asiya ya hangota tana shirin hawa babur ɗin CY. Yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya ke ƙin aikinta irin yadda ba ta damuwa da irin mutanen da ta ke mu'amala da su. Ya sha hanata mu'amala da wannan camera man ɗin amma kaman ma duk cikin Kamfanin su tafi jituwa da shi.

Sarai ta hango shi amma ta kauda kai kamar ba ta ganshi ba. Sai da CY ya tada machine su ka fara tafiya ya kula da motar Ubayd.

"Aseey ba motar fiancee É—in ki ba ne wannan"

"To sai me"

CY yai saurin taka birki har sai da Asiya ta bugu da bayanshi.

"Ya ka tsaya?"

"Bebz i no wan trouble, plz ki sauka"

"CY ka wuce mu tafi"

Lokacin da ya tada machine É—in a hankali ya ja su har wajen da Ubayd yai parking motar sa Asiya na ta ma sa faÉ—a akan ya wuce su tafi amma bai saurareta ba.

"CY za ka haÉ—u da ni gobe ai. I will deal with you"

Bai kulata ba sai É—agawa Ubayd hannu da yai yana faÉ—in "weldone Sir"

Ubayd ya sauke glass ƙasa ya ce "Sannu da ƙoƙari fa"

"Sannu Sir, a yiwa Amarya haƙuri yau ta gaji dayawa ne"

"Nagode"

Asiya ta watsawa CY harara kafin ta zaga ta je ta shiga motar Ubayd.

Sai da ya ga ta shige motar kafin ya ja machine É—in sa yai gaba.

Ubayd bai ce mata komai ba ya tada motar su ka fara tafiya. Itama ba ta kula shi ba sai ma kwantar da kujera da ta yi ta rufe idonta kamar mai bacci.

Traffic ne ya riƙesu saboda ma su dawowa daga maƙabarta.

Ƙaran siren ne ya tada Asiya daga baccin daya sace ta. Ta rintse ido ta buɗe da kyau ganin har yanzu suna round about na GRA kenan ko kusa da gida ba su yi ba.

Sai da motocin Gwamna su ka wuce kafin aka basu hanya suma suka fara wucewa hakan ya sa Asiya ta ja tsaki.

"Asiya" ya dakatar da ita lokacin da ta ke shirin fita daga mota.

Ta juyo ta kalleshi ba tareda ta ce komai ba.

"Zan kiraki bayan sallar Isha"

"Ok" ta faÉ—a sannan ta fita.

Data shiga gida tana jin shewar Abida ƙawar Hindatu mai murya kaman na maza. Ta dawo kenan ta faɗa a ranta sannan ta wuce ɗakin Umma.

Bayan ta yi sallar isha tana kwance akan sallaya tana danna waya kiran Ubayd ya shigo. Ta san dalilin kiran shiyasa ba ta ma ɗauka ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.

"Yau kuma shigar ta malamai ne"

Ubayd ya faɗa lokacin da ta ke ƙoƙarin zama akan kujerar roba da ke gefen sa.

"Idan ma gatse ne ka san dai daga gidan Malaman na fito"

"Shiyasa na ke alfahari da cewa jikar Gwani Baba zan aura. Allah ya jiƙan rai"

"Ka huce kenan?"

"My Aseeya kenan. Kin riga kin sani bana iya fushi da ke ai. Ki yi haƙuri"

Asiya ta É—an haÉ—e rai tana tura baki.

"Kwantar da hankalinki ba haka nan na zo biko ba, na zo da kayan sulhu"

Yana maganar ya jawo ledar da ke gefensa ya É—aura akan cinyarta.

"Whoa! Pringles, chocolates. Ba dan halin ka ba dai kaima ka yi haƙuri" tana maganar tana buɗe robar pringles ɗin.

"Ya Ubayd gaskiya yau ka yi abin kirki" tana maganar bakinta yana ƙurmus-ƙurmus.

"Ba za a sammini ba?"

"In your dreams. Ka san yanzu a zaune sai na cinye wannan bai isheni ba"

Ganin ya sakata farin ciki ya sa shi yi mata hiran shirye-shiryen bikin su da tsarin yadda komai zai kasance. Yau baya so ayi maganar kowa sai ta su. Ana taÉ—i ya tuno mata da ranan da ya fara ganinta a gidan su hakan ya sa Asiya mingirewa da dariya tanayi tana "kai Ya Ubayd"

Farkon haÉ—uwar su tana shekara shaÉ—aya a duniya ta zo yiwa ummanta hutu. Lokacin 'yar mitsila da ita amma wai tana JSS 2.
Chapter 8 · 0% Book details