← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To ki kirashi ki gaya masa zaki je goben"

Hannu data ɗaga zata jawo jakarta sai data rintse ido saboda yadda zuciyarta ke sukan ƙirjinta. Missed calls ta gani dayawa a wayar wanda na Ubayd ne yafi yawa. Tun isowarta ta turawa Umma text ta sa wayar a silent ta jefata cikin jaka.

Numbar Ale ta kira taji shi a kashe, hakan ya mata daidai dan ba son magana da shi take ba.

"Numbarsa a kashe take" ta faÉ—a da muryar da yafi kama da raÉ—a.

"Ki tashi kiyi wanka kizo ki ci abinci. Haka kawai ki hana kanki sakewa saboda a kanki aka fara yaÉ—a jita-jita"

"Tashi maza kin ji. Barin cewa Ladi ta É—eba miki ruwan zafi"

"Toh"

***

"Sumayye, Sumayye"

"Na'am Baba"

"Uban me kike a É—akin ne. Ki fito mu tafi ko na barki a nan"

"Gani zuwa Baba"

Minti ɗaya sai ga Sumayya ta fito daga ɗaki sanye da hijabi ruwan toka wanda saboda akwai duhu zaka ɗauka baƙi ne. Babu wuta shiyasa gidan ya ɗau duhu, wata da taurari kuma a daren kaman sunyi ƙaura.

Wayar latsawa ce a hannunsa amma yana dannata da ƙarfi kaman wanda idan bai yi hakan ba ba za tayi aiki ba.

"Baba gani"

Ya É—an yi murmushi saboda bazawararsa da suke chatting tace tana jiransa ya zo ya ga kwalliya.

"Baba gani fa"

"To fasa mun kunne Sumayye."

Sumayya ta fara tura baki wanda ba dan dare bane kuma hankalin Ale na kan bazawararsa da ya gani.

"Kin É—auko kazar?"

"Na É—auka"

Ficewa sukayi daga gidan dan yana sauri daga wajen Asiya zai wuce wajen masoyiyarsa Lubabatu.

Cikin motarsa ƙirar peugeot 406 fara wacce aƙalla ta bawa shekaru shatakwas baya ya ɗau Sumayya suka wuce gidan Gwani wanda yanzu ƙannensa da iyalensu ke zaune a ciki.

Masallaci ya fara tsayawa ya gaisa da Baffa Malam wanda ke koyarda É—alibai karatu sannan ya wuce cikin gida É—akin Mama.

"Gashinan Anty Asiya Ale yace a kawo miki Kaza. Ni na soyata da kaina"

"Ki ajiyeta Summy ba zan iya ci ba"

"Dan Allah ki tashi ki ci"

"Salamu Alaikum"

"Amin Alaikas Salam. Bismillah"

"Ina wuninku dai"

"Lafiya, Sannu da zuwa Ale FaruÆ™"

Mama ta miƙe daga kujera ta koma bakin gado gefen Sumayya.

Bayan sun gaisa da Mama sannan ya maida dubansa ga Asiya ya tambayeta ya hanya.

Daga inda Asiya ke kwance ta amsa masa da lafiya.

"Mama bata da lafiya ne? Ko za a kira Malam ya mata rubutu ko Asibiti zamu wuce?" yai maganar ba tareda ya tsaya ya ja numfashi ba.

"Taƙi cin abinci ne fa tunda ta iso"

"Wai haka Asiyata? Ke Sumayye baki bata kazarta bane?"

"Baba gashi nan ita tace ba zata ci yanzu ba"

"Ki daure dai ki ci kinji Asiya"

Kaman gaisuwar ce kawai ta kawoshi sai kuma bayan shirun minti biyu ya fitar da abinda ke ransa.

"Ke Sumayye ki bamu waje"

Bayan Sumayya ta fita daga ɗakin, Mama ta fara ƙoƙarin miƙewa Ale yace ta zauna.

"Asiyata ya jikin dai" bai jira amsarta ba ya cigaba.

"Wai asalin kuɗin da akace 'yan adawan sun baki nawa ne? Tun da safe Malam Yusha'u da Alhaji Ɗansabo suke musu akan kuɗin nan, ni dai nace duk kuɗin Umaru Kwom ai ba zai baki ƙasa da Miliyan biyar ba ko?"

Kaman wanda aka tsikara haka Asiya ta miƙe zaune tana yiwa mahaifinta kallon ƙurilla kamar yau ta fara ganinsa.

"Ba sai kowa ya san asalin kuÉ—in ba Asiya. Kinga bikin ki ya kusa idan kika bani miliyan biyu ko uku a ciki zan juya miki shi kafin lokacin biki"

Magana take son yi amma kukane ya ƙwace mata. Abin nata ya kai har mahaifinta ya tsaya musu da wasu akan kuɗin da ba ta san da su ba. Ba ma wannan ba, ashe har sunanta ya ɓaci a garin da take iƙirarin cewa nan ne asalinta.

"Lah! Daga tambaya sai kuka. To kiyi haƙuri"

"Ale FaruÆ™ inaga dai gara ka barta ta huta zuwa gobe sai kuyi maganar"

Bai musawa Mama ba ya miƙe ya musu sai da safe ya fice daga ɗakin. Sumayya dake zaune a balbalin Baaba Ladi matar Baffa Malam tana ganin Ale ya fito daga ɗakin Mama tayi saurin miƙewa ta wuce ɗakin da sauri.

Lokacin da ta shiga ɗakin kuka ta samu Asiya ke yi. Tayi saurin ƙarisawa wajenta ta shiga jijjigata tana bata haƙuri.

***

"Shi Malam Nuhu mijin uwarta ne, shi kuma Ale FaruÆ™ Uban daya haifeta kenan. Inaga dai chan garin nasu kawai zamu je saboda ayi komai daga tushe"

"Kana jina kuwa Saifu?"

"Baba, Bilkisu..." Gwamna ya faÉ—a cikeda damuwa

"Idan ta dawo ka turo min ita, za muyi magana"

Daga haka bai sake cewa komai ba. Shima Gwamnan ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da taraddadin abinda zai faru idan Bilkisu ta dawo taji maganar auren daya ke shirin yi...

A daren ranan Gwamna ya wuce gidan Abba. Tunda ya fara yiwa Abba bayani Abban bai ce uffan ba, kansa na ƙasa ya kasa ɗaga ido ya kalli Gwamna. Magana ne yayi a taƙaice amma nauyinta zai iya kaiwa nauyin treloli goma.

Ba wai bai yarda da maganar Gwamna bane daya ce zai auri Asiya ne saboda ya kare rayuwarta. Girmansa ya wuce ya zo har gida ya masa ƙarya. Gaskiyarsa ya faɗa sai dai gaskiyar nauyi gareta. Idan har zai yi tunanin cewa auren Asiya shi zai sama mata lafiya to kuwa tabbas abinda ke bibiyan Asiya abune mai girma.

Asiya 'yarsa ce kuma lafiyarta shine abu na farko da zai fara dubawa sama da komai. Ƙila ƙaddarar Asiya kenan, ƙila tsakaninta da Ubaydullahi sai dai alaƙar Ya da ƙanwa.

Ya kai minti biyu bai iya cewa komai ba. Ya sani, indai su Alhaji Sani Kachallah suka je gaban Ale FaruÆ™ gobe to an riga an gama dan maganar aurenta da Ubayd ta tashi kenan. Ya ji daÉ—i da Gwamna ya girmama shi bai manta cewa Ubaydullahi shine saurayin da zai auri Asiya ba.

"Ba a kai sadaki ba. Mun tambaya ne kuma an bamu kuma har an saka lokaci. Shi Ubayd akwai kuɗin sadakinta daya ajiye a wajena zuwa idan lokaci ya ƙarato sai na baiwa magabatanta, amma tunda Allah ya rubuta ba matarsa bace zan maida masa kuɗin gobe da safe idan Allah ya kaimu"

"Malam Nuhu..."

"Your Excellency nagode daka karramani, ka bani girma har kazo da kanka ka sanar dani komai. Ina addu'ar Allah yasa wannan haÉ—i ya zamo alkhairi a rayuwar Asiya"

Gwamna ya so yai wata maganar amma bashi da bakin yi. Duk abinda zai faÉ—a ba zai chanja abinda Abba zaiyi tunani akansa ba.

***

Kwanaki biyar kenan da zuwan Asiya gida. Kwana biyun farko zazzaɓi mai zafi ya sata a gaba. A kwana na uku ne ta samu ta fara warwarewa saboda ta rage tunani da kuka. Umma ta kan turo mata saƙo na ƙarfafa gwiwa kullum sannan Mama ma kullum tana cikin yi mata nasiha akan haƙuri da kuma yarda da ƙaddara. A wannan lokaci ta so ace Gwani na da rai. Yadda duk lokacin data shiga damuwa yake karanto mata tarihin Nana Asiya dan ya nuna mata mai sunanta jaruma ce da bata taɓa karaya ba.

*"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"*

Kalamansa kenan ranan da tazo ta sameshi tana kuka saboda Ale Faruƙ ya gaya mata cewa ya karɓi kuɗin aurenta a hannun Alhaji Talba. Tana shekaru shabiyar alokacin, Alhaji Talba kuma zai iya kaiwa shekaru hamsin da biyu zuwa da biyar. Da kuka wiwi ta iso zauren Gwani inda yake koyarda wasu manyan Almajirai dama wasu ɗalibai magidanta dake ɗaukan karatu a wajensa.

Bayan sun keɓe ta fara bayani

"Shi Baba komai kuÉ—i komai kuÉ—i. Ni gaskiya ba zan yarda ya sayar dani ba, ai bance masa aure nake so ba. Ni gaskiya karatu zan yi" tayi maganar cikin kuka.

"Ishiru Uwata, faÉ—a mini mi aka miki?"

Asiya ta goge hawaye ta zayyane masa duk abinda ya faru kan cewa Ale ne da safe ya gayawa Iyani da Fulani cewa su shirya karɓan baƙi gobe za a kawo kayan gaisuwar Asiya.

Ta haɗa da cewa " shi Baba rayuwarsa ta ƙare a kuɗi da mata. Abin kunya kwanakin baya daya saki Delu ina Bibalo ya auro. Bibalo fa, yarinyar da tun tana ƙarama take fama da taɓin hankali. Tsofai tsofai da shi ya ɓata mata rayuwa gashi Aljanunta sun hanata zama a gidansa"

Jin irin maganganun nan na fitowa daga bakin jikarsa zuciyarsa ta shiga ƙunci. Yai saurin karanto Isti'aza a zuciyarsa sannan ya riƙo hannun Asiya yace

*"Kina tunanin Allah ba zai jarrabce ki bane?"*

Tayi shiru tana kallonsa. Ya cigaba da yi mata nasiha tareda cewa ba abinda zata iya yiwa Ale sai dai ta rinƙa masa addu'ar Allah ya shirya shi, domin shi ɗin Uba ne gareta hakan kuma ba zai chanja ba har abada.

Bayan wannan abinda ya faru Gwani ya kira Ale Faruƙ ya masa faɗa yace bai hanashi aurar da 'yarsa ba idan ya ga hakane mafi alkhairi amma matuƙar yana raye ba zai taɓa bari ya mata auren dole ba kuma ko yayi bai yafe masa ba.

Saboda fasa auren da akayi Alhaji Talba ba ƙaramin rigima sukayi da Ale ba dan sai da suka yi kaca-kaca da shi.

Wannan dalilin ne kuma yasa Asiya ta dawo gidan Gwani da zama permanently har lokacin data samu admission a Congo University ta koma gidan Ummanta da zama.

Ale Faruƙ na kasuwa aka zo aka sameshi da zancen daya saka shi shiga mota ba takalmi dan har sai daya fita daga motar ya tunkari motocin Alhaji Sani Kachallah daya taka wani ƙaramin kara mai tsini ya lura cewa ashe babu takalmi a ƙafarsa. Wannan bai karya masa gwiwa ba yai saurin cire karan a ƙafarsa sannan ya ƙarisa motar daya ke tsakiya wacce yake tunanin a nan babban baƙonsa yake.

Samun buɗi ya sa Ale Faruƙ ya gyara ƙofar gidansa dama sashensa, wanda yanzu falo biyu gareshi ta farko ta karɓan baƙi ta biyu kuma wanda yake kallo ya ci abinci sannan anan yake zama da 'yan uwansa da abokansa na kusa lokaci zuwa lokaci.
Chapter 26 · 0% Book details