← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 38

Sashe 12

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan minti shida kafin CY ya gama saita komai ya É—agawa Asiya hannu yana faÉ—in one, two.... "ina zuwa CY" ta faÉ—a sannan ta yi saurin É—aukan ruwan da aka kawo mu su ta tsiyaya a kofi ta kafa kai sai da ta shanye. Ta sake tsiyaya wani ta shanye.

CY ya É—aga gira sama yana faÉ—in "Aseey are you nervous?"

Asiya ta yi saurin girgiza kai tareda yin gyaran murya ta ce "muje, na shirya "

CY na ɗaga ma ta hannu ta tattaro duk ƙarfin halinta ta fara bayani kamar haka *"ma su kallon mu barkar mu da warhaka, barkan mu da sake saduwa da ku a cikin shirin nan mai suna 'Siyasar mu a yau'. A yau dai za ku ga sauyin tsari, domin shirin namu kwacokam zai kawo muku hira ne da wani shahararren ɗan boko, ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wato mai girma Gwamna Saifuddeen Sa'ad Kachallah inda zai bamu cikakken tarihin rayuwar sa da yadda aka yi har ya kawo wannan matsayi. Ni Asiya-Shahidah Faruƙ Baba zan gabatar da shirin a madadin abokin aikina wato Comrade Faisal Kamaye"*

Sakataren Gwamna ne ya ƙariso wajen da sauri ya ɗan rankwafa yai wa Gwamna magana a kunne. Hakan ya sa C Y ya dakatar da ɗaukan shirin.

Gwamna ya kalli Asiya ya ce "za'a dakatar da shirin zuwa ƙarfe shaɗaya Insha Allah"

Bayan Gwamna ya tafi sannan Asiya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tareda fara yiwa kanta fiffita da hannu dan duk iskar wajen ta mata kaÉ—an.

CY ya matso wajenta yana yi mata dariya tareda tsokanarta kan cika bakin da tayi kafin zuwansu sai gashi ganinta kusa da Gwamna ta ruÉ—e.

Tun suna jiran Gwamna zai dawo ƙarfe shaɗaya har su ka fara sarewa ganin har ƙarfe ɗaya saura.

"CY anya ba za mu tafi ba. It seems wannan Gwamnan ya manta da mu fa"

Kafin CY ya bata amsa Sunusi driver yai saurin ɗaga murya da cewa ko ƙarfe nawa ne za su jira Gwamna tunda ya ce su jira shi.

"Bar Aseey, tana mana baƙin cikin kyautan da Gwamna zai mana ne" CY ya sa baki.

"Wannan maƙon ne zai baku kyauta?. Keep dreaming Clement".

"Allah idan aka bamu banda ke aciki tunda naga adawa ki ke da Gwamna" Sunusi ya faɗa yana ƙarisa sauran maltinan da Asiya ta rage.

Bayan Gwamna ya bar wajen su Asiya kai tsaye office É—insa ya wuce inda Alhaji Sani Kachallah ke jiransa. Idan ba shi É—in bama waye zai shiga office É—in Gwamna kai tsaye haka bayan Gwamna baya zaune a kujera.

"Baba sannu da zuwa" SSK ya faÉ—a yana faÉ—aÉ—a murmushinsa. Bayan sun yi musabaha sannan ya je ya zauna a kujerarsa yana kallon Alhaji Sani. Sun gama maganar naÉ—a mataimakin Gwamna tunda ya naÉ—a wanda su ke so bai san kuma mi ya kawo sirikin nasa office É—insa ba wannan safiya.

Bai yi mamaki ba da Alhaji Sani ya kawo maganar allowance na cabinet members daya riƙe. Sai dai duk da kunyan Alhajin daya ke ji hakan ba zai sa ya aiwatar da wannan baɗala ba.

"Baba tunda na hau kujeran nan na ke tsoron haƙƙin mutane da ke kaina. Idan na basu kuɗin nan tamkar na ci amanar wannan Jaha ce. Bayan ɗimbin albashi da sauran allowance da doka ta tanadar a basu miyasa zan sake ɗaukan maƙudan kuɗi na basu bayan akwai tarin ayyuka a gabana"

Gwamna yayi maganar ne a sanyaye saboda darajar Alhaji amma idan da zai fidda tiriri da zuciyar sa ke yi to ba ƙaramin amon wuta zai yi ba.

"Saifu kenan. Kaga siyasa lamari ne daya ke buƙatan hankali da takatsantsan. Kwata-kwata abun da za ka yi a wannan kujera kafin a sake wani zaɓe bai kai shekara ɗaya ba. Idan kuwa hakane dole ne ka tafi da mutanen nan yadda aka riga aka ɗaura su akai. Idan muna da rai kaci zaɓe sai ka fara naka sabon tsarin"

Gwamna yai shiru yana kallon Alhaji Sani. Yadda yai maganar cin zaɓe ya bashi mamaki. Domin zaɓe dai ba ayi ba balle a san ko zai koma kan kujerarsa ko ba ze koma ba.

"Baba da kamar wuya. KuÉ—in sun yi yawa"

"Ka biya kaso 70% na kuÉ—in"

Gwamna ya tauna leɓensa na ƙasa tareda sauke ajiyar zuciya. Yadda Alhaji Sani ya shawo kansa akan maganar naɗa Bala Yamai a matsayin Mataimakin Gwamna baya tunanin wannan karanma zai bar ofishinsa har sai ya samu abinda ya ke nema.

"Zan biya su kaso 40%"

Alhaji Sani ya ɗan ɗaga ido sama na ɗan daƙiƙu kafin ya sauke akan Gwamna Saifuddeen ya ce "mu rufe shi kaso 50% Saifu".

Bayan fitan Alhaji Sani daga office ɗin Sakatare ya shigo ya sanar da shi Contractors da za ayi meeting da su sun iso. Gwamna ya miƙe ya fita.

A chan wajen meeting ɗin ma wani ɓacin ran ya tarar domin kusan kaso saba'in da biyar na ayyukan da marigayi Gwamna Saminu Bacchi ya fara duk akan bashi ne. 'Yan Kwangila suna son a biyasu kuɗaɗen su idan ba haka ba sun dakatar da duk wasu ayyuka har sai baba ta gani.

Gwamna ya duba COS É—insa sannan ya maida dubansa ga Mr Paul. WaÉ—annan biyun sun fi kowa É—aga jijiyar wuya akan maganar allowance amma yanzu ana maganar ayyukan cigaba na Jaha amma kowannen su yayi tsit.

Kuɗin allowance ɗin nan da su ke buƙata idan da za a haɗa na wata huɗu zai biya gaba ɗaya basussukan da contractors ɗin nan su ke bin Gwamnati.

Haƙuri Gwamna ya basu tareda mu su alƙawarin zai biyasu dukkan kuɗaɗen su zuwa wani watan sai dai wannan wata za su fara ne da kaso 25% na kuɗin da zai biya su. Basu ɗau lokaci ba suka amince da maganar Gwamna.

A take a lokacin Mr Paul ya miƙa masa wasu takardu tareda check Gwamna ya saka hannu sannan aka miƙawa jagoran contractors ɗin wato Mr Azad Sahib Khan.

Gwamna na komawa kan kujerarsa Mr Paul da COS suka biyo bayansa da takardar da suke son ya saka hannu. Gwamna ya duba takardan a walaƙance sannan ya kalli fiskar Mr Paul wanda ƙarara ta nuna bai ji daɗin kaso 50% ɗin da za a basu ba ya ce " Mr Paul ina fata baka manta maganan ƙarin albashin malaman makaratan firamare ba"

"Your excellency na sani"

"Good".

Kusan ƙarfe biyu saura kwata da Gwamna zai fita sallar Azahar Sakatare ya tuna masa da su Asiya da ke jiransa tun ƙarfe goma.

Gwamna ya girgiza kai ya ce su dawo gobe dan akwai inda zai je idan yayi sallah.

Idon Asiya ɗar akan wayarta lokacin da wani security ya iso ya ce musu Gwamna ya ce su dawo gobe ƙarfe goma.

"Kan Uba..."

"Mungode zamu dawo gobe É—in" CY ya faÉ—a yana hararan Asiya.

Har suka isa ma'aikatarsu Asiya bata bar zagin Gwamna ba kan walaƙantasu da yai. Har iƙirari ta yi akan gobe ba za ta koma ba sai dai Comrade Faisal ya je yai tunda dama asali shirinsa ne. Sai dai MD bai bata damar hakan ba dan cewa yai ita ɗin dai yakeso tayi hiran da Gwamna goben.

Da dare da Ubayd ya zo hira kaman ta shaƙeshi dan yadda ta ke masifa tamkar shine Gwamnan.

"Mine, sunana Ubaydullah ni Likitan Ido ne ba Gwamnan Jahar Congo ba. Ki ajiye fushinki a gefe please"

"Dan shi Gwamna ne sai akace ya maidamu Awakai. He treat us like goats fa. Ya shanya mu for good 4 hours munata jiransa"

"My Asiya Gwamna fa akace. The first citizen of the state"

"And so bloody what!"

"Shikenan. Yayi haka a chanja hiran"

"Da wani shegen idonsa a wajen..." ta ƙarisa ƙarshen jimlar a hankali saboda wani abu da ya zo ya dabaibayeta. Idon da ta ke zagi shi dai ta gani yau ta birkice, ta rasa nitsuwarta. Idon ne dai da ya ke sukanta kamar kibiya lokacin da ta ke zaune daura da shi kafin CY ya gama haɗa camera.

Ba ta gayawa Ubayd wannan ba ƙila shiyasa ta dage kawai akan cin mutuncin da Gwamna ya mu su. Sai da Ubayd ya sako zancen kayan lefenta da yake haɗawa kafin ta ture maganan Gwamna a gefe ta koma ta rayuwar da su ke shirin farawa tare nan da watanni kaɗan.

***

Taron gaggawa Mr Paul ya kira a gidan Yallaɓai tunda suka haɗu kuwa aketa cacar baki sai da Yallaɓai ya tsawatar kafin sukayi shiru.

"Mr Paul ina sauraronka"

Mr Paul ya ɗaga takardar da Gwamna SSK ya sa hannu yace "Yallaɓai tunda Saminu Bacchi ya hau kujera bai taɓa chanja tsarinmu ba amma gashi nan wata biyu da hawan Saifuddeen ya hanamu allowance lokacin da ya ga daman bamu kuwa kaso hamsin ya bayar. Ka gaya min ta ina zamu yarda da wannan cin mutunci. Idan har ba zai iya ba to kuwa yai resigning a ɗaura Bala Yamai"

"Ka ci gidanku Eugene Paul. A gabana kake cewa Saifu yai resigning saboda baka da hankali"

"Alhaji Kachallah ka kama girmanka, ka san bana yarda da cin mutunci a gidan nan"

"Ayi haƙuri Yallaɓai amma Paul ya sani cewa an ɗaura Bala Yamai ne ba dan shi ba sai dan kawai lokacin saka mutumin Agun ne a matsayin mataimakin Gwamna. Ya kamata kuma ya sani cewa ba zan lamunta a ci mutuncin ɗana ba"

Bayan duka ɓangare biyu sun gama gabatar da ƙorafinsu sannan Yallaɓai yai magana.

"Kowani Gwamna muna bashi wata shida dan ya aiwatar da abinda ya ga dama a farkon tenure da kuma ƙarshen tenure ɗinsa. Lokacin Saifuddeen ne yanzu, Mr Paul ka barshi yai abinda yake so"

"Amma..." Yallaɓai ya ɗagawa Mr Paul hannu hakan ya sa shi datse maganarsa.

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

06
Chapter 12 · 0% Book details