Sashe 15
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana gama karanta rubutun ta sauka tareda jan dogon tsaki. Wai sunata maganan Lamara Damana, Lamara Damana, shi waye da za ta ji tsoronsa. Idan har ba za a fitar da labarin a ma'aikatarsu ba ai akwai social media. Ringing ɗin wayarta ya dawo da ita daga tunanin da takeyi. Koda ta ɗauki wayar Ubayd cigaba da roƙonta yayi yana cewa ta masa alƙawarin ba abinda za tayi, da ta ga ya dameta tace mishi ta ji za ta yi shiru sai dai chan ƙasan ranta ta san ba haka bane.
Lokacin da suka tashi CY ne ya nemi ya kaita gida saboda yana son jin labarin miye dalilin sauya tambayoyi da tayi, sannan miye dalilin da yasa COS ya nemi ganinta.
"Na san gulma ne ya kawoka Clement kuma ba za ka ji komai ba"
"Ahn-Ahn, Aseey Darling ya zaki fassarani haka, jiya ma fa ni na kai ki gida"
"Ahaf, ka gama kame-kamen naka dai ka dawo hanya, magulmaci"
CY yai dariya ya wuce gaba.
Suna fita daga ma'aikatar Obinze Maigadi ya É—aga waya jiki na rawa ya kira wata number ya ce yanzu Asiya ta fita daga ma'aikatar tasu ya haÉ—a da cewa tare take da abokin aikinta akan machine kafin aka katse kiran.
CY na tuƙi yana yiwa Asiya taɗin budurwarshi mai suna Evelyn da ta ce masa dole sai ya koma ɗariƙar Katolika (catholic) kafin ta iya auren shi, Asiya tana masa dariya. Ba suyi aune ba dai-dai za suyi kwana wata babbar mota da basusan daga ina ta fito ba ta zo ta mangajesu hakan yasa Asiya tsalle sama ta faɗi gefe yayinda motar tabi ta kan machine da ta danne CY ta wuce da bala'in gudu...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
07
"Darling" Bilkisu Kachallah ta kira da fake American accent É—inta wanda kunnen Saifuddeen ya kasa banbance "Dolin" tace ko kuma "Durling". Ya dai É—ago ido ya kalleta ba tareda ya furta komai ba. Ya sani ya kamata ya ce mata tayi kyau ko kuma yace jan lingerie (rigar bacci) data saka ya amshi jikinta sosai amma bai ce komai ba.
A mafiya lokuta idan ta yi shiga irin wannan tana buƙatarsa ne, ba kawai buƙata ba domin daga ƙarshe idan ta kwanta gefensa tana shafa gashin ƙirjinshi a hankali za ta bijiro masa da wata buƙatar ne, mafiya yawanci abubuwanda take tunanin ba zai mata su ba idan ta tambayeshi kafin ta shigo turakarsa su take tambaya.
Rabonsa da ita tun ranan farko da suka tare a gidan Gwamnati. Ba wai baya buƙatarta bane amma rashin nuna damuwarta gareshi yasa yake haƙuri da ita, ƙila saboda a koyaushe baya son takura mata ne. She's not yet 40 amma kuma lamarin sex life ɗinsu ya lalace tun lokacin da ta haifi Junior.
Takardu yake dubawa ta tura takardun gefe ta shiga kissing ɗinsa, farko daga goshinsa, kunnensa kafin ta kai bakinsa. Ba a jima ba ya tureta yace " ki bani minti goma na ƙarisa aikin dana ke"
"Haba Darling, ka san yaushe rabonka da ni kuwa? Aiki can wait please" ta faɗa tana zunɓura baki.
So yake ya ce mata laifinta ne idan bai nemeta ba tsawon kwanakin nan, saboda duk lokacin daya samu free time yake buƙatar kulawarta baya samu, amma bai faɗi hakan ba sai yayi mata murmushinsa mai shiga rai yace " kar ki damu, ba zan jima ba"
Bilkisu ta kwanta gefen gado tana kallon ceiling yayinda ya cigaba da duba takardun da idan bai duba yanzun ba bashida lokacin duba su gobe. Kusan minti talatin da uku kafin ya gama komai lokacin har Bilkisu ta fara gwarti. Ya je ya ajiye takardun acikin wani file ya saka a briefcase.
Bai tashi Bilkisu ba saboda ya san a gajiye take yau tace masa ta fita duba gidan marayu bai san details É—inba kuma bai tambayeta ba.
"Shine baka tasheni ba" ta faÉ—a lokacin da ta tashi da Asuba.
"You're tired"
"Still" ta faÉ—a tana haÉ—e rai.
"To barin dawo daga masallaci"
Lokacin daya dawo daga sallar Asuba ta riga tayi wanka ta chanja kaya, ba rigar bacci ta sa ba amma shima kamar na jiya guntu ne mai hannun spaghetti, rigan ya kamata sosai, ya bayyana ƙaton tumbinta da yake a taƙune.
Kamar yadda yai hasashe yana shirin miƙewa ya je yai wanka ta faɗa masa buƙatarta na son buɗe Bilkisu Kachallah Foundation dan tallafawa marayu. Ajiyar zuciya yai sannan yace "Allah ya sanya alkhairi" ya wuce banɗaki tda sauri...
Meeting biyu ya shiga daga zuwansa office, yanzun ma wani meeting É—in zai shiga nan da minti talatin. Yana duba report É—in da aka kawo masa. Sakatare ya shigo da wasu takardu a hannunsa.
"Your excellency na samu COS ya reschedulling ziyarar da za ka kai ƙaramar hukumar Antu zuwa jibi laraba"
"Ok" Gwamna ya faÉ—a yana cigaba da duba takardun da ke gabansa.
"Excellency kafin na manta. 'Yan jaridar da suka zo jiya sun yi hatsari"
"Asya!" Gwamna ya É—ago kai da mamaki
"Ita da abokin aikinta suna komawa gida wata babbar mota ta afka musu..."
"Is she alive?" Ya faÉ—a da tsananin damuwa a tattare da shi
"Na ji labarin dukansu suna raye. Ita Asiya ance nata da sauƙi amma shi ɗayan kam rai a hannun Allah"
"Hasbunallah! Keep me posted akan labarinta" ya faÉ—i labarinta kamar ita É—aya akace tayi hatsarin.
Bayan fitan Sakatare daga office ɗinsa ya ɗaura haɓarsa akan hannunsa yana tuna siririn ushiryar dake tsakanin haƙoranta wanda yake ƙara mata kyau idan tana murmushi.
***
Umma ne a gefen gadon da aka kwantar da Asiya lokacin da Ubayd da Abba suka shigo. Abba ya tambayeta ko Asiyan ta tashi tace masa bata tashi ba. Lokacin daya zauna ta tambayeshi jikin abokin aikin Asiya Abba yace ance musu har yanzu bai farfaɗo ba. Ubayd ya ƙurawa Asiya da ke kwance ido bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba. Ba dan kariyar Allah ba da ita ne ke halin da CY yake ciki ko kuma ace da yanzu an jima da bisineta. Yai saurin goge hawayensa dan kar Umma ta gani. Alhamdulillah ya furta a ransa kafin ya yiwa su Umma sallama ya fita.
Ba a jima ba Asiya ta farka a karo na biyu tun safiyar yau. Da farko data farka kuka ta dinga yi tana faÉ—in a kaita wajen CY. Yadda ta birkice musu sai da aka mata alluran bacci.
Wannan karan ma data farka sunan CY ta kira. "Abba CY ya mutu ko?, sun kashe shi ko?"
"Kwantar da hankalinki Shahidah. Yana nan da ransa"
Da bata faÉ—a gefen titi ba, da ba wannan zancen akeyi akanta ba. Gefen goshinta, kunnenta da kafaÉ—arta sai kuma gwiwarta da ya kurje su kaÉ—ai ne ciwon jikinta, sai dai saboda irin faÉ—uwar data yi duk jikinta ciwo yake mata.
Asiya ta sauke ajiyar zuciya hawaye na zubo mata.
"Abba idan CY ya mutu bazan taɓa yafe musu ba. Kuma sai na..."
"Asiya!" Ya kira sunanta da ƙarfi har sai da ta tsorata.
"Ba abinda zakiyi, kina jina? Nace ba abinda zakiyi. Zan mummunan saɓa miki idan kika sake maganan mutanen nan"
"Abba..."
"Zamuyi magana idan munje gida"
Ta kalli Abba da mamaki, ba yadda za ayi yai wannan maganar sai dai idan har yasan wani abu. Kenan Lamara Damana ya tuntuɓeshi.
Da yamma da Ubayd ya dawo ta tambayeshi ina CY yace mata CY na CUTH (Congo University Teaching Hospital ) an É—aura shi a na'ura saboda ya shiga coma.
"Mutuwa zai yi ko?" Ta tambaya murya na rawa
"Mine mutuwa a hannun Allah take. Ki masa addu'a amma he's in a very bad shape infact an yanke masa hannu É—aya"
"Ya Allah!" Ta riƙe baƙi.
'Yan wajen aikinsu sun zo sun gaisheta. MD shi kaɗai yazo da yamma lis kuma bai jima ba saboda lokacin ɗakin nata akwai mutane. Lokacin daya fita Abba ya bi bayansa da sauri. Bayan sun samu waje sun keɓe sannan MD ya bashi takardar dakatar da aiki na Asiya. Abban ne ya nemi hakan shiyasa yana karɓa ya masa godiya ya koma cikin Asibitin.
MD ya girgiza kai yana fata wannan ya zamowa Asiya mafita saboda ta tsokano tsuliyar dodo.
Kwanan Asiya biyar a Asibiti aka sallameta har lokacin kuwa ba suyi maganar abinda ya faru da kowa ba saboda Abba ya hanata. Kamar yadda kowa ya É—auka cewa tsautsayi ne ya kawo hatsarin da suka yi Asiya ta san ba haka bane kuma ta san Abba da Ubayd ma sun san ba hakan bane.
Kafin su wuce gida ta roƙi Ubayd da ke tuƙi akan ya kaita taga CY. Da farko ya ƙi amma data takura sai Umma tace ya kaita itama tana son zuwa dubashi.
Lokacin da taga CY kwance an jona masa wasu na'ura a jiki sai kawai ta fashe da kuka. Da Allah yayiwo CY mace da zata iya cewa har abada ba za ta iya samun ƙawa kamarta ba saboda yadda jininsu ya haɗu kuma suka fahimci juna, sai dai CY namiji ne shiyasa abotar tasu take da iyaka.
Sun gaisa da mahaifiyarshi inda take jadaddawa Asiya cewa Gwamna ya biya kuɗin aikin da za a masa a ƙasar waje takardunta da ake processing yasa basu tafi ba sai wani sati. Jin Josephine mahaifiyar CY ta ambaci sunan Gwamna yasa zuciyar Asiya ta cunkushe, tsanar mutumin ya sake sauka mata. Munafuki ta faɗa a ranta, shine ya jawo wannan matsalar sannan yake ƙoƙarin rufe bakin mutane da maganar biyan kuɗin aiki. Ita Asiya ba zata yi shiru ba, tayi alkawari.
Sanda suka isa gida Abba ya zaunar da ita ya mata bayani.
"Abinda ya faru Asiya ki ɗauke shi a matsayin ƙaddara. Ki riƙe bakin ki da zargi domin ba abinda hakan zai jawo sai fitina. Na saka an dakatar dake daga aikin ki, daga yanzu babu ke babu aikin jarida. Ban sani ba idan kin koma ƙarƙashin ikon Ubaydullah ko zai barki kiyi amma iya watannin daya rage miki ƙarƙashin kulawata, na dakatar da aikin ki"
Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa