← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 38

Sashe 22

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune ne a gidan amma gaba É—aya komai na gidan ya fita mata aka. Akwai lokutan da take tunanin gara kawai Ale FaruÆ™ ya saketa. Sai dai dokar sa ce baya sakin mace kafin ta cika shekara biyu. A cewarsa lokacin bai gama morar kuÉ—insa ba.

A cikin shekara na biyu da auren Zainabu da Ale Faruƙ ta sake samun ciki. Cikin yazo mata da laulayi mai tsanani amma babu wanda yake tausaya mata a gidan. Ba ta son warin abinci, bata cin abinci sai ƙanzo da kunun tsamiya. Idan za ta yi girki sai dai ta sa tsumma ta rufe hancinta saboda kar ta ji ƙanshin. Ranan da ta ƙi yiwa Fulani girki ta nuna cewa sai dai tayi tunda ranan girkinta ne haka ta mata chaa har da mata kashedin indai bata yi girkin ba za ta mata duka a gidan.

Ranan da Ale Faruƙ ya dawo ɗakinta, tace masa ya gayawa matansa cewa ba zata sake yiwa kowacce girki ba. Abin mamaki sai cewa yai tunda ta riga ta fara sai dai ta cigaba da hakan har zuwa lokacin da zasu ce ta dena. Abin ya ƙona mata rai. Bata taɓa tunanin kai ƙaran Ale ko matansa ba, koda wasu cikin 'yan uwanta sun kawo mata ziyara nunawa take bata cikin matsala.

Washegari ta saka hijabi ta wuce gidan mahaifinsa.

Ɗan karatun allo da tayi kafin aurenta da shi ta iya rubuta bayaninta da rubutun ajami a takarda ta miƙawa Mama Indo matar Gwani. Mama tana karantawa sai ga hawaye ya cika mata fiska. Tana tambaya ne akan ko addini ya bayarwa namiji daman ya yi rashin adalci tsakanin matansa. Sannan idan ta ƙi yiwa matan mijinta aiki akwai zunubi awajen Allah?

Mama bata bari Gwani ya gama karatu da almajiransa ba ta aika akan ya zo akwai matsala. Koda ta bayyanawa Gwani abinda Zainab ta faɗa ransa ya ɓaci sosai. A kullum tsakaninsa da Faruƙ shawara da addu'a domin muguwar tarbiyar da Tabawa ta bashi da kuma jahilci da ke damunsa shiyasa yake tafiyar da rayuwansa bisa ra'ayin kansa. Arziƙi dai Allah ya bashi amma ni'imar ilimi da kakansa Malam Falke keda shi, da Gwani keda shi da ƙannensa Malam da Zakari keda shi ya barranta masa. Bai nemi ilimi yana ƙuruciya ba kuma har yanzu da yake da damar neman ilimi kuɗi da mata sune a gabansa.

Gwani ya fayyace mata hakkin mace akan mijinta da hakkin miji akan matarsa hakan yasa zuciyar Zainab ya É—an yi sanyi.

Mama da kanta taje gidan ta tara matan Ale Faruƙ ta gaya musu saƙon Gwani akan duk wacce ta sake takurawa Zainab zai mugun saɓa mata. Yadda basa shakkan Tabawa haka suke tsananin shakkan Gwani.

Tabawa na zaune ƙofar ɗaki tana tauna goro ta fara faɗin "su matar Malam manya. Duk tsiyar ki dai Faruƙ ɗana ne. Idan Allah bai bashi ilimi ba ai ya bashi arziƙi" ...

Daga ranan kowacce mata ta karɓi girkinta.

Cikin Zainabu na wata bakwai Gambo wata maƙociyarsu ta fita daga takaba hakan ya sa Ale Faruƙ ya fito nemanta. Kamar kowacce mace arziƙinsa, kyaun surarsa da kuma gulmar ƙarfinsa da matan daya saka suke, shi ya kwaɗaita wa Gambo shiga gidansa, sai dai ta san mata huɗu gareshi.

Halime, Ale Faruƙ yai niyyan saka saboda ta kwana biyu a gidansa amma tunda ta masa rantsuwar duk ranan da ya saketa sai ta yanke masa gaba sai ya chanja tunani. Ba zai saki Iyani ba saboda itace uwar manyan 'ya'yansa sannan Fulani kuma ya rasa dalilin da yasa ya kasa sakinta. Kurma ce kawai zai iya saka a halin daya samu kansa sai dai kuma gaskiya bai shirya rabuwa da ita yanzu ba, har yanzu akwai ƙuruciya a tareda ita. Kuma ita kaɗaice macen da idan yace tayi abu za tayi idan yace ta bari ma zata bari.

Da dai yaga Alhaji Mato na ƙoƙarin kauda shi a wajen Gambo sai ya yanke ɗanyen shawaran sakin Zainabu.

Da sassafiya ya shiga ɗakinta ya miƙa mata takarda ya mata bayanin zata iya zama a ɗaya daga cikin ɗakunan gidan har ta haihu. Ba tayi boko ba shiyasa ko karanta hausar daya rubuta bata iya yi ba. Zuwa tayi wajen Jamilah ɗaya daga cikin yaransa wacce take da ɗan hankali tace ta rubuta mata abinda Ale ya rubuta da ajami. Jamilah ta rubuta mata kamar yadda ya rubuta da Hausa *na saki Zainabu saki ɗaya* bayan ta karanta rubuntun da Jamilar tayi a ƙasan na Ale, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauki takardar ta koma ɗakinta ta shiga haɗa kayanta. Zuwa ƙarfe sha biyu na rana ta gama tattara kayanta ta wuce gidan Inna Talatu. Ba zata iya komawa wajen Mama Asabe ba saboda a halin da take ciki wajen da zata samu kwanciyar hankali take nema.

A wajen Inna Talatu yar mahaifiyarta ce kaÉ—ai zata iya samun wannan.

Haka kwanaki suka dinga tafiya har wata ranan Jumma'a ranan da cikin Zainabu ya shiga wata tara da kwana biyar ta haifi kyakykyawar 'yarta.

Suna dawowa daga Asibiti da É—anyan haihuwa haka ta É—auki 'yarta ta wuce gidan Gwani da ita haÉ—e da takardar da ta rubuta ranan da Ale FaruÆ™ ya saketa.

Gwani na alwalar sallar la'asar Zainab ta shigo É—auke da jaririya a hannunta.

Tana zuwa gabansa ta ɗan rusuna sannan ta miƙa masa takardar hannunta.

Gwani da hankalinsa ya tashi da ganinta haka ya karɓi takardar yana ƙwalawa Mama kira.

Lokacin daya karanta takardar hawaye ya taru a idonsa. Tausayin É—ansa FaruÆ™ ya fi kamashi akan na Zainabu. Mama ta fito daga É—akinta tana tambayar Zainabu yaushe ta sauka amma Zainabu bata kulata ba.

Gwani ya ajiye takardar ya ƙarisa alwalarsa sannan yai wa Zainabu alamar ta miƙo masa jaririyar. Zainabu ta miƙa masa 'yar.

Gwani yai wa yarinyar kiran sallah a kunnenta na dama sannan yai mata iƙama a kunnenta na hagu kafin ya gama Mama ta shiga ɗakinta ta ɗauko masa dabino, dake cimar Gwani ne ba a rasawa a ɗakinta.

HuÉ—uba yaiwa 'yar da suna Asiya Shahidah sannan ya shiga tofa mata duka addu'o'in da Zainabu ta rubuta a takardar data kawo.

Yai addu'ar kada Allah ya sa ta ɗauko ko ɗaya daga cikin halayen mahaifinta da ta kakarta Tabawa. Yai addu'ar ta zamo mai ilimi, mai tausayi, mai imani da riƙon amana. Yai addu'ar kada ta zamo azzaluma mai tauye hakkin mutane, yai addu'ar yadda mahaifiyarta bata ji bata magana Allah ya sa ta ji ta kuma yi magana. Yai addu'ar ta zama jaruma marar tsoro wacce akoda yaushe neman gaskiya da aiwatar da gaskiya shine halinta, yai addu'ar Allah ya kareta daga sharrin Mutane, Aljanu, Dabbobi da kuma Shaiɗan la'ananne. Yai addu'ar ta zamo abin alfahari ga iyayenta dama al'ummar musulmai gaba ɗaya. Ya ƙara da cewa yana addu'ar ta samu tabarakkin mai sunanta wato Nana Asiyah.

Bayan ya gama addu'o'in sannan ya karɓi dabino a hannun matarsa ya gutsura ya tauna sannan ya sakawa Asiya a baki. Sai alokacin Zainabu ta fara murmushi.

Ita da Mama ne suka koma gidan Inna Talatu wacce ta birkice saboda rasa Zainabun da akayi a gidan...

A gidan Gwani aka yi suna dan kwana huÉ—u da haihuwan ya nemi Zainabun ta dawo gidansa. Kunyar Baban tsohon mijinta ya sa bata iya musawa ba. Ale FaruÆ™ ma dai nauyin Gwani daya ji ya sa shi kawo rago da kuÉ—i dan a yi suna da shi.

***

Tun kafin Asiya ta cika shekara biyu Inna Talatu ke yiwa babban É—anta mai suna Nuhu kwaÉ—ayin ya auri Zainabu. Matarsa ta farko ta rasu sannan Yahanasu da ya aura wacce ita É—in 'yar dangin mahaifinsa ce sai ta kasance fitinanniyar mace.

Shekarar Asiya uku aka yi auren Malam Nuhu Principal da Zainabu Kurma. Lokacin da Ale Faruƙ ya ji labarin auren baƙinciki kamar ya kashe shi, duk cikin matan daya rabu da su babu wacce yake jin rabuwar da ciwo kamar rabuwarsa da Zainabu. Ya rabu da Halime ita kuma Gambo data shigo gidansa tama fi Fulani fitina.

Malam Nuhu GidaÉ—o Malamin makaranta ne da ya kai matsayin Principal inda yanzu yake shugaban makarantar Special School Congo.

Matarsa ta farko Hassana sati biyar da haihuwa ta rasu hakan ya sa rainon É—ansa Ubaydullah ya koma wajen 'ya uwarta Hussaina. Shekaru uku da rasuwan matarsa kafin Mahaifinsa ya haÉ—a shi aure da Yahanasu wacce take marainiya a lokacin.

Lokacin daya auri Zainabu yaran Yaha uku ne duka mata. Aisha da suke kira da Ummi sai Fatima sai kuma Hindatu daga baya ne ta haifi Musa bayan ita Zainabun ta haifi É—anta na fari wato Muhammad Habibu sai Lukman da suke kira da Gwani sai autanta Aliyu.

Sanda Zainabu ta tare ko wata huɗu batayi ba Malam Nuhu ya sata a makarantar kurame inda ake koya musu rubutu da karatu da kuma sana'o'i. A nan ne ta koyi ɗinki da saƙa.

Asiya Shahidah ta taso ne tsakanin gidan Gwani da Inna Talatu bata zuwa gidan Mahaifinta sai dai idan shine yazo ya ɗauketa dan Allah ya saka masa ƙaunar Asiya. Saboda ita ne ma ya dage da zuwa gidan Gwani duk bayan kwana biyu maimakon da da sai yai sati biyu uku bai leƙa mahaifin nasa ba. A duk lokacin da ya zo idan yaji Gwani yana yabon kwanyar Asiya akan tana ɗaukan karatu sai ya dinga jin wani nishaɗi a tattare da shi. Duk yaransa a wajen Gwani suke zuwa ɗaukan karatu tun suna shekara biyu da rabi yake sawa a tisa ƙeyarsu wajen Mahaifinsa. Kuma duk cikinsu idan ka cire babban ɗansa Nafi'u daya rasu babu wanda ya taɓa ji Gwani ya yabi kaifin ƙwaƙwalwarsa kaman yadda yake yabon Asiya. Wani lokaci idan yazo sai ya ce Asiya ta ɗauko Allonta ta biya masa karatu ya ji. Duk da idan ka cire karatun sallah shi kam Jahilin Ƙur'ani ne hakan bai hana shi jin daɗin karatun Asiya ba.

Allah ya buɗa masa arziƙi amma hakan bai hana wani lokacin ya ji kishin ƙannensa Malam da Zakari ba, wanda suma Malamai ne yanzu domin sunyi karatu mai zurfi.

Dake idan Asiya tazo gidan Ale Faruƙ damunsu take da rigima shiyasa basa ma son zuwanta gidan musamman Fulani da Tabawa. Bata taɓa yin shiru idan aka gaya mata magana.
Chapter 22 · 0% Book details