← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 38

Sashe 34

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wa ye keda jaridar Climax?"

Ya tambayi COS bayan wasu mintoci daya É—auka bai yi magana ba.

"Da dai wani ne Mr Emmanuel Bassey amma na ji ance wani É—an siyasa ya siyi jaridar watanni biyu da suka wuce"

"Ka bincika min waya siya"

"An gama excellency"

***

Asiya kuwa tsaf ta shirya dan fara aiki da investigative reporter mai suna Fou'ad Salisu. Shekaransa uku da fara aiki amma ya fitar da manya-manyan report guda biyu da ya ɗaukaka shi a ƙasar da ma duniya baki ɗaya.

Fou'ad ya yiwa Asiya alƙawarin binciko mata abin da take nema cikin ƙanƙanin lokaci...

Asiya na zaune akan kujera ta harɗe ƙafafuwanta, hannunta ɗaya riƙe da waya tana karatu, ɗayan kuma soyayyiyar gyaɗa take ci da shi. Lokaci lokaci ta kan yi dariya. Wannan karan da ta fara dariya harda tunkuɗe kwanon gyaɗa da ke gefenta.

Sumayya da ke rubutu a kan carpet ta ɗago ido ta kalli 'yaruwarta tana tambayarta ko lafiya. Sai da Asiya ta yi dariya ta isheta kafin ta ce "wani waƙar KaSaSa nake karantawa wai Attaruhu, kin ji abin dariya. Kai matar nan Allah ya bata baiwar tsara waƙa. Bari ki ji na karanta miki..."

Sallamar Uwani ya katseta. "Ranki shi daɗe kinada baƙi a falo"

"Su waye?"

"Yaya Bello ne da wani tsoho"

Asiya ta kalli Sumayya, Sumayya ta kalli Asiya, dukkansu suka haÉ—a baki wajen faÉ—in "Ale".

Asiya ta sako hijabi ta fito yayinda Sumayya tace fir bazata fito ba. Ale na zaune yana kora lemu Asiya ta shigo falon.

"Matar Gwamna" Ale ya faɗa da ƙarfi kaman wani Yaro.

Asiya ta haÉ—e rai ta zauna nesa da su tace "Baba lafiya?"

"Haba Asiya Shahidan Baba. Babu gaisuwa sai tambaya"

"To ai ni ban taɓa jin inda aka yi aure sati biyu Baban Amarya ya fara bibiyar 'yarsa ba, sai dai idan babu lafiya ne"

"Lafiya ƙalau muke, su Baffanki ma sun ce na gaisheki"

Yaya Bello ya miƙe yace "barin barku ku tattauna"

Asiya ta harareshi dan ta san shine zai yiwa Ale kwatancen gidanta. Sai kuma ta tuna Ale da Yaya Bello basa shiri.

"Tunda na miki maganar kwangila kika dena É—aukan kirana. Haka ake yi, ko kin shigo daula kin manta da iyayenki ne"

"Ban manta da iyayen da tunda nayi aure suke aiko mani da addu'a ba. Amma na manta da Uban da ke maula a wajen mijin 'yarsa"

"Asiya!" Ale ya faɗa yana miƙewa a fusace.

Basu ji shigowar Gwamna falon ba sai da yai sallama.

Asiya ta kalleshi ta kauda kai yayinda Ale ya shiga gaishe shi jiki na rawa.

"Asya" ya kira a hankali. Ta É—ago ido ta kalleshi

"Follow me"

A tsakiyar falonsa ya tsaya, ya juyo ya kalleta. Yana tattare da fushin Bilkisu da Nana abinda ma ya hana ya fara wucewa chan gidan kenan, ya biyo nan ne saboda ya É—an huce kafin ya je gida, kada garin fushi zuciyarsa ta sa shi aikata abinda bai dace ba. To gashi ya zo nan ma itama wannan Attaruhun tana yiwa mahaifinta rashin kunya.

"Disrespecting your father Asya. Kin san darajan Uba kuwa, kin san mutane nawa ne a duniya ke kukan rashin Uba. Ba zan lamunci wannan ba, ki je ki bawa mahaifinki haƙuri"

"Ba abinda zan yi. Ba a chanja Uba amma ni na chanja ranan da ya sayar maka ni. Idan ba zaka lamunta ba ka sake ni mana, ai kasan yadda nake sarai amma ka nace sai da ka aureni saboda zalin....ci"

Numfashinta sai da ya kusa ɗaukewa saboda matsowa da Gwamna yai daf da ita. Kallo ɗaya ta yiwa ƙwayar idonsa ta san babu wasa tattare da shi.

"Na gaya miki iya zaman da za mu yi tare dole ne ki riƙe matsayin Matar Gwamna da kyau, which means duk wani rashin kunya, shirme da shiririta za ki ajiye su gefe. Ki je ki bawa mahaifinki haƙuri kafin raina ya ɓaci"

Ai da sauri Asiya ta bar falon. Bata manta kashedinsa ba, daren farko da aka kawota gidan. Ya riga ya san abu É—aya take tsoro, kuma da shi ne kawai zai iya maganinta.

Ale na zaune yana jujjuya maganganun Asiya a ransa, Asiya ta shigo falon.

"Kayi haƙuri Baba" Asiya ta faɗa ba tareda maganar ya kai zuciyarta ba. Ta tsani halin mahaifinta fiye da soyayyar da take mishi.

"Ya zan yi da 'ya'yan zamani. Allah ne ya baki wannan matsayi Asiya, ni ba sayar da ke nayi ba.

"Na ji daɗi da kika kawo Bello kusa da ke, ina fata za ki nutsar da shi ya dena shaye-shaye, yai ƙoƙarin ajiye Iyali. Na barki lafiya"

"Baba" Asiya ta kira da muryar kuka.

Ale ya juyo ya kalleta jikinsa a sanyaye.

"Ka yafe min dan Allah"

"Na yafe miki, nima ki yafeni in Allah ya so ya yarda ba zan sake yi miki maula ba"

"Haba Ale Faruƙu na gidan Tabawa da Gwani Lukman. Ni fa ban ce kana maula ba, inaga dai daga TV ka ji wannan maganar"

Ta yi maganar tana kamo hannunsa ta zaunar da shi a kujera. Wani abu ta gani a idonsa lokacin da yai maganarsa ta ƙarshe. Bata taɓa tunanin Ale zai ji kunya ko yai danasanin wani abu ba, amma yau ta ga kunya a idonsa, ya yi danasanin neman alfarma da ya zo yi.

"Baba barin shiga kitchen da kaina na maka girki"

Ale yai dariya yace "Ina Sumayye? ko ta je makaranta"

"Barin kira maka ita".

Asiya ta shiga kitchen ta zage ta yiwa Ale girki. Tuwon shinkafa miyar kuka da ya ji naman kaza ta yi, ta haÉ—a masa da tacaccen juice É—in Kankana da Abarba.

Ale ya ci abincin sosai ya kuma sa albarka. Da zai tafi ya ce ta gaishe masa da Gwamna ya ajiye mata kyautar da ya kawo wa Gwamna na tacacciyar Zuma a cikin jarka 5 liter.

Ga mamakin Asiya lokacin da ta shiga falon Gwamna sai ta sameshi a dining table yana cin abincin da ta girka.

Ta san dai ta ɗebi abincin Ale sannan ta barwa Sumayya ta kwashe sauran. Yaushe Sumayya ta haura sama ta kawo masa abinci bata sani ba?. Tukunnama dama tuntuni bai fita bane. Ita ba sanin ranakun ta yi ba balle ta gane yau kwananta ne ko ba nata bane. Bata taɓa masa girki ba, idan ya zo gidanta bata san ya yake cin abinci ba, bata ma san su waye ke gyara masa sashensa ba.

Gaskiyar Sha'awanatu Bacchi ne da tace dole ta koma gidan Gwamnati. Idan suka cigaba da zama irin haka ba zata rinƙa samun bayanai akansa ba.

"Babana ya wuce, ya bayar da wannan a baka"

Ta ajiye jarkar kusa da ƙafarsa. Bata san ya akayi ta tsaya kallon ƙafarsa ba, babu takalmi a ƙafarsa, jallabiya ya saka hakan ya sa zaman da yai ya bayyana silangarinsa da ƙafafuwansa. Ta kan ce Ya Ubayd na da marteten ƙafa, mai kauri, mai faɗi. Har tana tsokalarsa idan suka yi aure sai dai ya dinga saka safa saboda ƙafarsa ba ta da kyau.

Ta zubawa doguwar ƙafarsa ido, ƙafar a mulmule take da gani zai yi laushi, yanada dogin yatsu cike da baƙin gashi zara-zara da suka ƙarawa ƙafar kyau.

"Ƙafar ne yai miki kyau ko neman wajen da zaki ɗaura min jarkar kike?"

"Allah sawwaƙa, mi zan yi da baƙin ƙafa kamar na Burgu"

Murmushi yai har saida haƙwaransa suka fito. Asiya ta yi saurin ajiye jakar ta juya.

"Ki shiga min da shi É—aki, Please"

"Ban san wanne ne É—akin ka ba"

"Kin taɓa tambaya ba a nuna miki ba?"

"Zan nema da kaina"

ÆŠakin farko da ta duba a kulle yake, na biyu ma haka, na ukun da ta shiga ta ajiye masa jarkar kusa da gadonsa. ÆŠakin ya mata kyau sosai, tun daga design zuwa furnitures da aka saka.

Ta buɗe ƙofa kenan tayi kiciɓis da Gwamna zai shigo.

"Har kin gama ganin É—akin?"

"Babu abun kallo ai"

"Na É—auka za ki tsaya muyi wanka tare ai"

Yai maganar yana kanne mata ido. Ƙirjinta ya shiga lugude. Iya zaman da za ta yi da shi ba abinda zai shiga tsakaninsu, jikinta da ruhinta duk na Ubayd ne.

Ta tsane shi, daga nesa zata gama cika baki akansa amma yana zuwa kusa da ita ƙwaƙwalwarta sai ya juya ya fara kawo mata wasu tunani daban.

Matsawa yai ta fice daga É—akin ba tare da ta iya furta komai ba.

***

Umaru Kwom na zaune a guest house É—insa tareda wasu mutane guda biyu. ÆŠaya member ne na House of Assembly, É—ayan kuma mai bashi shawara ne.

"Idan har aka tsige Saifuddeen Kachallah banida matsala da Alhaji Yamai, saboda tamkar na lashe zaɓe ne an gama"

"Kana ga za a tsige Saifuddeen Kachallah? Mutumin nan fa ba shida wani aibu, he's totally clean"

"Senator Bashari kenan. Ai idan Saifuddeen Kachallah bashida wani datti, mu zamu yaɓa masa dattin, burinmu ai duniya ta ganshi da datti ne"

"Da kamar wuya Alhaji Umaru" Senator Bashari ya faɗa. Ya cigaba bayan ya kurɓi giya "Alhaji Sani Kachallah ba zai taɓa bari a tsige ɗansa ba"

"Ko ba a tsige Saifuddeen Kachallah ba, na yi alkawarin shi da kansa sai ya yi resigning"

Mai bashi shawara yace " ban ƙi taka ba Excellency, amma koma mi zamu yi ya kamata muyi da sauri tunda sati uku masu zuwa za a yi primary election daga nan kuma ba wani lokaci garemu ba, Kamfen za a fara gadan-gadan"

"Kar ku damu komai zai zo cikin sauƙi, an riga an fara aiki akai"

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

17

Lokacin da 'yan fensho (pension) suka yi zanga-zanga jaridar Climax ce ta fitar da labari mai jan hankali akan haka. Kusan jaridar Climax ta maida hankali ne wajen nuna gazawar Gwamna Saifuddeen Kachallah. Tunda jaridar ta fitar da labarin birthday É—in 'yar Gwamna sai mutane suka maida hankalinsu wajen karanta jaridar. Kafin Umaru Kwom ya sayi jaridar Climax, jaridar ta disashe, ba kasuwa. Yanzu kam a Jahar Congo tana É—aya daga cikin jaridar da mutane ke marmarin karantawa saboda labarai masu zafi da take fitarwa.

"Har yanzu ba a san wanda ya sayi Jaridar Climax ba?" Gwamna ya tambayi COS daya kawo masa jaridar.
Chapter 34 · 0% Book details