Sashe 35
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Umaru Kwom"
"Umaru Kwom? Hmmm wannan mutumi dai ya ɗau aniyar ɓata mini suna kafin zaɓe"
COS yai shiru yana nazari, ya faɗawa Gwamna waye mai rubuta labaran nan ne ko kuma ya gayawa Kachallah. Idan ya faɗawa Gwamna zai shiga tashin hankali, amma ba abinda zai iya yi akai. Lokacin da ya gayawa Kachallah cewa Asiya ce 'yar jaridar da ta saurari maganansa kwanaki ba abinda aka mata dan haka zai yi shiru ya zubawa dukkansu biyu ido zuwa lokacin da zasu gano da kansu wanda ke ɓata musu suna a jaridar Climax.
"Ina son sanin waye É—an jaridar da ke rubutun nan"
"Angama Excellency, za a nemo koma wanene" COS ya faÉ—a yana murmushin mugunta.
***
Asiya tana zaune ta shirya kayanta tsaf tana jira Sumayya ta gama haÉ—a nata kayan su tafi.
"Ni kam Anty Allah bana so mu bar nan, a chan fa takura za mu yi"
"Idan ba za ki bini ba, kya iya wucewa hostel daga nan" Asiya ta faÉ—a tana hararanta.
Babban labari take bibiya kuma dole sai tana gidan Gwamnati za ta samu. Irin kira da saƙonnin da Nana ke tura mata ya sa tayi zargin ko yarinyar 'yar maɗigo ce. Har a whatsapp idan tayi hoto sai ta turawa Asiya wai ta gani ko tayi kyau.
Yaya Bello ne ya kaisu gidan. Asiya ta shiga gidan tana addu'ar Allah ya sa ta samu ta gama komai cikin ƙanƙanin lokaci.
Masu aikin gidan sun ganeta sai dai ganinta da kaya yasa suka tsaya cirko cirko. Babu wanda ya faÉ—a musu Amaryar Gwamna za ta zo. Gashi Gwamna da Bilkisu ba sa nan balle aje a tambayesu.
Hansa'u da ta fito ta kalli Asiya zaune a falo ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, gabanta kuma akwatuna ne guda uku. Hansa'u ta yi murmushin gefen baki dan ta hango drama idan Bilkisu ta dawo.
"Hajiya Barka da zuwa, a shiga miki da kayan ciki ne?"
"Kira min Nana" Asiya ta faÉ—a tana danna wayarta
Hansa'u ta wuce É—akin Nana da gudu.
Lokacin da ta shiga cacar baki ta samu Nana da Zunnairah na yi.
"A wani dalilin za ki ce ta dawo gidan nan idan ba soyayya ku ke ba"
" Tana da ikon zama a gidan nan saboda itama matar Daddy ce. Sannan idan ma soyayyar muke ina ruwanki. Ke mata nawa kike da shi. Yes ina sonta"
Hansa'u tayi gyaran murya, dukkansu suka juyo suna dubanta. Ta taɓa kamasu suna aikata maɗigo tun farko-farkon fara aikinta a gidan. Sun mata kashedi akan kada ta kuskura ta faɗawa kowa, sai dai ba kashedinsu ne ya sata yin shiru ba. Aikinta bai bata daman tona musu asiri ba sannan ta lura Bilkisu gafalalliyar Uwa ce. Wani lokaci tana gani suna abinda bai dace ba amma sai tayi shiru.
"Hajiya Asiya tana neman ki "
"Ina zuwa"
Nana za ta fita Zunnairah ta riƙe hannunta tace " wallahi duk ranan dana kamaki da ita sai na gayawa Daddy komai"
" ni kuma sai na faÉ—awa kowa cewa ke É—in 'yar shegiya ce, da cikin ki Mommynki ta yi aure"
Zunnairah ta kaiwa Nana duka Nana ta goce ta fice daga É—akin da gudu.
Zunnairah ta dunƙule hannu tana huci.
Tun ranan da ta saurari faɗan iyayenta abin ya taɓa mata ƙwaƙwalwa. Tana shekara shaɗaya a lokacin ta buƙaci mahaifinta ya kaita karatu ƙasar waje, lokacin yawanci 'yan ajinsu 'ya'yan manya da suka gama firamare tare iyayensu sun kaisu ƙasar waje.
"Ni zan kashewa shegiya kuɗi" amsar daya bata kenan data faɗa mata buƙatarta. Ta wuce ɗakin mahaifiyarta tana kuka. Daren ranan bayan ta kwanta ta jiyo Iyayenta na faɗa inda mahaifinta ke cewa ba lallai bane ace cikinsa ne tunda ba budurwa ya sameta ba, sannan koda suke tare ai tanada wasu samarin. Yayinda mahaifiyarta take cewa idan bai yadda Zunnairah 'yarsa bace ya je ayi gwajin DNA.
"Koma minene dai ba zan kashe mata kuɗi ba. Idan ba zata boarding school da aka sama mata ba ta haƙura da karatun"
Da wannan aka tura Zunnairah boarding school a nan kuma aka koya mata maÉ—igo...
Nana na zuwa falo ta rungume Asiya tana dariya. Ita ta mata jagora har ɗakin da ke kallon nata tace ta zauna a ɗakin idan Daddy ya dawo sai ta zaɓi ɗakin daya mata.
Bilkisu bata shigo gidan ba sai chan yammaci. Tana zuwa kuwa aka ce mata Asiya ta zo, ta haura sama kaman za ta tashi sama.
ÆŠakin Nana za ta shiga ta ga Zunnairah ta fito daga ciki.
"Ina take?"
"Wa?"
"Shegiyar da ta shigo min gidana"
Zunnairah ta nuna mata É—akin da Asiya take.
Bilkisu ta banko ƙofa ta shigo ɗakin tana huci.
Nana da Asiya da Sumayya ne ke zaune akan gado suna hira.
"Ku bamu waje"
"Mommy daga zuwanki" Nana ta faÉ—a tana tura baki.
"Ki fata ko na ci miki mutuncin, wawuya kawai"
Kafin ta gama magana ma Sumayya ta fice daga ɗakin, yayinda Nana ta fice tana buga ƙafa.
"Ehen, mi ya kawo ki?" Bilkisu ta faÉ—a bayan su Nana sun fita.
"Mi ya kawoni kuma?"
"Uban wa ya baki damar zuwa gidan nan?"
"Inaga dai kin manta cewa ni da ke matsayinmu É—aya. Yadda kike da iko da gidan nan haka nake da shi"
"Never. I am the first lady of the state, ba ki da matsayi a nan. Ki koma inda kika fito kafin na sa a maida ki ta ƙarfi"
Asiya ta miƙa mata wayarta tace "gashi, kira shi ki ce masa ba zaki bi umurninsa ba"
"Shi...shi Saifuddeen yace ki tattaro ki dawo nan?" Bilkisu tayi tambayar ta kasa gaskata hakan. Gwamna ba zai taɓa kawo Asiya ba bayan ya san ba ta so.
"Ki tattara kayanki ki koma inda kika fito"
"Idan kinga na tafi, to Excellency ne da kansa yace na bar gidan nan"
"Asiya kike ko wa. Ki fita a gidan nan kafin rayuka su ɓaci"
"Bismillah, Bilkisu Kachallah" Asiya ta faÉ—a tana dariya.
Bilkisu na fita daga É—akin ta shiga kiran Gwamna, bai É—auka ba hakan ya sake tunzurata. Lokacin daya kira bayan minti talatin ihu ta fara masa a wayar kan a wani dalilin zai cewa Asiya ta dawo gidan Gwamnati. Gwamna yace koma minene ta bari ya dawo.
Bilkisu har ƙarfe shaɗayan dare haka ta zauna zaman jiran dawowar Gwamna. Lokacin da ya shigo gida shabiyu saura a falonsa ya samu Bilkisu tana zaman jiransa.
"Ina ji, miya kawota gidana?"
Da rana bayan sun yi waya da Bilkisu, kiran Asiya yai dan ya ji dalilin dawowarta Gidan Gwamnati amma sai tace tana son zama a gidan ne, tana son sanin ya ake ji idan ana zaune a gidan gwamnati a matsayin Matar Gwamna.
"Saifuddeen ina jin ka"
"Bilkisu ke ba yarinya bace, ku ba yara bane. Ka da ku É—aga min hankali dan Allah, akwai abubuwa dayawa a kaina"
"Haka ma zaka ce...haka ma zaka ce ko"
Gwamna ya wuce É—aki ya barta a wajen.
Da sun san abinda ke damunsa yanzu da ba za su fara faÉ—a akan gida ba.
Ya kasa biyan albashin 'yan fensho da suke bin gwamnati har na wata huÉ—u, ga kumadu 'yan secretariat da malaman Sakandare duka sai dai ya biya su kaso hamsin na albashinsu wannan watan.
Lokacin da yayi wanka ya kwanta, bacci ƙaurace masa yai. Yana so koda kaɗan ne ya samu ya rintsa amma zuciyarsa tana cikin ƙunci nan da kwanaki kaɗan idan bai biya albashi ba mutane zasu fara magana. Ƙarshe dai sai daya sha maganin bacci kafin bacci ya ɗauke shi.
***
Da sassafiya kira ya shigo wayar Asiya tana dubawa taga numbar ƙasar waje . Tana ɗauka aka kira sunanta "Aseey"
"Ya Allah! C Y?, kana nan, ya kake ya jiki"
" lafiya Excellency, jiki da sauƙi"
"Gaskiya na ji daÉ—i C Y, ya hannunka"
"An samin na roba"
"Sorry ka ji"
"Ki tayani yiwa Gwamna godiya, he's a good man Wallahi, na ji daÉ—i da aka ce kin aure shi"
"Tsaya, tsaya, CY kana asibitin ma gulma kake. Waya gaya ma na auri Gwamna?"
CY ya ƙyalƙyale da dariya yace " har video ɗin dinner ɗinku na gani"
"Magulmaci, yaushe za ka dawo?"
" sunce za su sallameni nan da sati biyu haka"
"Na missing É—inka sosai"
"Rufa min asiri kar Gwamna ya sa a harbeni"
Asiya ta sa dariya.
Kaman haɗin baki suna gama waya da CY sai ga kiran Fou'ad Salisu. Kafin ta amsa kiran sai da ta shige banɗaki ta kulle ƙofa.
"Ina jinka Fou'ad"
Daga ɓangaren Fou'ad ya fara yi mata bayani "akwai wani account mai suna Sa'ad Kachallah, inaga na Gwamna ne. Lokacin da Gwamna ya bayar da takardar shaidar kuɗi da dukiyar daya mallaka kafin a rantsar da shi bai haɗa da wannan account ɗin ba, sannan account ɗin duk wata akwai miliyoyin kuɗi da ake turawa ciki. Zan ƙarisa bincike na tabbatar da gaskiyar komai"
Asiya cike da farin ciki tace " idan aka tabbatar account É—in nashi ne za a iya tsige shi kenan?"
"Za'a iya"
Asiya ta yi murmushin jin daÉ—i...
***
Sumayya tana gama lectures na ƙarfe shabiyu ta hau keke ta wuce Asibitin da Ubayd ke aiki. Ta samu yana tareda marar lafiya dan haka sai da ta jira kusan minti talatin kafin yace ta shigo.
Da suka gaisa Sumayya ta masa bayanin abinda ya kawota. Murya na rawa tace
"Yaya Ubaydullah, Ina tsoron abinda zai faru idan Gwamna ya gane Anty Asiya tana cin amanarsa"
Ubayd ya jawo kujerarsa gaba ya gyara zama da kyau yace "mi take yi?"
"Dan Allah kar ka faɗa mata cewa ni na gaya maka. Anty Asiya tana son ɓatawa Gwamna suna, da bakinta tace min sai ta sa an tsige Gwamna hankalinta zai kwanta"
Ubayd ya É—an jijjiga kai alamar ta cigaba.
"Anty Asiya ta san Nana 'yar Gwamna tana shaye-shaye sannan...sannan"
Abin yai wa Sumayya nauyin faÉ—a.
"Kar ki ji tsoro ba abinda zai faru"
"Nana 'yar lesbian ce, Anty Asiya tace zata wallafa hotonta da ta 'yaruwarta suna kiss tsirara"
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"
"Dan Allah ka hanata, Wallahi Gwamna yanada kirki ba zai taɓa jin daɗi ba idan aka buga hoton 'yarsa tsirara a jarida"
Ta ƙarisa maganar kamar za ta yi kuka.