← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 38

Sashe 13

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Asiya ba ta shirya da wuri ba dan sai takwas da rabi ma ta fita daga gida. So take MD ya tura Comrade Faisal da CY gidan Gwamna amma kash! MD ya nace sai ita ɗin zata je. Yau kan maimakon riga da wando data saba sakawa Atamfa ta saka riga da skirt da ƙaton mayafi daya kai mata gwiwa. Shikansa MD sai da yai wa Asiya kallon mamaki ganin shigar da ta yi, rabon da Asiya ta yi shigar Atamfa zuwa office har ya manta. Suna tafiya a hanya CY ya dinga tsokalarta wai tayi shigan matan aure. Asiya bata kulashi ba dan gaba ɗaya gabanta faɗuwa yakeyi, ta rasa dalilin hakan kuwa.

Koda suka isa gidan Gwamnati ƙarfe goma saura minti shabiyar. Wajen da aka ajiyesu jiyan dai nan aka sake zaunar dasu. Basufi minti goma da zuwa ba fitsari ya kama Asiya, cikin ranta sai dana sanin shayin da ta sha kafin su fito take. Ƙarshe data ga abin zai dameta ta miƙe ta tafi wajen wata mata da ke da office a corridor ɗin lobby ta tambayeta ina ne banɗaki, matar da keta tauna cingam kamar zata haɗa da harshenta tayiwa Asiya kwatance tana haɗe rai, Asiya ta wuce tana mamakin matar da fiskarta ya gama soyewa saboda bleaching.

**

"Na san ka san matsayinka a wannan Jaha. Kuma ka san baya daga cikin ayyukan ka abinda ka aikata"

"Your excellency..."

Gwamna ya ɗaga masa hannu ya cigaba "kar hakan ya ƙara faruwa Mr Lamara Damana. Matsayin Chief of Staff zai iya faɗawa hannun kowa nan gaba. Ina fata ka fahimta"

"Yes your excellency. Hakan ba zai sake faruwa ba da yardar Allah"

"Good. Now ka duba min ko kwamishinan ayyuka ya fara aikin da aka bashi"

Lokacin da COS ya fita Gwamna ya jawo takardar da ya ajiye ya kekketata sannan ya watsar. Ba zai taɓa lamunta da wannan ba. Fitar COS keda wuya Sakatare ya shigo ya sanar da Gwamna cewa 'yan jaridan jiya sun dawo.

COS na shiga office ɗinsa ya cillar da file ɗin hannunsa takardun ciki suka watse. Ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin dambe, ya kira sunan Gwamna da ƙarfi "Saifuddeen Kachallllaaaaah!"

Yana cikin huci ya tuna da wani abu nan da nan yai saurin lalubo wayarsa a aljihu ya shiga danna kira, ba aÉ—auka ana farko ba sai a kira na biyu.

"Akwai matsala Kachallah" abinda ya fara furtawa kenan da kakkausar murya. Bai bari wanda yake maganar ya ƙarisa ba ya katse shi da cewa " har Gwamna zai yi iƙirarin cireni a matsayina. Ya manta ne? Ya manta ne?"

Yai shiru yana sauraron bayani daga ɗaya ɓangaren sannnan ya ɗaura da cewa

"idan har bai san yadda akayi aka ɗaura shi akan kujera ba to kuwa lallai ƙaddarar da ta hau tsohon Gwamna za ta sameshi. Ta inda aka hau tanan fa ake sauka Kachallah... eh inaji.... sai dai abu ɗaya na sani idan har Saifuddeen ya cireni a matsayina saina gayawa duniya cewa Saifuddeen Sa'ad Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna..."

Saura kaɗan recorder da ke hannun Asiya ta faɗo saboda firgita da tayi. Tayi saurin toshe bakinta saboda kar mutumin da take naɗan maganarsa ya jiyo nishinta. Ta fito daga banɗaki kenan za ta koma inda aka ajiyesu ta hango Chief Of Staff ya zo ya shige wani lungu a bircike. Curiosity nata na 'yar jarida ya sa ta bi bayansa. Wani office taga ya shige hakan ya sa ta bi bayansa da zimmar ko za ta iya gano dalilin fushinsa tunda hanyar da ta ga ya fito tanan ne office ɗin Gwamna, koma minene ya ɓata masa rai yanada nasaba da Gwamna ɗin.

Ihun da ta jiyo COS yayi yana kiran sunan Gwamna yasa ta laɓe ta fidda ƙaramar recorder ɗinta ta fara naɗan maganar sa.

Ganin yayi shiru yana sauraron bayanin da ake masa ya sa tayi saurin jan jiki ta bar bakin ƙofar.

Ba ta ji ƙarshen maganar sa ba.

"Eh...ina sane amma... shikenan zan kiyaye sai dai gara a nuna masa cewa mune muka buÉ—a masa hanya har ya samu ya hau kujeran, idan aka cigaba da ninke shi a baibai zai yi abinda zai jawo masa dana sani... to shikenan zamu haÉ—u idan na tashi a office"

Da ƙyar Asiya ta iya komawa wajensu CY dan a tsorace take, abinda ta jiyo ya girgizata matuƙa yayinda tsanar Gwamna Saifuddeen ya dira a zuciyarta, dama ya aka ƙare balle kuma...

Ta samu CY na faman saita camera, shi da Sunusi suna taÉ—i shiyasa hankalinsu bai kai gareta sun lura da chanjawar yanayinta ba.

Bayan minti biyar sai ga Gwamna ya iso fiskarsa ɗauke da annuri. Kallon tsana Asiya ta bishi da shi tana ji a ranta kamar ta shaƙeshi ya mutu kawai.

Maimakon jiya da za a naÉ—i shirin sannan a editting na shi kafin a É—aura a tasharsu yau kam live za a saka shirin a gidan talibijin na su.

Yau kam ba kamar jiya ba babu tsoro ko fargaba a tattare da Asiya, cike da nitsuwa ta fara gabatar da shirin. Tambayoyin da aka amince ta masa su takeyi sai da aka kai tsakiyar shirin sannan ta sako zancen tsohon Gwamna wanda ba Gwamna kaÉ—ai ba hatta CY sai da ya sha jinin jikinsa da tambayar

"Gwamna Saifuddeen duba da yadda mutuwar tsohon Gwamna ya zo bagtatan ko za ka iya sanar damu yadda mutuwarsa ta zo maka?" Tambayar offscript ne baya cikin jerin tambayoyin da akace za a masa shiyasa ya ɗan ji abin banbaraƙwai amma ya dake ya amsa da cewa.

"Kowanni halitta dake doron ƙasa sai ya ɗanɗani mutuwa. Dukkanmu lokaci muke jira. Haƙiƙa mutuwar tsohon Gwamna ta girgizani matuƙa saboda yadda ya zo mana lokaci guda..."

"Excellency baka ganin ya kamata a duba mutuwar tasa kodai akwai lauje cikin naÉ—i duba da cewa Gwamna nada 'yan adawa dayawa"

Ba dan shirin kai tsaye aka ɗaura shi ba da CY tuni ya katse ɗaukan shirin saboda yadda Asiya take chanja alaƙar shirin nasu.

Gwamna ya kalleta cikin zargi amma bai bari hakan ya bayyana a fiskarsa ba yace " Malama Asya mutuwa koda ciwo ko babu ciwo sai anyita. Likitoci sun tabbatar da cewa hawan jini ne yai ajalin tsohon Gwamna Allah ya jiƙan rai"

"Ya yanayin alaƙarka da shi kafin rasuwarsa?"

"Munyi zama na amana da shi, Allah ya gafarta masa kurarensa da ma namu gaba É—aya"

"Amin"

"Tambayata ta gaba ko miyasa Gwamna ya zaɓi Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa duba da cewa ana zarginsa da cin hanci da rashawa har ma shekarun baya hukumar EFCC sun kama shi?"

Kafin Gwamna ya bada amsa daga chan ma'aikatarsu aka katse shirin aka saka talle saboda a samu daman katse ɓaranɓaramar da Asiya ke yi.

"Jesus! Aseey lafiyanki kuwa?"

CY ya faɗa da ɗan ƙarfi, kafin ta bashi amsa MD ya kirata tana ɗauka ya shiga surfa mata masifa kaman zai zo wajen ya bindigeta. Tana ajiye wayar tareda sauke ajiyar zuciya ta haɗa ido da Gwamna. Duk da tsanar da take masa hakan bai hana tasirin kallon sa gareta ba.

"Yaudara na ɗaya daga cikin abubuwan da na ke ƙyama. Miss Asya na yarda da wannan interview ne saboda babu maganar siyasa a cikinta, kar ki manta da wannan"

A yadda ransa ya sosu da abinda tayi niyyarsa ya miƙe ya bar wajen saidai idan har yai haka ya sani daga lokacin 'yan jarida zasu murɗa labarin da cewa Gwamna ya ƙi amsa tambaya saboda bashi da gaskiya. Ya sani Alhaji Bala Yamai ba shine candidate ɗin daya so ya zama mataimakinsa ba sai dai kamar yadda Alhaji sani ke yawan faɗa masa cewa a siyasa dolene ka yi abinda bature ke kira compromise. Ba zai manta lokacin da Alhajin ya kirashi ya ce masa mataimakinsa shine Alhaji Yamai ba. Ya faɗi maganar kamar bashi da zaɓi, kamar ba shine mai ikon naɗa duk wanda yakeso ba.

"Alhaji Yamai yanada record na rashawa, Baba" ya faÉ—a da murya mai sanyi.

"Ka zo gida muyi magana" Alhaji Sani ya faÉ—a. Koda ya sameshi a gida bayani ya masa wanda hakan ya birkita shi har sai da asthma É—insa ta fara barazanar tashi.

Ya sani tun kafin ya kawo wannan matsayi Alhaji Sani Kachallah yana ɗaya daga cikin wanda suke riƙe ko yace suke juya jahar Congo. Tun zamanin mulkin soja ake damawa da shi har aka dawo mulkin farar hula.

"Mutane huɗu ne keda alhakin zaɓan Gwamna da Mataimakinsa. Wannan karan ɓangarena ne da Gwamna, ɓangaren Mataimakinsa yana hannun ɓangaren Yellow Group kuma sun zaɓi Alhaji Yamai. Kar ka damu, Alhaji Yamai hoto zai zama kawai" yadda Alhaji Sanin ya faɗi kalmar hoto sai ya tuna da yadda shima watannin baya yake kamar hoto a matsayinsa na mataimakin Gwamna. Ya so yaja da hakan amma bai samu ƙwarin gwiwar yi ba. Tun lokacin da Alhaji Sani ya gabatar da shi a jam'iyyarsu ya sanar dashi ma'anar tutar Jahar Congo. Kalar Baƙi da ta fi yawa a jikin tutar ita ke ɗauke da kaso 45% wanda Yallaɓai ke shugabanta yayinda kalar Blue ke ɗaukan 25%, kalar Red ta ɗauki 18% sai Yellow 12%.

kalar blue ta Alhaji Sani Kachallah ne hakan na nufin da shi ake damawa a Gwamnati, hakan na nufin Saifuddeen ba shi da ikon yin komai sai da yardar sa.

Yanzu da aka dawo daga tallen da aka saka wanda ta kai kusan minti takwas bai ɓata lokaci ba ya amsa tambayar Asiya da cewa ya zaɓi Alhaji Bala Yamai ne a matsayin mataimakin Gwamna saboda an riga an wanke sunansa daga laifin rashawa da ake tuhumarsa da shi shekarun baya, ya haɗa da cewa Alhaji Yamai yanada experience a harkar siyasa fiye da shi shiyasa ya zaɓe shi. Lokacin da ya gama bayanin lokacin da aka ɗibarwa shirin ya ƙare dan haka Asiya bata sake wata tambayar ba ta ƙarƙare shirin.

CY na cewa Cut Gwamna ya miƙe ya tafi yayinda muƙarrabensa suka bi bayansa cikin sauri.

"Aseey kin fuck up Wallahi" CY ya faɗa yana girgiza kai yayinda Sunusi yake jimamin yanzu ɗan alkhairin da za a basu ya wuce tunda gashi ran Gwamna a ɓace ya bar wajen su.
Chapter 13 · 0% Book details