← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 38

Sashe 29

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Asiya zata zauna a Kachallah House" Bilkisu ta ƙatse shi tun kafin ya dasa aya.

"Na riga nayi magana da Hajiya Umma akan za'a..."

"Matarka zata zauna a Kachallah house. Idan kuma chan bai isheta ba ka iya siya mata wani gidan daban amma wancan gidan Bilkisu ne" tana gama maganar ta fice masa daga É—aki.

Dunƙule hannunsa yai yana huci. A waje shi Gwamna ne, a cikin gida kuma shi mijin Bilkisu ne. Ba yau ta fara fita daga ɗaki idan suna tsaka da magana mai mahimmanci ba amma yau abin ya taɓa shi sosai.

***

*Takawarki lafiya Asiya Matar Gwamna.... Ayyiriri yiriri yiriri*

Guɗa da kirari ke tashi ta ko'ina, masu watsa filawowi nayi, masu yawo da turaren wuta nayi, haka aka shigo da Amarya Asiya ɓangaren Hajiya Dadda kakar Gwamna. Hajiya Dadda na zaune da wasu manyan mata aka zaunar da Asiya gabanta, Asiya na sanye da alkyabba ruwan Gwal ko fiskanta ba a gani saboda hular alkyabban ya rufe. Dadda ta riƙo hannun Asiya ta dinga zuba mata addu'a. Bayan an gama da wajen Hajiya Dadda aka kai Asiya wajen Hajiya Aisha mahaifiyar Bilkisu.

Hajiya Umma ce ke gaba akan komai, tunda Gwamna ya kirata ya gaya mata cewa a Kachallah House Asiya zata zauna ta shiga faÉ—a, wai sam ba zai yiwu ba. Bilkisu ba zata ja musu magana ba. Yadda aka riga aka tsara hakan za ayi. Za a fara kawo Asiya Kachallah House tayi kwana É—aya, washegari a wuce da ita gidan Saifuddeen.

Duk cikin ƙannen Alhaji Sani, Hajiya Umma ce macen da ko shi Alhaji Sanin ba ƙaramin shakkanta yake ba. Tanada faɗa sosai kuma bata ragewa kowa.

Bai san ya suka ƙare da Bilkisu ba, da dare daya shigo gida Bilkisu ta sameshi akan cewa ya sani bata yadda a saka Asiya a sama ba. Indai wannan ne da sauƙi dan dama a ƙasan aka shiryawa Asiya kayanta.

Bayan sun bar sashen Hajiya Aisha sai aka wuce da Asiya ɓangaren Saifuddeen lokacin yana saurayi. Ƙaramin falo ne da ɗaki a ciki haɗe da banɗaki.

Anata shigowa gaishe da Amarya sai ƙarfe shaɗaya da rabi Hajiya Umma ta kori mutane aka bar Asiya da ƙanwarta Sumayya, Faty da kuma ƙawarta Queen Bee.

Gobe da safe za'ayi wuni da yamma kuma ayi dinner wanda Bilkisu Kachallah ta shirya.

Bayan an watse ne Asiya ta samu ta cire kaya ta shiga banÉ—aki dake cikin É—akin ta fara wanka. Kuka ta saka lokacin da ruwan shower ya fara sauka mata. Kukan da bata yi ba lokacin da za'a kawota, kukan da bata yi ba lokacin da aka kaita gaban Abba yai mata nasiha.

" an ɗauraaaa, Anty Asiya kin zama matar Gwamna" maganan Sumayya kenan tana tsaye dai dai ƙofar ɗakin Umma.

Live aka nuna ɗaurin auren a gidajen talabijin. Hakan ya sa 'yan biki suka cika falon Abba da ɗakin Inna Yaha sai kuma masu kallo a waya. Umma kam dama babu TV a ɗakinta shiyasa Asiya ta samu salama, ta kwanta tana ayyana abubuwa da dama a ranta. Su uku ne a ɗakin sanda Sumayya ta leƙo tana faɗa mata munanan kalamai. Umma da ba jin mi ta faɗa tayi ba ta cigaba da ninke kaya. Wata Goggon Asiyan da ke kwance saboda ciwon kai ta miƙe zaune tana doka kabbara lokacin da taji abinda Sumayya ta faɗa.

"Anty kinga fiskar Ale kuwa ? da aka nunoshi kaman mai tallen Makilin..."

"bar nan Sumayya!"

Sumayya ta sake labule ta sa gudu.

Buga ƙofar da Queen Bee ke yi ya sa ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

"Governor's wife, fata zaki chanja a banÉ—akin ne wai? Muma zamu watsa ruwan fa"

Bata kulata ba sai kawai ta matsi shower gel ta fara shafawa a dogon gashinta wanda ruwa data bari ya zuba mata akai ya sa ruwan mai ya mamaye ilahirin jikinta. Ba ƙaramin gyara gashin ya sha ba a hannun Queen Bee saboda harkanta kenan.

Bayan ta gama wanke kan ya dena fitar da mai sannan ta yi wanka ta É—aura towel ta fito.

"Queen Bee akwai hand dryer a kayanki?"

"Yanzu wanke kai kikayi tun Ango bai gani ba"

Queen Bee ta faɗa tana taɓe baki.

"Kin zo da shi, e ko a'a?" Tayi maganar da ɗan ƙarfi dan ruwan kanta ya fara sauka ƙasa saboda bata goge kan ba.

"Barin É—auko miki"

Faty na zaune bakin gado tana kallon ikon Allah. Babu walwala ko kaɗan tattare da Asiya irin na Amaren nan. Lokacin da aka kira mai hoto cikin gida ana ɗaukan hotuna ko sau ɗaya bata murmusa ba, ƙarshe ma cewa tayi kanta na ciwo ba zata iya tsayuwa ba.

Anya Asiya ba zata yi wani mugun abu ba kuwa wajen dinner ɗin da za ayi? Ko kuma ma idan an kaita tayi ƙoƙarin illata Gwamna. Tayi saurin kauda tunanin a ranta da cewa Asiya na da ilimi ba zata yi wannan haukan ba.

Asiya ta kunna hand dryer ta fara busar da gashinta, Faty ta miƙe daga inda take kishingiɗe ta ce " kawo na miki"

Lokacin da Queen Bee ta fito daga banɗaki suka rutsa Asiya da ke shirin bacci da nasiha. Faty a matsayinta na ƙanwar Ubayd kuma ƙawa ga Asiya tunda duk cikin 'ya'yan Inna Yaha itace suka shaƙu ƙwarai, shiyasa ma aka saka aurensu lokaci guda ita da Asiya kafin lamari ya chanja. Faty ta bata shawaran ta manta da Ubayd ta rungumi mijin da Allah ya bata.

Queen Bee ma a matsayinta na babbar ƙawa wacce suka yi Jami'a tare, sannan suka haɗa business tare, ta bawa Asiya shawaran haƙuri da hukuncin Allah.

Asiya jinsu kawai take amma ba abinda ta É—auka cikin maganganunsu. Tun kafin Queen Bee ta ida maganarta Asiya tace ta gaji, bacci za ta yi.

Asiya ta samu gefen Sumayya da ta jima da bacci ta kwanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.

***

Zurmemiyar wuƙa Asiya ta ɗauko a kitchen ta wuce ɗakin Gwamna da shi. Yana tsaye sanye da farar jallabiya yana waya ya bata baya, a hankali ta ƙariso ta zurma masa wuƙa a gefen cikinsa.

Gwamna ya saki ƙara, ya juyo a hankali yai taga-taga kamar zai faɗi ƙasa Asiya ta riƙo shi "I hate you Saifuddeen Kachallah" ta faɗa tareda ƙara danna wuƙar ciki sosai.

BuÉ—e idon da Asiya tayi ta hango ceiling É—in É—akin. Dogon numfashi ta ja kafin ta ce a ranta " ba zan kashe ka ba sai dai..."

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

14

***

Tunda su Asiya suka ci abinci suka koma sashen Dadda. Daga safe zuwa yammaci baƙi ne ke ta shigowa ganin Amarya. Matan manya da kuma manyan manyan Mata da su kayi suna a ƙasar. Wasu kallon ƙwaƙwaf ne ya kawosu saboda a samu latest gist da za a tattauna idan an haɗe a wajen shaƙatawa, wasu kuwa sun zo ganin Asiya Shahidan da ake kururutawa ne saboda ba su santa a Talabijin ba. Wasu kuma sun zo ne domin samun gindi a wajen Asiya dan basa shiri da Bilkisu Kachallah.

Asiya bata bada fiskar da zai sa a gane tana cikin matsala ba. Ko Faty da Queen Bee sun yi mamakin yadda ta sake tana dariya cikin mutane kamar auren soyayya akayi.

Kusan ƙarfe biyar da rabi na yamma Anty Saudah ƙanwar Bilkisu ta kawo musu wata jaka tace kayan da Amarya zata saka ne a wajen dinner. Basu waiwayi kayan ba saboda suna cikin jama'a.

Ƙarfe bakwai da minti Arba'in bayan Asiya ta idar da sallar Isha ta shiga banɗaki ta watsa ruwa. Suna ɓangaren da suka kwana jiya, su huɗu ne a ɗakin a chan falo kuma ƙawayen Asiya na makaranta ne da abokanan aikinta da suka samu pass ake wa kwalliya. Queen Bee ce ta karɓo pass ɗin dan haka Asiya bata san iya mutanenta da zasu zo wajen dinner ba.

Tunda Queen Bee ta fito da kaya Asiya ke girgiza kai, amma bata ƙi ta su Faty ba da suka ce ta dai gwada ta gani. Abu ɗaya ta sa aranta shine ko ta sha giyan wake ba za ta sa wannan kayan ta fita waje ba. Gown ɗin yayi ba ƙarya, ya amshi jikinta, duk wani tudu na jikinta ya fito sosai, sai dai rigar offshoulder ce rabin ƙirjinta a waje yake sai net da aka rufe wajen da shi wanda ko makaho ya shafa ya san ba abinda net ɗin ya tare. Cikinta ma net ɗin aka saka saboda an fafe lace ɗin wajen ne aka saka net. Ɗinkin yayi kamar bra ta saka da skirt sai aka rufe sauran wajen da ke bayyane da net.

"Inaga za mu nemi shawl da zai je da kayan kawai sai..."

"Baki da hankali Bahijja" ta kira sunan Queen Bee na asali.

"Gaskiya dai wannan kayan sai a hankali" Faty ta faÉ—a tana girgiza kai, sai yanzu da Asiya ta sa kayan ta gano akwai matsala.

"Bilkisu Kachallah ta riga ta rubuta headline da zai fito gobe a labarai idan na sa kayan nan. Beside, ni ba mahaukaciya bace na san darajan gidan dana fito"

"Anty dan Allah barin É—auke ki a hoto, wallahi kin yi kyau" Sumayya ce da wannan maganar.

"Ban yadda ba... ki bari" sai kawai ta haƙura ta tsaya saboda Sumayyan ta riga ta fara ɗaukanta hoto.

ÆŠaya kayan dake cikin jakar ma babu kanta, atampa ce da aka yiwa fitanniyar É—inki. Ko gwadawa batayi ba ta tura gefe.

Ba abinda ya rage sai dai su saka abinda suke da shi.

"Ko na yiwa Hajiya Umma magana ne? tunda dama tace za a kawo mana kaya na ce an riga an kawo" Queen Bee ta faÉ—a tana kallon Asiya da ke zaune a gefen gado daga ita sai zani.

"Akwai wani gown a jakar da nace ki tahomin da shi Sumy, É—auko min"
Chapter 29 · 0% Book details