← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ubayd ya ja dogon numfashi yace " kar ki damu zan kirata"

Sai da yai sallar Azahar kafin ya kira numbar Asiya har yanzu sunan da yai saving da shi ne bai chanja ba wato *Mine* yanzu kam dole ya chanja numbar ko dan gudun zargi.

Asiya za ta shiga wanka ta ji wayarta na ringing. Tunaninta Mr Bassey ne shiyasa ta koma ta É—au wayar dan ta gaya masa nan da anjima kaÉ—an za ta tura masa labarin da ta rubuta. Ta gama rubutun editting É—insa kawai za ta yi.

Tana duba wayar ta ga sunan Ubayd.

"Ya Ubayd kuma?" Ta furta a fili, sai da wayar ya kusa yankewa ta É—auka tareda sauke ajiyar zuciya.

"Asiya ke ce kike rubutu a jaridar Climax ko?" Ya katse shirun na su

"Ya Ubayd dan Allah kada kace na dena"

"Ai ban isa na hanaki abinda kika yi niyya ba. Ina ce taurin kanki ne ya zamo mafarin komai"

"Ya Ubayd..."

"Yanzu ba za ki karɓi hukuncin Allah a rayuwarki ba. Yanzu Asiya har zuciyarki ya bushe za ki iya nuna hoton tsiraicin yara ƙanana a jarida"

"Za a rufe inda bai kamata ya fito ba, ina dai so a gansu suna aikata maÉ—igo ne"

"Idan har haka kika zamo Asiya, Alhamdulillah da ban aure ki ba. Asiya kin san ya yaran nan za su ƙare rayuwarsu idan kika tona musu asiri haka. Kina kiran Gwamna Azzalumi amma inaga sunan daya kamata ki fara kiran kan ki kenan"

"Kar ka zageni Ubayd. Ni miye Gwamna da matarsa ba su min ba, har yau akwai mutane dayawa da suke min kallon karuwa"

"Asiya kina da ilimi, da da yanzu ba É—aya bane. Yanzu Gwamna mijin kine"

"Mijin da bana so ba, bana son shi Ya Ubayd, ba zan taɓa son shi ba"

"Idan kika wallafa hotunan tsiraicin yaran nan bana tunanin Allah zai yafe miki Asiya"

Daga haka ya kashe wayar.

Asiya ta fashe da kuka. Da ta yi mai isarta ta shiga banɗaki ta fara wanka. Komai ya zo mata da sauƙi sai gashi Ubayd yana so ya dagula mata lissafi.

Kwananta huÉ—u a gidan ta kama Nana da Zunnairah akan gado, ba tareda sun ankara da ita a É—akin ba ta É—auke su hoto ta fita.

Ta zo tana editing hoton a laptop Sumayya ta gani hankalinta ya tashi. Asiya tace mata maganin 'yan iska za ta yi.

Da farko labari za ta rubuta akan hoton da Mr Bassey ya turo mata, wani hoton Nana ce a wajen party tana shan shisha. Hoton bai jima sosai ba dan ba zai fi wata É—aya da aka É—auka ba. Ko a ina ya samo hoton oho ita dai damuwarta ta yi rubutu ta aibata Gwamna sai kuma kwatsam ta samu hoton da ya fi wancan armashi.

Tana fitowa daga banɗaki ɗaure da towel ta dafe ƙirji saboda ganin Gwamna da tayi riƙe da wayarta.

Idonsa ya kaÉ—a yayi ja sai ta fara tunanin kodai ya ga hoton Nana ne, to amma kuma wayarta akwai password.

Ringing wayar ta fara yi hakan ya sa ya miƙa mata wayar. Jiki a sanyaye ta ƙariso ta karɓi wayan a hannunsa. *Ubayd Luv* ta gani ƙarara a fiskar wayar, ta ɗaga ido ta kalli Gwamna wanda shima kallonta yake yi.

"Akwai taron da zamuje gobe da ƙarfe goma na safe" daga haka ya fice daga ɗakin.

"Ashe dai bai gani ba" ta faÉ—a a hankali.

Ba ta ɗau wayar ba sai da ta je ta kulle ƙofa kar wani ya sake shigo mata ɗaki bagtatan.

Kiran numbar Ubayd tayi bayan ta zauna a gefen gado.

Lokacin da ta ɗauka roƙonta ya fara yi akan dan Allah kada ta wallafa hotunan nan. Yadda ya dinga yi mata nasiha yasa dole ta haƙura da abinda tayi niyya, tace masa ba zata wallafa hoton ba.

Da suka gama wayar ta saka kaya ta jawo laptop É—inta ta goge rubutun da tayi da farko ta fara rubuta wani sabo akan hoton da Mr Bassey ya turo mata.

***

Washegari aka fitar da labari mai taken *'yar Gwamna tana shaye-shaye* rubutun ya soki Gwamnatin Saifuddeen Kachallah inda aka bayyana cewa yadda Gwamna bai iya kula da tarbiyar 'yarsa ba haka zalika ba zai iya kula da haƙƙin talakawa ba. Duk da jaridar bata fito ta bayyana cewa Nana Kachallah 'yar maɗigo bace amma ta yi ishara da hakan ta hanyar cewa akwai alamun Nana Kachallah za ta iya zama 'yar maɗigo saboda illar shaye-shaye.

Gwamna bai samu ganin jaridar da aka wallafa ba sai da ya dawo daga taron buɗe wani Asibiti da suka je a wata ƙaramar hukuma shi da matansa biyu.

Lokacin da ya ga hoton 'yarsa tana zuƙan shisha sai dayai ƙwalla Allah ya taimaka ma babu kowa a office ɗin nasa. Gaba ɗaya komai ya fice masa a kai, tunda aka fitar da hoton birthday ɗinta ya ja mata kunne akan irin shigar da take yi sannan ya hanata fita idan ba makaranta ko gidan kakanninta ba.

Amma a haka bai tsira ba, mulkin gaba É—aya ya ishe shi. Lokacin da yake koyarwa yanada lokacin iyalinsa sosai amma tunda ya shiga siyasa yanayin zama da iyalinsa ya ja baya, musamman yanzu da yake kan kujerar Gwamna.

Kiran Direban yaransa yai yace ya je ya É—auko Nana a makaranta ya kaita Kachallah house.

Shima É—in bayan ya samu zuciyarsa ta É—anyi sanyi Kachallah House É—in ya wuce.

Yana zuwa ya samu Dadda na yi mata faÉ—a, suma sun ga jaridar.

Dadda shigewa ɗakinta tayi ta basu waje. Nana da idonta ya ciko da hawaye ta shiga rantse-rantsen sau ɗaya ne kuma a wajen party aka tirsasata saboda ƙaryar da Bilkisu tace tayi kenan.

"Hoton bai yi kama da yarinyar da aka tursasa ba, ya fi kama da yarinyar da ta ƙware wajen shan shisha dama wasu abubuwan"

"Daddy I swear..."

"Ki gaya min gaskiya yanzu, ko kuma na sa a binciki jininki a duba min traces na kayan maye. Idan aka samu Nana ba za ki so ki sake kirana mahaifinki ba"

Nana ta tsorata da yanayinsa, yadda ya É—au fushi ba abinda ba zai iya yi ba.

Ƙarshe da taga gaskiyar ce kawai zata fishsheta sai ta sanar da shi komai. Zunnairah ce ta koya mata shan syrup da shisha.

"Wani mummunan abun ta kuma koya miki?"

"Babu. Allah babu" Nana ta yi saurin faÉ—a tana fashewa da kuka.

" Khadijah ba zan bar nan ba sai kin gaya min duk abinda Zunnairah ta koya miki. Idan kika min ƙarya zan gane dan nasa a bincika mini CCTV camera da ke cikin gida" duk da sai yanzu yake danasanin ƙin yarda a saka masa CCTV a gida da yai.

Tsoro ya É—arsu a zuciyar Nana, kenan duk abinda suke da Zunnairah Daddy zai gani. Idan haka ne ta kaÉ—e.

"Ina jin ki Khadijah"

"Daddy ka yafe min, wallahi ba laifina bane. Airah ce, Airah ce ta kemin wasu abubuwa tun bana so har na zo na fara so. I swear Daddy na dena, cewa tayi zata faÉ—a maka shiyasa na sake yi"

Gwamna ya jingina kansa da kujera yana faÉ—in "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

18

Asiya ce ta fara shiga falon. Ta samu Gwamna yana zaune yayi tagumi. Ya mata tsufa, idonsa ya faɗa, ƙasan idonsa ya yi baƙi, ga furfura kaɗan-kaɗan a jikin gemunsa. Asiya ta zuba masa ido ba tareda tace komai ba.

Minti uku sai ga Bilkisu ta shigo É—ankwali a hannu.

"Saifuddeen koma wanene ya rubuta labarin nan sai na sa an nemoshi an hukunta shi. In fact sai nayi kaca-kaca da jaridar Climax"

"Nana tana zama a gidan nan tareda ke amma baki san tana shaye-shaye ba"

"Kar ka kawo min wannan Saifuddeen, ka san ina ƙoƙari akan yarana, especially Nana. Zunnairah ce ta koya mata. Na riga na turata wajen uwarta kafin ta ɓata min 'ya"

Ta zauna gefensa kafin ta cigaba da magana

"Saifuddeen kai ne Gwamna, ya kamata ka ƙwace lasisin gidan jaridar Climax. Ta ya za su ce Nana zata zama 'yar lesbian"

"Saboda da gaske ne" Gwamna ya furta a hankali

Bilkisu ta zaro ido.

"Da gaske kuma? Mi kake nufi?"

"Nana ta faÉ—a min komai. Ita da Zunnairah suna aikata maÉ—igo a gidan nan kuma babu wanda ya sani cikinmu, saboda mun gaza, mun gaza Bilkisu. Ba jaridar Climax zamu bincika ba, kanmu za mu bincika a matsayinmu na iyaye"

Jikin Bilkisu yai sanyi, ta fara yin fifita da É—ankwalin hannunta duk da kuwa sanyin AC ya ratsa falon.

Kaman wanda aka tsikari Bilkisu haka ta tashi ta fice daga falon.

"Tsanar da kika min har ta kai haka"

Asiya ta zaro ido dan a tunaninta ya gano cewa ita ta rubuta labarin ne, sai kuma ta ji ya ƙara da cewa.

"Na karɓi wayan Nana, na ga irin saƙonni data dinga tura miki. Lokacin da tace tana sonki miyasa baki faɗa min ba? A matsayina na Uba ba kya ganin ya dace na san 'yata tana yiwa wata mace 'yaruwarta kallon da bai dace ba"

In dai ya ga chats ɗinsu to babu halin ta masa ƙarya dan a ƙasan wajen da Nana ta ce mata "I love you" tambayarta tayi wani irin so, Nana ta amsa da cewa " ina son lips ɗinki, ƙirjinki, bayanki, kai komai na halittar ki"

"Ko a tunaninki yarinyar shekara shabiyar ya kamata ta dinga faÉ—in irin wannan maganganu?"

Idan ya cigaba da bin diddigi zai iya alaƙantata da jaridar Climax kuma ba yanzu take so ya sani ba. Ta yi saurin cewa " ni ban ɗauki wannan komai ba tunda na ga kamar tarbiyyan gidan kenan. Kana gani 'ya'yanka na yin shiga da bai dace ba a cikin gidan nan bayan akwai ma'aikata maza, baka taɓa musu magana ba, ban taɓa gani suna karatun addini ba, bana ma tunanin suna zuwa Islamiyya. Rayuwar da kuka ɗaurasu irin ta turawa ce, sannan a wajen mahaifiyarsu ni jikar maiƙusumbi ce, a wajenka kuma ni hajar Kamfen ce. Taya zan ƙalubalanci abinda 'yarka ke faɗa mini, ƙila ba matsala bane a wajenku"
Chapter 36 · 0% Book details