Sashe 7
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ke ce ki ka ce na kawo shi kwili-kwili (quickly-quickly) kuma na ji Hajiya na kira shiyasa na kawo shi haka nan"
"Dalla je ki ɓare ƙwan ki kawo" Nana ta faɗa da tsawa.
Hansa'u ta É—auke kwanon ta koma kitchen da sauri.
Hajiya Bilkisu da ta fito ba ta wuce ko'ina ba sai Kachallah House. Da ta shiga gidan ba ta wuce sashen kowa ba sai sashen mahaifinsu wanda ya ke gefe da asalin cikin gidan, a nan ya ke karɓan baƙin sa a nan kuma ya ke duk wasu harkokin sa. Sashen ya ƙunshi falo guda ɗaya da dining room sai manyan ɗakuna guda huɗu. Ba kowane ya sani ba amma ita Bilkisu ta san akwai falon sirri a gidan wanda Mahaifinsu ke karɓan baƙi na musamman inda ake yin meeting na tsakar dare a ciki.
Shekarunta shabiyar lokacin da ta gano ɗakin, ta je duba wani littafi a library ɗinsa ne hannunta ya danna wani switch a jikin bango sai gashi carpet ɗin wajen ya ɗage. Ba tareda tsoro ba ta leƙa wajen daya buɗe ɗin sai taga matakala ce a wajen. Ta sa ƙafa ta fara taka matakalar har ta nitse ciki dan falon underground ne. Ta san turawa na yin ɗaki ko basement a cikin ƙasa amma ba ta taɓa tunanin sashen mahaifin na su na da irin wannan ba. Falo ne Babba da ya sha kayan alatu fiye da ɗaya falon sai ɗakuna biyu wanda tayi-tayi ya buɗu ya ƙi buɗuwa shiyasa ma ta haƙura ta fito ba tareda ta ga abinda ke ciki ba.
Ta ci sa'a Baban na su na nan dan lokacin ne ma ya ke ƙoƙarin karyawa ga tulin abinci kala-kala da aka ajiye ma sa wanda aƙalla mutum shida za su iya cin abincin su ƙoshi sarai.
"Bilkisu" ya kira sunanta da mamaki.
Ya duba agogon hannunsa ya ga ƙarfe bakwai da minti arba'in da bakwai.
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya Baba"
Bayan ya tambayi lafiyar mijinta da 'ya'yanta sannan ya tambayi mi ke tafe da ita da sassafen nan dan yasan haka kawai Bilkisu ba za ta nemeshi ba.
"Saifu ne zai miki kishiya?"
"Baba idan kishiya ce ai da sauƙi. Baba tambaya na zo yi"
Alhaji Sani Kachallah ya suɗe romon kan rago da ke shirin gangarowa zuwa gwiwar hannunsa. Wani lokaci idan Mahaifinsu yai wani abun kamar wani faƙiri wanda ba shi da gata ko kaɗan. Yanzu miye na suɗe hannu?. Ta yi saurin kauda wannan tunanin a ranta ta maida hankalinta zuwa abunda ya kawota.
"Baba yaushe Saifuddeen zai zama Gwamna?"
Alhaji Kachallah ya saka bredi ya dangwali romo zai kai baki ya ji maganar Bilkisu ta ma sa dirar bazata.
"Wace tambaya ce kuma wannan?"
"Baba dan Allah ka amsa min tambayata"
Alhaji Kachallah ya kalli idon 'yarsa da kyau ko zai gano wani abu amma bai karanci komai a fiskarta ba sai tsananin ɓacin rai, ya ce " idan Saminu Bacchi ya ƙarisa tenure ɗin sa guda biyu Jaha za ta koma ta Saifu dan shi za mu tsayar a zaɓe na gaba"
"A taƙaice kusan shekaru biyar kenan?"
Alhaji Kachallah ya ture kwanon gaban sa gefe ya É—aura hannu akan table yana zubawa Bilkisu ido.
"Babu yadda za'ayi Saifuddeen ya zama Gwamna kafin lokacin?. Baba ku ne da gwamnati, ku kuke juya jahar nan, mi zai hana ka É—aura Saifuddeen a kujerar Gwamna, shekaru biyar ma su zuwa sun yi nisa sosai"
"Bilkisu!"
"Baba break the rules, boycott the protocols make Saifuddeen the governor and..."
Idan da bai yi tunanin hakan ba to yanzu Bilkisu ta ankarar da shi. Mr Paul da ya ke son haɗa ma sa manaƙisa a wajen Yallaɓai dole ne ya nuna ma sa cewa kafin mutum ya ga biri to biri ya gan shi.
Bayan fitar Bilkisu daga falon, Alhaji Kachallah ya faɗa kogin tunani. Ta ina zai fara? Akwai gaskiya a hasashen Bilkisu dole ne ya san yadda zai yi ya shawo kan matsalar tun kafin lokaci ya ƙure a juye ma sa baya.
***
"Miyake faruwa naga kwana biyu ba kya fita"
SSK yai maganar yana zama gefen gadon Bilkisu tareda kissing goshinta.
"Ba na jin fitan ne kawai. Ina buƙatar hutu ne ma"
"Nima ina buƙatar hutun nan Allah. Inaga tunda Gwamna ya dawo why not mu je UK hutu ko da na sati biyu ne?"
"Its a good idea gaskiya. Muna buƙatan hutun nan sosai" ta yi maganar tana murmushi.
SSK bai jima da fita daga É—akinta ba wayarta ya hau ruri. Madam Bintu ta gani a jikin screen É—in hakan ya sa ta faÉ—aÉ—a murmushinta. Ta yi saurin É—aukan kiran tana faÉ—in " mutanen Turkiyya kin shigo kenan"
Daga ɓangaren Madam Bintu ta ce "na shigo jiya da dare zan shigo wajen ki anjima"
"To sai kin zo"
Ƙarfe biyar da rabi sai ga Madam Bintu a gidan ta. Hansa'u ta kira ta kawo musu abin taɓawa.
"Har yanzu ba ki rabu da wannan matar ba bayan shirmen da ta yi kwanaki"
"Bintu tausayi ta ke bani Allah. Besides yanzu ta iya aiki sosai ba kaman farkon kawota ba sai dai ba a rasata da shirme kam. Most importantly tana sani dariya and that's help alot ga mu ma su hawan jini"
"Ok" ta faɗa tana ƙarewa Hansa'u kallo. Gani ta ke kaman idon matar na mata kama da wacce ta sani amma ta rasa gano ko wacece.
Bayan Hansa'u ta bar wajen Madam Bintu ta tambayi Bilkisu yadda taron matan Gwamnoni ya kasance dan lokacin da aka yi taron ba ta ƙasar.
"Ba abunda zan ce miki Bintu sai dai in ce kawai taro yayi kyau. Kuma za a sake wani taron nan ba da daÉ—ewa ba"
Madam Bintu ta kalli Hajiya Bilkisu cikin rashin fahimta, maimakon ta mata ƙarin bayani sai kawai ta fashe da wata ƙasaitacciyar dariya.
**
A chan gidan Yallaɓai kuwa Chief of Staff (COS) ɗin Gwamna ne a gaban Yallaɓai yana ma sa bayani mai mahimmanci wanda ya sa Yallaɓai nitsuwa na ban mamaki. Har ya gama bayanin Yallaɓai bai ce komai ba sai ma murza gemunsa da ya fara yi a hankali.
Ba kasafai ya ke samun ma su taurin zuciya irin ta KACHALLAH ba. Shekaru da dama an taɓa yunƙurin aikata irin wannan abu sai dai kuma komai ya zo ya chanja a ƙurarren lokaci.
"Ka haɗa meeting da Kachallah cikin satin nan" Yallaɓai ya faɗa bayan yayi dogon nazari.
COS yai murmushin gefen baki dan ya san yanzu liyafa za ta cigaba. Ya ƙwallafa rai sosai akan Gwamna Saminu Bacchi sai dai cikin shekaru uku da yai a kan mulki sun samu saɓani sosai domin lokacin da idon Gwamna Saminu ya buɗe da kuɗi sai ya zamana yana ƙoƙarin take duk wata hanya da su suke yagan rabon su, yanata wawure komai shi kaɗai da iyalin sa ba dan Yallaɓai ya tsayar ma sa ba wasu abubuwan haka za su dinga wuce shi.
Saifuddeen Sa'ad Kachallah daban ya ke da Gwamna Saminu, kuɗi ba za su ruɗe shi ba. SSK ya gaji arziƙi irin arziƙin da ko da ba zai yi wani aiki ba zai isheshi ci da iyalen sa har iya karshen rayuwar su ba tareda sun yi talauci ba.
SSK shine mafita a gareshi da shi da KACHALLAH.
***
"Wallahi an cuceni Ya Ubayd. MD mugu ne wallahi"
Ubayd yai murmushi ya ce " ni kam ya min dai-dai, dama daurewa kawai na ke yi amma kullum aka nunaki a TV sai na ji kamar zuciyata za ta fashe"
"To ta Allah ba taka ba. Sai an maidani reporting unit"
"Ina kishin ki Asiya na haƙura ne kawai saboda babu yadda zan yi amma Allah idan ki ka shigo gidana ba za ki sake bayyana a TV ba, ko dai ki tsaya aiki a bayan fage ko kuma ki haƙura da aikin"
"Ya Ubayd you are joking right"
"I'm not Asiya. Gara ma ki saba da inda aka kai ki yanzu"
Sati ɗaya da suspension ɗin ta aka kirata akan ta dawo. Yau ta fara fita aiki amma duk ta ji ba daɗi ba ta son ɓangaren da aka kaita ko kaɗan.
"Ya Ubayd ba haka mu ka yi da kai ba baka ce za ka rabani da aikina ba"
"Ba rabaki zanyi da aikin ki ba na dai ce bayan munyi aure ba ƙaton da zai sake ganin ki a TV yana ƙare miki kallo especially with irin shigan da ki ke yi" yai maganar da ɗan ƙarfi
Asiya ta miƙe daga kujeran da ta ke zaune ta ce "ba ka isa ba kuwa"
Ta wuce ta barshi a wajen baki buÉ—e.
Washegari ko jiran sa ba ta tsaya yi ba ta hau keke ta wuce office...
***
" na gaya miki babu kuɗi a ƙasa, duk wani abu da zamuyi yanzu mutane za su yi magana. We need this year to work on something saboda campaign da za a fara nan da watanni huɗu ma su zuwa"
Gwamna Saminu Bacchi kenan yana ƙoƙarin lallashin matar sa.
"Kana so ka ce min ba ka da kuÉ—in da zamu celebrating 8years anniversary na mu?"
"Ba wai ba kuÉ—in bane amma kuÉ—in campaign ne"
"Kar ka gaya min magana dan Allah. Uban me Saifuddeen Kachallah ke da shi da zai iya celebrating 15yrs anniversary na su a tsakiyar teku shekaru biyu da suka wuce. Na je party É—in fa. Sati biyu aka yi a cikin jirgin ruwa wanda komai da komai da mutanen ciki su ka yi yana wuyan sa"
"Sha'awanatu. Saifuddeen Kachallah millionaire ne tun kafin mu hau gwamnati ko mi zai yi ba wanda zai zargeshi amma ni..."
"Ba zan yadda ba fa. Dole ne ayi anniversary party namu a Italy. Wallahi kai ka ke sawa ma Bilkisu Kachallah tana raina ni. Ina matar Gwamna amma ko motan da ta ke hawa tafi tawa"
"Yanzu kinsan ya za ayi ne? Za mu yi party amma a nan Nigeria. Bamu jima da dawowa daga ƙasar waje ba idan muka sake fita mutane za su yi magana..."
"Wai ina ruwanka da mutane ne. Kai fa Gwamna ne. Gwamnar jahar CONGO wancan tafiyar Asibiti ka je wannan tafiyar kuma yana cikin yiwa iyalinka hidima ne"
" Amma Sha'awa..."