← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shiyasa na ce assignment ne. Ko dai yanzu akwai aikin daya gagari Asiya-Shahidah ne?"

Asiya ta ƙunshe baki tareda sauke ajiyar zuciya.

"Ba komai Sir zan nemi permission daga gidan Gwamnati kafin satin nan ya ƙare Insha Allah"

Ko da ta bar ofishin sa office É—in su CY ta wuce ta sameshi yana editing wani video da za a É—aura anjima.

"Babez ya na ga kin haÉ—e rai?"

"za ka rakani Government office gobe"

"Government office? Why?"

"Kai dai ka shirya kawai".

"Okey dokey"

***

Ƙarfe takwas saura suna bakin Gidan Gwamnati. Ba su samu matsalar shiga ba suna nuna ID card ɗin su aka ce su wuce.

Wani security ne ya mu su rakiya har ofishin Sakataren Gwamna.

Asiya ta yiwa Mr Baffayo Sakataren Gwamna bayanin abinda ke tafe da su. Bayan ta gama ya ce " Malama Asiya na ji daÉ—in zuwan ku gaskiya sai dai Mai Girma Gwamna ya ce ba zai yi zama da kowani É—an jarida ba yanzu, sai dai ko gaba"

"Ranka shi daÉ—e, Hill TV zata yi hira da shi ne gameda tarihin rayuwar sa babu maganar siyasa a ciki"

"Malama Asiya kenan. Zai fi dai ku haƙura zuwa lokacin da Gwamna zai so yin hiran da kan shi"

"Sir da dai ka miƙawa Gwamna letter ɗin mu ƙila a dace" ta faɗa a marairaice

Sakatare ya karɓi wasiƙar ya ce zai miƙawa Gwamna.

Su ka ma sa godiya su ka tafi.

Koda Gwamna ya dawo Sakatare bai ba shi wasiƙar ba, bai ma gaya masa su Asiya sun zo ba.

Asiya na nan tana jiran kiran Sakatare amma shiru. Washegari ƙarfe goma ta sake komawa ofishin Gwamna.

"Kin ga abinda na faɗa miki ɗin ne dai, Gwamna ya ce ba zai karɓi gayyatar ku ba"

"Dan Allah Malam ka sa baki. I really need to take his interview"

"Ki yi haƙuri. Zan dai sake yi ma sa magana ince kin sake zuwa. Kin san matsalar ne. Akwai wanda su ka fi ki naci sunyita zuwa Kwanakin baya, ƙarshe Gwamna ya ce kar a sake bari ɗan jarida ya zo ofishin sa amma..."

"Oh haka ko?" Asiya ta faÉ—a a hasale

Sakatare ya zuba ido yana kallonta da mamaki.

Asiya ta ciro wasiƙar da su ka ajiye ma sa jiya a ƙasan laptop da ya ke aiki da shi.

"Zan iya rantsewa wannan bai je hannun Gwamna ba"

Sakatare ya fara kame-kame. Allah na gani girman shekarunsa da Asiya ta gani ya sa ta iya controlling kanta ba ta ma sa rashin mutunci ba.

"Zan dawo gobe, zan jira ko ƙarfe nawane sai na ga Gwamna da kaina na bashi wasiƙar. Zan haƙura ne kawai idan shi da bakinsa ya ce ba zai yi hira da ni ba"

Daga haka ta fice daga office É—in ta bar Sakatare baki buÉ—e.

Bayan tafiyar Asiya da Sakatare ya shiga wajen Gwamna kai ma sa wasu takardu sai ya haɗa da wasiƙar Asiya.

"Wannan fa?" Gwamna ya tambaya yana ɗaga envelope ɗin da wasiƙar ke ciki.

"Your excellency gidan talibijin na Hill TV ke son hira da kai"

"Malam Baffayo hira da 'yan jarida sai gaba, we have better things to do with our time now"

"Yes excellency"

Daga haka ya fita bai sake É—ago maganar ba.

Washegari kuwa kamar yadda Asiya tayi alƙawari sai gata a ofishin Gwamnati sai dai wannan karan ko ƙarasawa ofishin Sakataren Gwamna ba ta yi ba aka dakatar da ita.

"Ban gane in tafi ba. Ina son ganin Gwamna ko akwai dokar da ta hana hakan?" Asiya ta faÉ—a wa security guard É—in daya tsareta cikin tsawa.

"Gwamna baya office ki je ki dawo wani lokaci"

"Ba inda zan je. Gwamna yana nan. I need to have audience with him"

" idan ba ki fita ta lallami ba, za a fita da ke ta ƙarfi. So please leave"

"Ba inda zan je fa" Asiya ta faÉ—a tana gyara tsayuwarta.

A ofishin Sakatare kuwa Gwamna ne ya zo wucewa zuwa wani exco meeting ya jiyo hayaniyar da ake yi hakan ya sa shi ya É—an tsaya.

COS da ke bayan sa ya kalli Sakatare cikin tsawa yace "wai wacece a wajen nan ne?"

"Wata 'yar jarida ce ta dage sai ta ga Gwamna".

"Kul ka taɓa ni, wallahi yatsata ka taɓa sai ka san wacece Asiya-Shahida a garin nan. Na san 'yanci na dan haka kar ka kuskura ka min barazana"

Wannan karan tana maganar ta zauna a kan kujera da ke Lobby ɗin tareda ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana huci.

"Malam Baffayo ka ce ta dawo ranan Monday"

Ba da ƙarfi yai maganar ba amma duk sun ji shi. Bai jira mai Sakataren zai ce ba ya wuce abinsa.

Asiya ta zauna na kusan minti shabiyar kafin Sakatare ya fito.

"Malama Asiya ya da haÉ—e rai haka"

"Ba fa inda zan je" ta faÉ—a tana girgiza kai

Sakatare ya miƙa ma ta wani envelop. Tana gama karanta takardar da ke cikin envelope ɗin ta saka ihu. Sai kuma ta yi saurin rufe bakinta da hannunta.

Sakatare yai dariya ya ce " gaskiya kin taki sa'a. Gwamna ya amince ya ganki ranan Monday, best of luck"

Fiska a washe Asiya ta ma sa godiya ta tafi. Shi kan sa Sakatare yayi mamaki da amincewar Gwamna cikin sauƙi haka.

***

A chan ɗakin da ake taro kuwa dukkan wanda ya ke da alaƙa da wannan taro ya riga ya hallara dama Gwamnan kawai ake jira.

COS ne ya ja masa kujera ya zauna yana kallon mutanen da ke wajen ɗaya bayan ɗaya. Kusan minti guda ya ɗauka sannan ya ja dogon numfashi sannan ya ce "gentlemen ina buƙatar report na wannan wata"

"Kwamishina Isiaka" Gwamna ya kira yana duban wani ƙaton baƙin mutum sanye da babbar riga kalar light blue. Kwamishinan ilimi yai gyaran murya sannan ya fara bada bayani wanda ya ɗaukeshi tsawon minti huɗu da rabi.

"Not impressive Kwamishina Isiaka. Ban ji ka yi maganar Albashin Malaman firamare da za a ƙara ba"

"Your excellency mun submitting budget farkon watan nan amma abunda ya iso mana daga hannun Kwamishina of Finance shi mu ka yi amfani da shi"

Gwamna SSK ya juya ya zubawa Mr Paul idanunsa ma su kaifi hakan ya sa shi fara wiki-wiki da ido.

"Mr Paul!" Gwamna ya faɗa da ɗan ƙarfi.

"Excellency saboda akwai basusuka dayawa da tsohon Gwamna ya bari muna so a fara rage wannan kafin a fara maganan ƙara albashi"

"Abinda aka fara tunkarana da shi lokacin dana ƙarfi wannan kujera shine maganan ƙarancin albashin Malaman Firamare. If i can remember clearly. Sai da na ce Kwamishina Isiaka ya drafting budget ya nuna maka, kana tunanin da wasa na yi maganar?"

"No your excellency" Mr Paul ya faɗa yana sunne kai ƙasa.

"Ina Kwamishinan raya karkara"

"Your excellency" wani mutum fari dogo ƙyamusashshe ya faɗa yana ɗaga hannu.

"Banga report dana buƙata ba tun farkon watan nan"

Cikin turancin sa da take nuna asalin harshen bahaushe ya fara bayani.

"Na tura memo wa Kwamishina Paul ya kai sau huÉ—u amma babu wanda ya reply aciki"

Wannan karan ma Gwamna ƙurawa Mr Paul ido yai.

"Your excellency budget da aka yi da tsohon Gwamna babu buƙatun Kwamishina Ɗanladi a ciki shiyasa babu yadda za ayi yanzu a ƙirƙiro kuɗi a bashi sai yai haƙuri sai wata shekarar"

"Oh hakane ko?. Ina buƙatar budget da aka drafting na wannan shekarar da kuma abubuwan da akayi da su haɗe da receipts na komai. Kwamishina Paul zan saurari report ɗinka gobe da safe a office ɗina"

Mr Paul ya taƙune fiska kamar wanda ya tauna flagyl yayinda sauran excos da ke wajen kowa ya sha jinin jikinsa.

Lokacin da SSK ya ke mataimakin Gwamna bai taɓa ɗaga murya ba, infact idan za ayi meeting sau dubu to zaka iya irga iya maganan da yai a meeting ɗin amma wai yanzu roughly wata biyu daga rantsar da shi ya rikiɗe musu ya koma wani Zaki.

Magana ta ƙarshe da aka yi shine maganar naɗa sabon mataimakin Gwamna wanda Gwamna ya tabbatar mu su da cewa ranan talatin ga wata za'a rantsar da mataimakin Gwamna wanda har yanzu basusan ko wanene ba.

"Babu mamaki idan kuka cigaba da irin wannan sakacin a office É—in ku zan sake sabon cabinet"

Gwamna na gama faɗin haka ya miƙe tsaye yana ɗaukan wayoyinsa guda biyu da ipad yayinda sauran excos ɗin ma suka miƙe tsaye suna faɗin "Excellency"...

A ɓangaren Asiya kuwa tana fita daga gidan Gwamnati ta wuce ma'aikatar su. Tun a hanya ta kira CY ta ma sa albishir.

Tana isa kuwa Office É—in MD ta fara wucewa. Tana shiga ta ajiye ma sa takardar hannunta wanda tunda ta cirota daga cikin envelope ba ta iya maidashi ciki ba.

"Yaushe zan koma bakin aikina?" Ta faÉ—a tana kallon MD daya wangame baki saboda ganin seal É—in Gwamna akan takardar.

"That's fantabulous Asiya. Ya kika yi? Kai i'm happy. This means gidan talabijin É—in mu ne za ta fara hira da Gwamna Saifuddeen. Whoaw!"

Asiya ta sa dariya. Farin cikinta ko kaɗan ba shi da alaƙa da kasancewarta 'yar jarida ta farko za ta yi hira da Gwamna SSK tun da ya hau kujerar Gwamna. Farin cikin ta ya zo daga abu biyu ne. Na farko aikinta da za a dawo mata da shi (ta tsani aikin editting ɗin nan). Na biyu kuma cimma burinta da ta yi.

Idan za ka lissafo halayen Asiya to dole ka sako cewa ita É—in mace ce mai son cimma duk wani abu da ta sa a gaba.

A cikin dictionary É—inta babu kalmar impossible. Akoda yaushe slogan É—inta shine *it's possible but.... HOW*

Kafin ta bar office É—in MD sai da ya ce ta drafting tambayoyin da za ta yiwa Gwamna ta kawo mishi kafin a tashi...

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

05

Tunda Gwamna SSK ya zauna ya ke sauke numfashi akai-akai saboda maganganun Baffan na sa daya saka mishi rashin nitsuwa har ya ji ƙirjinsa ya cunkushe. Ƙarshe hannu ya sa a aljihu ya lalumo inhaler yai saurin jijjigata sannan ya kai bakinsa ya matsa.

Alhaji Sani ya sassauta muryansa ya ce "sannu Saifu. Har yanzu yana damunka sosai ne?"
Chapter 10 · 0% Book details