← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 38

Sashe 16

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waɗanda kika samu saɓani da su sun zo sun karɓi laptop ɗinki na gida da wajen aiki dama wayarki amma sun dawo da wayar taki jiya. Sun bayarda saƙo a baki *ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, hakan zai sa su manta da komai*"

"Abba ya zaka min haka?" Ta ma rasa haushin wanne É—aya za ta ji. Na halin da CY ya shiga saboda ita ne ko kuwa dai na aikin da ya hanata ne ko kuma na É—auke laptop É—inta da COS ya sa akayi. Abin takaicin ma a laptop É—in kawai ta tura recording É—in ba ta riga ta tura a wani wajen ba.

"Asiya ki yiwa Allah ki manta da komai. Bana so ko da Umman ki kiyi wannan maganar saboda kar hankalinta ya tashi"

"Abba dafa na mutu yanzu, dafa..."

"Ki godewa Allah kawai ki riƙe bakin ki Asiya"

Abba bai bata daman magana ba sai kawai ta fashe masa da kuka, da tayi mai isarta ta miƙe ta bar falon.

Tuwon shinkafa miyar taushe Umma ta zubo mata bayan tayi sallar Isha, ta haɗa mata da zoɓo mai sanyi. Duk yadda take marmarin ci kafin a girka yanzu ya fita mata aka saboda rasa recorder ɗinta da tayi, koya akayi suka samu recorder ɗin ma oho, dan a ƙasan katifar Umma ta saka bayan ta gama kwafan abinda ke ciki zuwa laptop ɗinta. It means bata da wani evidence kenan.

Umma ta katse mata tunani da cewa ta ci abinci

"Umma ki bani a baki" ta faÉ—a da yaren kurame. Umma tayi murmushi ta wanke hannu ta fara bata a baki.

Ƙarfe shabiyu na dare tanata juyi a kam gado ta kasa yin bacci. Wayarta da Abba ya bata an share komai na kai kamar sabon waya. Tunanin rashin imani irin na Gwamna ya tsaya mata a rai, ita yanzu ta daina ganin laifin COS ma dan gani take da umurnin Gwamna ya aiwatar da komai.

Ƙarshe ta jawo wayarta ta sake downloading twitter da facebook da aka goge. Tana saka gmail da password ɗinta na da ta samu access zuwa ga tsohon account ɗinta nan da nan ta shiga rubuta dogon article a blog website nata, data gama ta kwafa ta kai shi twitter ta jerasu a dogon thread of tweets . Ta kai facebook ma ta posting a wall nata. Tana ganin duka rubutun ya hau tace "Excellency yanzu aka fara wasan"

Yadda ake fama da talauci da wasu matsaloli wannan rubutu nata tabbas zai jawo hankalin mutane kan Gwamna and this is good.

Kalaman ɗan jarida suna da kaifi, kalaman da ke iya kunna jita-jita tsakanin al'umma ya maida gaskiya ƙarya sannan ƙarya ta koma gaskiya.

Kusan minti goma shabiyar kafin ta fara ganin comment na 'yan tsirarun mutanen da suka gani. Tana bin comments É—in tana murmushi idan taga wanda ya yabi Gwamna kuma sai ta yi tsaki.

Asiya bata kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi, dake Umma a ɗakin Abba ta kwana yasa bata samu mai tashinta da Asuba ba sai ƙarfe shida saura minti biyar da Umma ta shigo ɗakin ta tasheta sallah...

***

Chief of Staff Lamara Damana yana kwance kusa da matarsa ƙarfe huɗu da rabi wayarsa ta shiga ƙara. Bayan ya ɗau wayar miƙewa yai ya bar kan gadon dan wanda ya kira ɗin special agent ɗinsa ne mai kula masa da hidimominsa a yanar gizo.

"Ina jinka Felix" ya faÉ—a lokacin daya zauna a kujeran dake falonsa.

"Asiya again?" Ya faɗa yana cizen leɓe. Lokacin da aka tabbatar masa Asiya bata mutu ba sannan bata ji ciwo sosai ba yaso ya sa a ƙarisata a Asibiti amma daga baya ya chanja ra'ayinsa. Beside ita macece dole taji kashedin iyayenta.

Yanzu da Felix ke karanto masa abinda ta ɗaura yayi mamakin ƙarfin halinta.

"This girl! Yanzu dai kasa a blocking accounts nata, sannan ka controlling duk wata jarida da zata yi sharyi akan abinda ta rubuta"

Lokacin da Asiya ta idar da sallan Asuba ko Azkar bata yi ba ta jawo waya ta fara duba twitter account ɗinta sai dai kash! An riga an banning account ɗin tun misalin ƙarfe biyar na Asuba, ta zaro ido waje tareda duba website nata cikin sauri sai dai shima an blocking na shi, facebook ma haka.

Tayi ƙoƙarin searching article ɗin a google amma an sauke shi gaba ɗaya babu ko mai kama da shi.

"Nooo" ta faÉ—a tana kaiwa sallayar da ta ke kai duka...

Gwamna na zaune a office wayarsa ta shiga ƙara yana dubawa yaga sunan Baba.

"Saifu mi yake faruwane? Yanzu nake jin wai Umaru Kwom yayi wata magana a twitter akan abinda wata 'yar jarida ta É—aura"

"Bani da labari Baba amma yanzu zan tabbatar"

"Nayi magana da COS amma ka tabbatar da adviser É—inka ya kashe duk wani hayaniya da za ayi a yanar gizo akan maganar"

Gwamna na ajiye waya ya kira mai magana da yawunsa a yanar gizo.

Umaru Kwom abokin adawar Saifuddeen Kachallah ne saboda lokacin yana tareda Alhaji Sani Kachallah ya so ya zamo mataimakin tsohon Gwamna Saminu Bacchi amma Alhaji Sani ya ƙi ya tsaida Saifuddeen, tunda aka tsaida shi kuwa ya fice daga jam'iyyarsu ta CDA ya koma Q party.

Lokacin da Special adviser Ahmad Tanko ya shigo ko kaɗan Gwamna bai ji daɗin yadda aka ƙi sanar dashi abinda ya faru ba.

"Mi Umaru Kwom ya ce?"

"Excellency an riga an cire duk wani tweet ko post na 'yar jaridar amma awa biyu da suka wuce Umaru Kwom ya tweeting wasu maganganu daga ƙarshe ya haɗa da screenshot na tweet ɗin 'yar jaridar"

"What did he say?" Gwamna ya faɗa da ƙarfi.

Ahmad ya fito da wayarsa ya fara karanta tweet ɗin "inada tabbacin 'yar jaridan nan tayi gaskiya duba da yadda Gwamna ya biya kuɗin aikin da za ayi wa Clement Yohanna a ƙasar waje. Idan ba a manta ba Clement da Asiya sune suka je interview ranan, idan har babu lauje a cikin naɗi ba abinda zai sa ayi yunƙurin hallaka 'yar jaridar a ranan da tayi maganar mutuwar Gwamna Saminu Bacchi. Bisa wannan, muna so mu gayawa Gwamnatin SSK cewa duk abinda ya sami Asiya 'yar jarida nan gaba zamu yi ƙaran Gwamnati. #a binciki mutuwar tsohon Gwamna"

SSK ya sauke ajiyar zuciya kafin yace Ahmad ya miƙa masa wayar yaga rubutun da Asiya tayi.

Bayan ya gama karantawa ya miƙa masa wayar yace ya fita masa daga office ɗinsa.

Ba yadda za ayi Asiya tayi wannan iƙirarin idan har ba wai ta ga ko ta ji wani abu ranan da suka zo bane. Dole ne ya gana da 'yar jarida Asiya Shahidah...

***

"Shikenan ai tunda kinyi gaban kanki, kin nuna cewa ba nina haifeki ba"

"Abba ba haka bane, Wallahi ba haka bane"

"Kinyi gaskiya Asiya, ba nina haifeki ba ban kuma manta da hakan ba.Tunda ban isa na baki shawara ki bi ba shikenan Allah ya baki sa'a. Kije kiyi magana da Umaru Kwom daganan ku wuce kotu ku bi wa Marigayi Saminu Bacchi hakkinsa"

Asiya ta kalli Abba tana zaro ido. Kenan Ubayd ya gaya masa komai.

"Tashi ki tafi"

"Abba..."

"Tashi ki tafi kawai"

Jiki a sanyaye ta fice daga falon.

Ɗazu Umaru Kwom da kansa ya kirata yace yana son haɗuwa da ita saboda su tattauna iƙirarin da tayi a yanar gizo. Ya tabbatar mata yana tareda ita ɗari bisa ɗari. Bata ɗauka Abba zai fassara maganar haka ba. Abba bai taɓa faɗin magana makamancin wannan ba hakan na nuna ba ƙaramin fushi yai da ita ba. Ubayd ma tun safe daya kira ya gama balbaleta da masifa bai sake waiwayanta ba, koda ta kirashi dan ta sanar dashi kiran Umaru Kwom ƙin ɗaukar wayarta yai.

Lokacin da zata shiga ɗakinsu ta ji Hindatu na mata habaici wai 'karyar 'yan siyasa' bata tanka mata ba ta shige ɗaki. Rasa ma mi zatayi tayi dan yadda ran Abba ya ɓaci bata jin zata iya zuwa wajen Umaru Kwom.

Da yamma lis tana kitchen tana haɗawa Umma zoɓonta na siyarwa Ubayd ya shigo da sallama. Kasa amsa sallamar tayi saboda wani tsoro da taji ya taso mata lokaci guda. Umma ba ji take ba bata ma san anyi sallamar ba tana faman tuƙa tuwon Masara.

"Inna Yaha ina Asiya?" Ubayd ya faɗa bayan ya leƙa ɗakin Umma bai ga kowa ba.

Inna Yaha dake ƙullin gyaɗa ta kauda kai gefe tace "kaban ajiyarta ne?"

Bai ma gama jin mi take faÉ—a ba ya wuce kitchen.

Suna haÉ—a ido da Asiya ta ji gabanta ya faÉ—i. Idon Ubayd ya kaÉ—a yayi ja.

Sama-sama ya gaishe da Umma yace da Asiya ta biyo shi.

"Yaya Ubayd miya faru?"

Bai kulata ba ya fice daga kitchen É—in cikin sauri.

"A dai bi a hankali har yanzu ba a shafa Fatihan ba" Inna Yaha ta faÉ—a tana tauna gyaÉ—a.

Da Asiya da Ubayd É—in duk babu wanda ya kulata suka shige falon Abba.

"I'm disappointed in you Asiya. Ban ma san mizan faÉ—a ba. Tunda attension kike nema kin samu yanzu. Congratulations! Gwamna zai zo wajenki yau da dare"

"Gwamna kuma?"

"Abinda kike nema kenan ina, kin samu sai mi ya rage kuma"

Zuciyarta ne ya tafaso. Taya zai zargeta da neman suna.

"Kar ka gaya min magana, idan baza ka tayani neman hakkina ba baka da ikon zargina"

"Asiya kar ki kawo mana rikicin siyasa gidan nan. We are happy the way we are"

"Ni ban san mi kake nufi ba. Ni ba harka nake son yi da 'yan siyasa ba i just wanted to..."

"A gaban Gwani aka mari Abba" maganarsa ya katseta.

"Mari?"

"Yes Asiya. Abba bai gaya miki yadda komai ya faru bane saboda baya so ya ɗaga miki hankali, amma ke ba abinda kika sani sai kanki. Ranan da suka zo karɓan Laptop ɗinki Gwani na wajen shi ya faɗa min komai. Asiya yaron da bai kai sa'an Habibu ba ya ɗaga hannu ya mari Abba saboda ke..."

"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun"
Chapter 16 · 0% Book details