Sashe 28
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Wanda suka min magana ta whatsapp ko wattpad ban amsa ba, ina baku haƙuri. Wanda suka kirani numba na a kashe suma ina basu haƙuri. Ya kamata ace nayi muku bayani amma banyi ba. Ina neman afuwa akan haka.*
*Insha Allah part 2 zai fara zuwa daga ranan Asabat idan Allah ya kaimu.*
*Nagode da haƙuri da ni...*
13
Matar Gwamna. Ayyiriri Amarya"
"Queen Bee bana so, ki bari. Tukunna ma ya akayi kika sani? "
Queen Bee ta É—aga mata waya tana faÉ—in Umma.
"Haba Asiya! So kike a kaiki gidan Gwamna kamar wata ƙwarangal. Look at you"
"Idan wannan ya kawoki, tashi ki tafi"
"Baki isa ba, Wallahi baki isa ki ja mana kunya ba. Dole sai anyi miki gyaran nan"
"Zaki yi ki barni dan ba abinda zanyi"
Duk yadda Queen Bee ta so su fara gyara Asiya bata ba da haÉ—in kai ba. Duk da Umma ta sa baki hakan baisa ta chanja ra'ayinta ba.
Ana saura kwana bakwai a ɗaura aure, da safe irin ƙarfe goma shaɗaya aka kawo lefen Asiya. Lokacin bata gida, ta raka Sumayya makaranta, za ta fara registration dan ta samu admission a Jami'ar Congo.
Lokacin da Asiya da Sumayya suka shigo gidan, a cike suka samu da mutane, yawanci maƙota ne sai kuma 'yan tsirarun 'yanuwansu dake zaune a Congo.
Faty 'yar Inna Yaha ce ta jata suka shige falon Abba saboda ɗakin Umma a cike yake da baƙi.
"Ban gane mi yake faruwa ba, wani taro ake yi a gidan?"
" 'yaruwa kinga lefenki kuwa?"
Ƙoƙarin buɗe ɗakin Abba ta shiga yi Asiya ta katseta. Bata buƙatar ganin koma minene aka kawo. Ashe shiyasa jiya da yamma Umma da Fatyn suka wuni suyan kaji a kitchen.
"Ki barshi Faty, ba sai na gani ba" Faty bata bari ta ƙarisa ba ta jata suka shige ɗakin.
Akwatuna ne akan gado gefen gado da duk wajen da akwai sarari. Wasu baƙaƙe, wasu ja, wasu blue, wasu brown, wasu lemon green da kalan silver.
"Ashirin da huɗu cif" Faty ta faɗa tana wage haƙora.
"Yanzu Anty Faty an buÉ—e dukkansu?" Sumayya ta tambaya cike da farin ciki.
"Guda shabiyu aka buÉ—e, Hajiya Adda tace a barsu haka, wai da ana maida kayan an rasa zannuwa uku a ciki"
Asiya juyawa tayi ta bar musu ɗakin dan ba zata juri ganin kayan takaicin nan ba. Ubayd ya kammala haɗa kayanta kawowa ne kawai ba ayi ba. Akwatuna biyar ne kuma ta riga ta san minene a ciki saboda fiye da rabin kayan kuɗi ya bata ta siya, wasu kuma sukan je siya tare. Lefen da Ubayd ya haɗa shi take so, ba wannan kayan ƙaryar ba.
Fita tayi daga gidan gaba É—ay ta wuce shagonsu. Tana cikin keke text É—in Umma ya shigo, ta maida mata amsa da cewa shago zata je.
Saura kwana huɗu ɗaurin aure sai ga text ɗin Ubayd a wayarta, yace ta zo ta sameshi a office ɗinsa da ƙarfe biyar na yamma. Ƙarfe uku text ɗin ya shigo, dan haka tana sallar La'asar ta ce da Umma zata fita, Umma tace ba inda za ta je. Hakan ya sa ta mata ƙarya akan gidansu Queen Bee za su je karɓan saƙo ita da Sumayya. Umma tace su je amma lallai su dawo kafin ƙarfe shida na yamma.
***
"Daddy da gaske aure zaka ƙara?" Nana tayi magana tana tsare mahaifinta da idanu.
Gwamna yai shiru bai ce komai ba.
"Ka bata amsa mana Mijin 'yar Kurma"
Gwamna ya maida dubansa ga Hansa'u da ke bawa Junior abinci a baki yace "Kada ki sake bashi abinci a baki. Kada wanda ya sake bashi abinci a baki"
"Tuba nake ranka ya daÉ—e" Hansa'u ta faÉ—a tana ajiye cokalin da ke hannunta
"Kar ka saukar da fushinka akan ɗana. Kai ka sawa kanka auren jikar maiƙusumbi" Nana da Zunnairah suka fara dariya ƙasa-ƙasa.
Ko kallon Bilkisu bai yi ba ya miƙe ya bar dining room ɗin. A irin wannan ranaku da yake samun daman zama da iyalinsa ba abinda yake so sama da soyayyarsu. Sai dai yanzu kam Bilkisu ta gaza bashi wannan soyayyar. Dolene ya takawa Bilkisu birki. Juniour ba yaro bane da sai an bashi abinci a baki. Nana ta yi girman da bai kamata ta masa magana karangatsau haka ba, sai dai koma minene shi ya jawo wa kansa.
A ƙaramin falo Bilkisu ta zauna ita da babbar ƙawarta Madam Bintu suna tattaunawa kan kasuwancinsu. Bayan Hansa'u ta kawo musu abin taɓawa sai kawai suka ga ta zauna a tsakiyar falon ta ƙurawa TV ido.
"Hansa'u lafiya? Baki da aikin yi ne?"
"Shirin su Aarti da Yash zan kalla"
"A duk faÉ—in gidan nan sai a nan zaki yi kallo. Tashi maza ki bani waje" Bilkisu ta daka mata tsawa.
"Kema dai Bilkisu miyasa zaki kawota nan. A chan gidanku ma tana shirme balle a nan"
"Akwai ƙauyanci a tattare da ita amma ta iya aiki ne Bintu. Kuma gaskiya ban sake da ma'aikatan gidan nan ba duba da cewa sun yiwa Sha'awanatu aiki a baya. In fact, chief cook ɗin ma sai dana sa aka chanja shi"
"Wai baza ki tashin bane?"
Hansa'u ta miƙe tana susa kai ta bar wajen.
***
Da sauri-sauri take tafiya zuciyarta na tsalle a cikin ƙirjinta. Ita kaɗai ta san ya take ji a ranta.
Tana son shi, tana fushi da shi, tana kuma tausayinshi.
Sai da ta ja dogon numfashi kafin ta buɗe ƙofar office ɗinsa a hankali.
Ubayd na zaune a madaidaicin office É—insa da ke É—auke da wata na'ura da ake duba idon mutane. Akwai kujeru biyu na zaman masu jinya. Akwai manyan hotonan ido da akayi rubutu ajiki a bangon office É—in.
Farar riga da likitoci ke sanyawa ya ɗaura akan jamfar da ya saka kalar toka. Fiskarsa ɗauke da baƙin gilashi daya ɓoye idanunsa.
Sautin karatun ƙur'ani ke fitowa daga laptop ɗinsa, shigowarsu ya sa shi katse karatun.
"Ina wuni Yaya" Sumayya ta gaisheshi idonta na kallon ƙasa, duk da yana sanye da gilashi ba zata iya kallon idonsa ba.
Duk cikin 'ya'yan Ale, Asiya ta fi jituwa da Sumayya shiyasa ya mata farin sani. Tun kafin ta ƙare Sakandare ta sha zuwa hutu wajen Asiya.
"Lafiya Sumayya, yaushe a gari?"
"Na É—an kwana biyu"
"Bismillah, ga kujera"
"Barin baku guri" bata ji ma mi yake faÉ—a ba ta fice daga office É—in da sauri har lokacin Asiya na tsaye ta zubawa Ubayd ido.
"Ki zauna Asiya"
Kafin ta zo ta tanadi maganganun da za ta faÉ—a masa amma ganin fiskarsa ya share komai na kwanyarta.
"Asiya ..."
"Kai na ke so Ya Ubayd, fight for me, fight for us" ta faÉ—a lokacin da ta zauna
"Asiya muyi haƙuri"
"Zamu iya guduwa Ya Ubayd, there's still time. Mu je Kano gidan..."
"Ba inda zamu je Asiya"
"Saboda ka dena sona? Saboda kana tsoro, Saboda..."
"Saboda na karɓi ƙaddarata da hannu bibbiyu. Saboda nayi alƙawarin yiwa mahaifina biyayya matuƙar ba abune daya saɓawa addini ba"
"Oh! Ni ce ban san mi nake ba ko. Ni ce bana girmama iyayena ko?"
"Ina sonki Asiya Shahidah. Bana tunanin zan so wata kamar yadda nake son ki. Amma in har aurenki da Gwamna zai kawo..."
"Ya isa!" Miƙewa Asiya tayi tsaye, ta sa hannu ta goge fiskarta fes babu ko ɗigon hawaye.
"Ya Ubayd ka ci amanata, ka ci amanar soyayyarmu. Zan auri Gwamna, but mark my words Ya Ubayd, Ni Asiya sai na ga ƙarshen Gwamnatinsa, Ka huta lafiya"
"Mine... Asiya... Asiya... Asiya"
Ciro hankerchief yai daga aljihun labcoat É—insa ya shiga goge gumin goshinsa, Shikenan daga yau bashida ikon kiranta Mine. Lokacin daya cire gilashin idonsa sakanni kaÉ—an bayan fitan Asiya, hawaye ne masu É—umi suka fara gangaro masa. Chan cikin zuciyarsa kuma yana yiwa Asiya addu'ar Allah ya sassauta zuciyarta kar taje tayi abinda za tayi dana sani daga baya...
**
Kwana uku saura ɗaurin aure gari ya ɗauka cewa Gwamna zai ƙara aure. Ba kuma kowa zai aura ba sai 'yar jaridan nan da ta so ɓata masa suna kwanakin baya.
Mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu akan batun, wasu na ganin kwata-kwata bai dace ba, wasu kuma suka fara cewa ai dama chan karuwarsa ce, maganganu dai kala-kala.
Bilkisu Kachallah ce ta juya akalar maganar inda ta fito ta bayyana cewa tausayin mahaifin Asiya yasa Gwamna ke son auren Asiya Faruƙ Baba. Ta bayyana cewa, sun samu labarin saurayin da zai aureta ya fasa saboda abinda ta aikata, kuma yadda duniya ta riga ta san abinda Asiya ta yi babu namijin da zai so aurenta. Yadda iyayenta sukayi ta roƙon Gwamna shiyasa ya ji tausayinsu, ya musu wannan alfarmar akan zai auri Asiya dan ya rufa mata asiri...
An gama zanawa Asiya lalle tana jira ya bushe a cire Queen Bee ta gaya mata abinda ta gani yana yawo a social media.
"Baby kar ki damu, idan kika shiga gidan ki yi maganin shegiya" Queen Bee ta faÉ—a dan ta kwantar ma Asiya hankali
"Yanzu Ya Ubayd ma sai da aka ɓata masa suna"
"Shahidah dan Allah kar ki saka wannan a ranki. Bari kiga a É—aura auren nan, wallahi sai abinda kika ce a faÉ—a za'a faÉ—a"
Tunda ta bar office ɗin Ubayd ta sawa ranta indai ta shiga gidan Gwamna Saifuddeen Kachallah to sai inda ƙarfinta ya ƙare amma yadda ya rabata da masoyinta itama sai ta rabashi da kujerarsa.
Tun daga lokacin ta sake jikinta duk abinda akace tayi, tanayi.
***
Minti arba'in kenan da kiran Bilkisu da yai amma har yanzu bai ga idonta ba.
"Darling" ta faÉ—a lokacin da ta shigo É—akinsa fiskarta É—auke da murmushi.
"Sorry na jima, maganar aurenka ne ya riƙeni. Ka san cewa Hajiyan Saudiyya zata shigo gobe, yaushe rabonta da Nigeria. Ni inaga ma kamar jira dama take a min kishiya ta zo taron biki"
"Bilkisu please!"
"Idan akan abinda na faɗa ne to ka sani duk abinda zai ɗaga darajarka a idon mutane zan yi, saboda an kusa zaɓe"
"Ba sai kin ci zarafin iyayenta ba Bilkisu. Ya kamata ki san..."
"Idan akan wannan ka kirani, then excuse me, inada aikin yi"
"Ba wannan kaɗai bane" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa.
"Asiya zata zauna a gidanmu na da..."