Sashe 32
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina so ƙanwata ta zo ta tayani zama. Sannan ina son kawo Driver nawa na kaina"
"Mi ya samu Dreban da aka baki?"
Yai maganar yana tsareta da idanu.
"Na fi son wanda zan yarda dashi É—ari bisa É—ari"
"I see. Ki submitting CV É—insa a duba"
" Yayana ne, Ubanmu É—aya, akwai wani CV daya wuce wannan?"
"Ta ya zan yarda cewa wanda ki ka faÉ—a shi É—in za ki kawo?"
Ta ji zafin maganansa amma ta dake tace " ka iya sawa a mana DNA test da ni da shi"
Yai murmushin gefen baki yace " abu ne mai sauƙi ai"
"Sannan abu na gaba. Bana son kuɗin jini, kuɗin talakawa. Kasan yadda za ka yi ka cire kuɗin da ka zuba a account ɗina yau da rana, bana buƙatarsu"
Miƙewa yai yace " gudummawa ce da Ahalin Kachallah suka miki, idan ba kya buƙata ki tuntuɓi Hajiya Umma ki mata bayani"
"Zan iya kawo Sumayyan? ko itama sai da DNA test"
"Zasu iya zuwa" ya furta sannan ya wuce wani hanya wanda take ganin a nan É—akunan sashen suke.
Tana shiga É—aki ta kira numbar Yaya Bello. Yana nan teburin mai shayi ana rikici da shi akan kuÉ—i ta kira.
Daga wajen da yake yana ɗaukan kira ya fara cewa "gashi nan ai ƙanwata Matar Gwamna ke kira"
"Yaya Bello"
"Hello Asiya, Hello esselenci. Esselenci kina jina"
"Ina ji Yaya, ya kuke"
"Lafiya lau muke. Ya Gwamna?"
Asiya ta katse zancen da cewa "Yaya inada aiki da zan baka, idan babu matsala"
"Wallahi zan yi"
Lokacin data faɗa masa direbanta take so ya zama wani tsalle ya daka yana ihu. Yaya Bello ya girmeta da kusan shekaru shahuɗu amma bai damu da cewa ƙanwar bayansa zai dinga tuƙawa ba.
Shine babban ɗa namiji acikin 'ya'yan Ale Faruƙ amma kuma shine marar aikin yi walaƙantacce. Shaye-shaye ya lalata masa rayuwa. Lokacinda yake yaro shekara goma shabiyu zuwa shabiyar haka, ya taɓa halin ɓera, da abin ya ishi Ale sai ya kaishi wajen Gwani. Gwani ya dinga masa addu'a yana bashi ruwan rubutu har ya zo ya rabu da abun.
Daga baya daya bi wasu abokai suka tafi chan kudu leburanci shikenan ya lalace da shaye-shaye. Baya bin mata, dan akoda yaushe addu'ar Gwani Allah ya raba shi da sata da kuma zina.
A shekarar da Gwani ya rasu a shekaran ya dawo gida. Bai dawo da komai ba saboda komai ya tafi a shan abubuwan maye.
Ale ya masa aure ya buɗe masa shago ko zai nitsu amma inaa. Kafin wata shida komai ya ƙare a shagon, ita kuwa Amarya shekara ɗaya tayi da 'yan kwanaki iyayenta suka sa ya saketa saboda tunda aka kawota ko hannunta bai taɓa riƙewa ba.
Ale ya kaishi wajen wani abokinsa mai maganin gargajiya a duba shi ko bashida lafiya ne, amma akace lafiyarsa lau.
Ƙannensa maza biyu sun yi aure harda 'ya'ya, sannan suma kasuwancinsu ya fara bunƙasa tun lokacin da Ale ya yaye su daga kasuwancinsa, amma Yaya Bello kam sai zaman daba...
***
Asiya na aiki a laptop É—inta Sumayya ta shigo É—akin da sallama.
"Kai Anty na gaji" ta ajiye jaka ta faÉ—a kan gado
"Tun yanzu? Shekara huɗu zaki yi, idan kuma aka shiga yajin aiki ƙila kiyi biyar ko shida"
"Kai! Allah ya sawwaƙa"
"Welcome to the game sister, haka muma muka yita cika bakin nan, daga ƙarshe sai da muka ƙara wata biyar akan shekaru huɗun daya kamata muyi"
"Anty kin san me, wata a ajinmu tace tana son ƙawance dani, ta nuna min hoton da mukayi a wajen dinner ashe nima na zama celebrity"
"Ban yadda ba"
"Iye?"
"Ban yadda da ƙawancen nan ba. Duk wacce za ta shiga jikinki saboda ke ƙanwar Matar Gwamna ce ba ƙawa ce da zata ɗore ba. Sannan ina so ki sani cewa matsayina na Matar Gwamna na lokaci kaɗan ne"
Sumayya tayi saurin miƙewa zaune.
"Anty dan Allah kada kice min za ki bar gidan nan. Kwana biyu dana yi a gidan nan ban taɓa gani kin shiga sashen Gwamna ba, idan ya dawo ko..."
"Bana son gulma. Kada ki bari wani matsayi ya ruÉ—e ki dan ba mai É—orewa bane"
Sumayya ta riƙe baƙi tana kallon Asiya da hankalinta ke kan abinda take ta rubutawa a laptop ɗinta.
Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin aka yi, Sumayya ta je ta buɗe.
Da ta dawo ta miƙawa Asiya wani envelop tace Uwani ce ta kawo.
Asiya ta karɓi envelop ɗin ta yaga ta fito da wasiƙar ciki.
"Shegiyar mata wai office of the first lady, ko uban wa ya bata office oho"
"Anty minene?"
"Bilkisu Kachallah ke gayyatata taron gajiyayyu da naƙasassu da za ayi gobe Asabat a foundation ɗinta"
"Anty zaki je?"
"Idan ban je ba ai ta ci nasara a kaina"...
Tunda aka kawota bata taɓa fita ba, a ranan da ta yiwa Yaya Bello maganan zama Direbanta washegari ya niƙo garinsa ya taho.
Kiran Yaya Bello tayi a waya tace masa gobe za su fita za ta aiko Sumayya da key É—in mota ya duba lafiyar motar.
Washegari kuwa ƙarfe shaɗaya Asiya da Sumayya suka wuce wajen taro.
Lokacin da suka je an tanada mata waje na musamman kusa da Bilkisu Kachallah. Tana zama Bilkisu tace "ƙarfe goma aka fara taro, nan gaba ki duba agogonki da kyau"
"Ohh sorry! Kin san yau Excellency zai bar gidana, dole na kimtsa shi kafin na fito. Kin san ai yana jimawa a banɗaki idan zai yi wanka, da muka shiga tare kuwa na yi ƙoƙarin na dirzashi da kyau amma dana taɓa shi sai jikinsa ya ɗau mazari..."
"Shut up!" Bilkisu ta faɗa a fusace, bata san ma maganar ta fito da ƙarfi ba sai da ta ga wanda suke kusa da su na kallonta. Sai ta bige da kama hannun Asiya tana dariya kamar irin wasan nan take. Asiya ta yi murmushin nasara, yau duk ta inda Bilkisu Kachallah za ta fito tana nan dai dai da ita.
Kiran Bilkisu Kachallah da aka yi ta zo tayi bayani nan take naƙasassun wajen suka fara tafi suna kiran sunanta.
Ko da za su shigo hall É—in abin daya fara ba wa Asiya haushi shine UWAR MARAYU da aka rubuta a saman hoton Bilkisu Kachallah. Bilkisu ba ta yi kama da macen da za ta so talaka ba balle maraya amma da sannu za ta karya mata fiffiken da take furkawa da shi.
Maganan minti shabiyar tayi sannan ta ce zata kira 'yaruwa, ƙanwa, kuma abokiyar zamanta ta zo ta faɗi abu ɗaya ko biyu a wajen duba da cewa ita ɗin ma ta fito daga tsatson naƙasassu.
Asiya ta cizi leɓenta lokacin da Bilkisu Kachallah ta kirata da 'yar Kurma jikar maiƙusumbi.
" Hajiya Asiya Kachallah" MC É—in wata mata wacce bleaching ya gama koÉ—ar mata da fiska ta sake kiran Asiya a karo na biyu bayan Bilkisu ta koma ta zauna.
Dai dai zata tashi taji Bilkisu tace "maza aje a gaya musu yadda ake kula da naƙasassu"
Sallama Asiya tayi lokacin data karɓi mic a hannun MC. Jin an amsa ƙasa-ƙasa ya sa ta ƙara maimaita sallamar da muryarta mai kaifi, wannan karan suka amsa da ƙarfinsu.
"Barin baku wasu labarai masu daaaaɗiiiii" ta ja ƙarshen maganar tana juya hannunta. Nan da nan aka saka dariya
"Akwai wani yaro da aka haifeshi da ƙusumbi shekaru tamanin da biyar da suka wuce. Aka damƙa shi wajen wani malami dan yai karatu tun yana shekara shida haka. Wannan yaro yai karatu sosai a wajen Malaminsa dama wasu Malaman daban. Yai aure Allah ya azurta shi da 'ya'ya uku Maza. Wannan yaro mai ƙusumbi ɗinkin hula yake yana ciyar da iyalinsa da gumin hannunsa har Allah ya ɗau ransa. Sai dai kun san me? Kafin ya rasu yayi karatun ƙur'ani, ya ji haddan Ƙur'ani har mutane su ka rinƙa kiransa da Gwani. Wasu daga cikin ɗalibansa sun ce kafin Gwani ya rasu ya rubuta ƙur'ani daga farko har ƙarshe da ka sau ashirin da ɗaya wasu ma su kance sau talatin ne. Lokacin da Gwani ke ciwon ajali kafin a bashi abinci ya ci sai ya yi ƙoƙari ya rubuta ayoyin ƙur'ani a Allonsa kafin ya ɗanɗani abincin. Har ya koma ga Allah bai taɓa roƙo ba, bai taɓa zuwa maula wajen Attajirai ba.
"Akwai wata mace dana sani da aka haifa da lalurar kurmanta, aka mata aure, suka rabu da mijinta da 'ya ɗaya tsakaninsu. Wannan mata ta sake aure mijinta ya taimaka mata ta fara karatun yaƙi da jahilci. Ta koyi sana'ar ɗinki da saƙa, yanzu haka matar nan Allah ya rufa mata asiri tana ɗinki tana kuma saida kayan sanyi irinsu, Zoɓo, kunun Aya da sauransu.
"Akwai wani gurgu a ƙasan layinmu kullum idan zan wuce Islamiyya yana zaune a ƙofar gidansa yana gyaran takalmi , da Allah ya yassara masa har takalma ya saro na maza da mata yana saidawa, duka a ƙofar gidansa.
"Lokacin da nake bautar ƙasa a wani gidan talabijin akwai wata mata makauniya wacce ke gabatar da shiri na musamman dan wayae da kan al'umma akan mahimmancin ilimi wa naƙasassu. Inaga za ku tuna da Dr Hajiya Laraba Bakatsine wacce ta rasu farkon shekaran nan, ga wanda basu sani ba degree uku ta yi kuma duka da lalurar makanta.
"Abu na ƙarshe da zan faɗa shine, naƙasa ba lasisi bane na yin barace-barace ko maula. Ina so ku sani Naƙasassu na da damar yin kasuwanci ko sana'a, sannan su nemi ilimi kamar kowa. Ina fata Gwamnati za ta bawa naƙasassu damar yin kasuwanci d neman ilimi kamar kowa. Mu tashi lafiya"
Kafin ta kai kujerarta wani gurgu ya turo kekensa ya sha gabanta, idonsa fal da hawaye ya haɗe hannunsa biyu ya fara mata godiya, kan kace me, naƙasassu sun yanyameta suna mata godiya. Maganganunta sun taɓa naƙasassu da dama a wajen, wanda zuciyarsu ta kafe kuwa, sun sawa ransu cewa bara sana'a ce kuma ko me za a musu sai sun je Kudu sun yi sana'ar su.