← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 38

Sashe 11

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nagode Baba" abinda ya iya faÉ—a kenan

Alhaji Sani bai matsa da cigaba da maganar da su ke ba ganin SSK yana buƙatar hutu sai dai kafin su rabu ya jaddada ma sa cewa tabbas zai kai ma sa ziyara zuwa office ɗin sa gobe.

Bayan Gwamna ya bar Kachallah house kai tsaye gidansa ya wuce dan har yanzu ba su koma gidan Gwamnati ba saboda gyararraki da ake yi.

Bayan wannan dogon rana ba abunda ya ke buƙata irin bacci cikin kwanciyar rai amma yana isa falonsa ya iske Bilkisu tana zaman jiran sa.

"Excellency Darling" ta faÉ—a tana manna ma sa kiss a kumatu.

"You're just here on time, yanzu na gama parking kayanka. May be mu je ka gani ko akwai abubuwan da za ka buƙata"

"Parking?"

"Dont tell me ka manta jibi Asabar za mu koma Government house"

"An gama gyaran ne?" Gwamna ya faÉ—a yana zama a kan kujera

"Darling yaushe ka fara mantuwa ne. Jiya fa na ke gaya maka an gama gyaran gidan za mu iya shiga yanzu"

"Bilkisu ki miƙo min ruwa mai sanyi please"

Sai da ta ɗan tsaya kaman mai shirin shawara da zuciyarta kafin ta miƙe. Ya sani da a falon ƙasa su ke sai dai ta kira ma sa Hansa'u ko ɗaya daga cikin ma su yi mu su aiki.

Ko da ta kawo ruwan ba ta barshi ya sha da daÉ—in rai ba ta cigaba da maganar komawar su gidan Gwamnati.

"Hansa'u da Uwaji za su bimu, sauran za su zauna a nan tunda dai ba za a bar gidan kango ba"

Kallon da ya ke mata kallon ki barni na huta ne amma ita Bilkisu sam ba ta karanci hakan ba. Sai ma cewa da ta yi "ko akwai wanda ka ke so a tafi da su bayan su Hansa'un?"

Bai amsa ma ta ba, sai ma kauda zancen da yai da cewa "ina yarana?"

"Duk sun yi bacci. Mahira ma ta dawo yau da yamma"

Gwamna ya miƙe tsaye yana faɗin "sai da safe"...

***

"Ya Ubayd ina tsoro, mafarkin danayi jiya ya tsoratani sosai"

"Wani mafarki kenan?"

"Na yi mafarki wai..." sai kuma ta yi shiru. Ta ina za ta fara ce ma sa ta yi mafarkin marigayi Kakanta Gwani yana É—aura aurenta da Gwamna Saifudden Kachallah. This is absurd ai, ba abune da ya ke da daÉ—in faÉ—a ba. Balle ta san halin kayanta da shegen kishi.

"Ance ba kyau faÉ—in mummunan mafarki dan haka ka barshi kawai"

"Yau kuma?" Ya faɗa yana taɓe baki

"Mu bar zancen kawai. Ya maganan aikin kitchen É—in nan an saka sink É—in nan kuwa?"

"An gama Yallaɓiya. Kin matsu ko? Saura wata huɗu da kwana ɗaya tak"

Yana maganan ta ji ƙirjinta ya buga hakan ya sa ta yi saurin faɗin "Insha Allah" shima Ubayd ɗin ya maimaita kalmar.

Bayan sun gama hira da Ubayd ta shiga ɗaki ta iske Umma na duba wasu kulolin abinci. Umma na ganinta ta mata magana da hannu akan ta zo ta duba kulolin ko sun yi kyau. Asiya ta zauna tana dubasu tareda faɗin kulolin sun yi kalan 'yan ƙyauye.

"Umma ni ban san miyasa kike siyan kaya a wajen Laraba dillaliya ba. Ga kayanta tsada gashi ba wani kyau ne da su ba. Indai ni kika siyawa gara ki mayar mata dan ba su min ba" ta ƙarisa maganar tana turo baki

Umma ta taɓe baki tana kallon Asiya.

"Allah Umma ko kin saka a kayana kyautar da shi zan yi, dan wannan kulan ba zai zauna a dining table É—in gidana ba ehe"

Umma ta yi murmushi sannan ta mata bayani akan gudummawar da ta ke son bayarwa 'yar maƙotan su da za a aurar ne nan da sati biyu.

"Yanzu na ji batu Umma na" ta yi maganar tana rungume Umman ta...

Yau ma dai mafarkin data yi ne ya tasheta daga bacci, abin mamaki irin mafarkin jiya ne sai dai wannan karan Gwani ya haɗa hannunta dana Gwamna yana ma ta nasiha akan mahimmancin haƙuri da kuma yarda da juna a rayuwar aure.

Ba ta cika yin mafarki ba hakan ya sa a mafiya lokuta idan ta yi mafarki za ka ga abun yanada nasaba da rayuwarta.

"Allah ka sa wannan mafarki ba gaskiya ba ne. Ubayd na ke so ya Allah" ta faÉ—a a hankali tareda sauke ajiyar zuciya sannan ta koma ta kwanta sai dai bacci ya gagareta...

***

Asiya ta fito daga kitchen a fusace saboda ruwan wankanta da aka juye.

"Wani marar imanin ne ya juye min ruwana?"

"Waye a banɗakin nan ne?" Ta faɗa tana ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin kaman za ta ɓalla shi.

"Mutum ya tashi da Asuba ya saka ruwa azo a juye ma sa, a hakan ba za a saka masa wani ba. Koma waye yau sai ya biyani ruwana"

Kusan minti uku sannan Hindatu ta buɗe ƙofa ta fito ɗaure da zani.

"Miye ne kike ta buga ƙofa kamar wata sabuwar mahaukaciya"

"Ke ce mahaukaciyar ai. Na saka ruwa a heater kin zo kin juye min saboda tsabar iya shege"

"Dama akwai wanda ya kafa dokar idan kana gidan ubanka sai ka nemi izinin Agola kafin ka yi amfani da abun gidan ne?"

Asiya ta buɗe baki za ta yi magana amma ta fasa saboda ɓata lokaci ne biyewa Hindatu da sassafen nan. Ba ta san mi ta tsarewa wannan Hindatun ba. Ta rasa kishi ta ke da ita ko kuma haka kawai tsantsar ƙiyayya ce.

Banɗakin ta shige ba tareda ta tankawa Hindatun ba, ta fito da bokiti ta je ta ɗebo ruwa mai sanyi. Kafin ta ce za ta haɗa wuta ta ɗaura wani ruwan wankan lokaci zai tafi dan haka kawai ta daure ta zo ta yi wanka da ruwan sanyi. Tana fitowa kuwa da gudu ta je ta shige ɗakin su ta kullo ƙofar da ƙarfi

Umma ta kalleta ta ce lafiya? da hannu

"Sanyi Umma" ta amsa tana ƙarisawa wajen jakar kayan kwalliyarta.

Ƙarfe bakwai saura kwata Asiya ta fito daga gidansu sanye da wandon jeans blue, baƙin riga sai farin blazer jacket da ta saka sannan ta yane kanta da light blue gyale. Keke ta nema ta wuce ma'aikatar su.

Tana zuwa office ta fara duba tambayoyin da ta tsara wanda jiya da daddare MD ya kirata ya ce ta ƙara da tambaya ɗaya wato miyasa Gwamna ya naɗa tsohon Kwamishinan ayyuka Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa.

Kusan komai ya tafi daidai. Zuwa ƙarfe tara Asiya da CY su ka kama hanya zuwa gidan Gwamnati.

Lokacin da su ka zo an ajiye su a waje na musamman kafin Gwamna ya fito.

A cikin ofishin Gwamna kuwa COS ne ya ke ganawa da Gwamna.

"Your excellency ina so ka dai sake tunani akan wannan lamari, yanke wannan allowance É—in dai dai ya ke da fushin cabinet members É—inka"

"Wani ɓangare ne cikin magana na baka gane ba?. Kana sauraron kanka kuwa?. For God's sake bayan ɗimbin ayyukan da ke gaban mu har kuna da zuciyar da za ku tambayi wani allowance"

"Excellency wannan allowance É—in tun kafin administration É—inka ake bayarwa idan ka ce ba za ka cigaba da bayarwa ba za a samu matsala"

"Look Mr Damana. Ba zansa hannu a wannan ɗimbin kuɗin ba bayan munada abubuwa dayawa a gaban mu. Ka ƙara jaddadawa Mr Paul cewa bazan biya kuɗin nan ba. Now please leave my office"

COS ya miƙe jiki a sanyaye.

Bayan fitan COS Gwamna ya kira Sakatare

"Malam Baffayo ka haɗa meeting da Contractors ɗin nan ƙarfe goma"

Sakatare yai saurin cewa "Excellency akwai hiran da za ka yi da 'yar jarida daga Hill TV ƙarfe goma, sun ma iso lokaci su ke jira"

Har zai ce a ce su dawo wani lokaci sai kuma ya fasa yace ya maida meeting ɗin sa da Contractors ɗin ƙarfe goma da rabi saboda minti talatin kacal zai yi da su Asiya.

Asiya na tsaye tana yiwa CY magana Gwamna da tawagarsa su ka iso.

Ganin CY yayi saurin miƙewa ya sata juyawa ba shiri.

"Your excellency Sir" CY ya faɗa yana murmushi. SSK ya miƙa ma sa hannu CY yai saurin saka hannu biyu ya damƙi hannun SSK yana faɗin " myself Clement Yohanna"

"Welcome Mr Yohanna" sannan ya miƙawa Sunusi hannu dreban daya kawo su Asiya.

"Allah ya ja zamanin Gwamna. Allah ya kare ka, Ubangiji ya maka jagora" Sunusi ya dinga sunbatu kamar zai haÉ—iye Gwamna saboda farin cikin sun yi musabaha da Gwamna SSK.

Tunda Asiya ta juya ta ganshi bakinta ya kafe. Yadda kasan an tura mata dunƙulen Auduga a maƙoƙoro haka magananta ya toshe ya ƙi fitowa. Sau ɗaya su ka haɗa ido amma gaba ɗaya ta rasa nitsuwarta. Kaifin idanunsa gareta sun karya ma ta duk wata laka da ke jikinta. Abin mamaki wai ita Asiya-Shahidah da ta ke iƙirarin ba mutumin da ba za ta iya magana a gabansa ba sai gashi kusan minti biyu da zuwan Gwamna wajen ta kasa ko da gyaran murya ne. A baya duk lokacin da aka yi maganar ƙwarjinin SSK ƙaryatawa ta ke yi sai gashi yau ta gani a zahiri.

Bayan Gwamna ya gama darawa bisa surutun Sunusi da CY sannan ya maida hankalinsa ga Asiya.

*"Asya?"* Ya kira sunanta da sigar tambaya

Ji tayi jiri yana shirin kwasarta a wajen saboda irin yadda taji wani abu ya ratsa jijiyoyin jikinta lokaci guda. Taya ma zai iya kiran sunanta da daÉ—i haka?

Ta yi kusan sakan goma kafin ta iya haɗiye koma minene daya toshe mata maƙoƙoro ta ɗan yi ƙaramar gyaran murya sannan ta ce " your excellency, Asiya Shahida Faruƙ Baba"

"Of course. The famous Asya ta tashar Hill tv"

"Sit" ya faÉ—a yana nuna mu su kujera. Sai da ya zauna kafin suma su ka zauna

"Wannan location yayi ko za a chanja wani?"

CY yai caraf ya amsa da cewa "yayi your excellency. Barin saita camera sai a fara É—aukan hiran"

Da rawar jiki CY ya miƙe ya fara saita camera yayinda Asiya ta sunkuyar da kanta ƙasa tanajin kamar idanun Gwamna yana yawo a duk ilahirin jikinta. Sai yanzu ta yi dana sani da hijabi ta saka ba gyale ba.
Chapter 11 · 0% Book details