← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 38

Sashe 23

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Gambo tayi yayinta ta ƙare, lokacin maganinta ya dena ci, a lokacin ne kuma Ale Faruƙ ya lalubo musu wata mata mai suna Yawo. Daga chan wani ƙauye ta fito wanda ake yawan cewa ƙauyen akwai mayu a wajen. Ba budurwa bace dan aurenta bakwai amma tacewa Ale Faruƙ aurenta biyu. A rumfarsa suka haɗu ta zo siyayya, farar fatarta ya ja hankalinsa.

Sati biyu da tarewarta Ale Faruƙ ya fara ciwo. Idan ya tashi da safe sai yaji duk jikinsa na masa ciwo musamman hannu da ƙafafuwansa. Tun yana iya fita kasuwa har ya koma zaman gida saboda ko bai fita ba haka kawai jikinsa sai ya dinga ciwo. Ya je Asibiti an bashi maganin ciwon jiki amma duk da haka abun ba sauƙi.

Ana hakane kuwa biyu daga cikin 'ya'yansa suka rasu mace da namiji dukkansu 'yan ƙasa da shekaru goma. Abin duniya yabi ya isheshi, rashin fita kasuwa kamar yadda ya saba duk ya saka shi damuwa dan gani yake baza a kula masa da dukiyarsa kamar yadda ya kamata ba...

A gindin wata bishiyar giginya wasu mata guda uku suka haɗu a talatainin dare. Cikon ta huɗunsu ta taho tana basu haƙuri akan dalilin rashin zuwanta taron nasu da wuri.

"Ni kam Yawo keda kike da nisa ya akayi kika rigani zuwa?" Wacce ta zo yanzu tayi tambayar tana kallon farar cikinsu wacce duk da kasancewar dare ne sosai farin fiskarta na haskawa.

Yawo tayi dariya tace "ai dokina shegen gudu gareshi. Gashi chan na É—aure shi a wancan bishiyar"

Matar ta juya ta kalli inda Yawo ta nuna mata sannan ta ƙyaƙyale da dariya tace "ashe zaki bani aronsa idan zan je taron mutanenmu da za ayi na ƙasa"

"A ina za ayi taron?" Wata tsohuwa tukuf a cikinsu ta tambaya.

"Wancan shekaran anyi a Kaduna ne amma wannnan shekaran a Ogbomosho za ayi"

"Kai yayi nisa ba zan je ba" tsohuwar ta faÉ—a tana lashe baki ganin naman da aka kawo musu wacce jaririyar Gambo ce da ko wata bata cika ba.

"Kai! Yawo gaskiya aurenki da Ale Faruƙ akwai daɗi. Kullum cikin ƙoshi muke"

Yawo ta baza haƙora tana dariya tace " nan gaba naman wancan 'yarsa daya fi so zan kawo, nasan ba ƙaramin daɗi za ta yi ba"

Dukkansu huÉ—un suka bushe da dariya marar daÉ—in ji.

Washegari Asma'u 'yar Gambo ta rasu. 'Yarta ta biyu kenan a gidan Ale.

Da yamma Mama da Asiya da matar Baffa Malam suka zo ta'aziyya gidan.

Suna falon Gambo Yawo ta shigo gaishe da Mama. Suna haÉ—a ido da Asiya ta fara mata murmushi. Asiya ta ce " Maman Rabi'u ga wadda ta cinye miki Asma'u" gaba É—aya sai suka maida dubansu ga Yawo da Asiyar ke nunawa.

Yawo ta kama salati tana salallami harda fashewa da kuka.

Mama ta kwaɓi bakin Asiya tace "bana son shegen surutu Asiya. A ina kika ji wannan banzar maganar?"

Asiya ta tura baki tace "in ta cinye duka 'ya'yan Baba ai shikenan, nikam bazata iya cinyeni ba"

Mama ta ranƙwasheta tace ta rufe musu baki. Sannan ta shiga bawa Yawo haƙuri.

Maganar ta tsaya a ran Mama shiyasa da suka koma gida tace zata faÉ—awa Gwani idan ya dawo daga tafiya.

Ranan da dokin Yawo ya je Ogbomosho washegari Ale Faruƙ ya tashi ko yatsarsa baya iya ɗagawa. Yadda ka san wanda jikinsa ya shanye haka yake kwance a sanƙare ko'ina yana masa ciwo kamar anyita dukansa da taɓarya.

Bayan kwana huÉ—u da rasuwan Asma'u Gwani ya dawo. Da ya huta Mama ta gaya masa abinda Asiya ta faÉ—a, tareda faÉ—a masa cewa ranan da suka dawo, da dare Asiya ta dinga sunbatu cikin baccinta tana cewa babu wanda zai iya cin namanta.

Gwani ya ɗau Allo ya rubuta ayoyin shifa ya wanke da ruwan zamzam ya zuba a gora ya miƙe da kansa ya wuce gidan ɗansa.

Lokacin daya isa gidan kai tsaye sashin Ale ya shiga inda Ale Faruƙ ke shimfiɗe a kan tabarma a tsakiyar falonsa. Fulani da ɗansa Bello wanda shine babban ɗansa namiji ya gani a kusa dashi suna ƙoƙarin bashi kunu.

"Ya jikin nasa?"

"Yau kam Malam ko hannunsa ya kasa É—agawa" Fulani ta amsa cike da tausayawa mijinta wanda duk yadda yake tana sonsa a haka.

Bello ya taimakawa Gwani wajen bawa Ale ruwan rubutu. Bayan ya sha, Gwani ya karanto addu'o'i ya tofa a hannunsa ya shafa masa a goshi, hannu da ƙafafuwansa. Da yamma ma yazo yai masa haka, washegari ma ya sake zuwa yai masa haka safe da yamma.

A rana ta uku kuwa da Yawo ta tashi hawa doki zata je majalisansu doki ya ƙi tashi, tayi tayi amma inaa ya ƙi ko matsawa gefe hakan ya sa ta haƙura da ɗaukansa. Da ta isa majalisa ta kai ƙorafin abinda ya faru wajen shugabarsu tsohuwa Ayya. Ayya tace ai mahaifin Ale Faruƙ ne ke shirin ɓata musu aiki kada ta bari ya sake zuwa wajensa. Naman Asiya ma da suke son ɗauka shima abin ya gagara shiyasa suka koma kan ƙanwarta Farida 'yar Halime wacce nan da kwana uku zasuyi abincin dare da ita.

Washegari ya kama kwanan Yawo dan haka ita ce ta kasa ta tsare a gefen Ale Faruƙ. Ƙarfe tara na safe sai ga Gwani ya zo yiwa Ale addu'a. Yawo ta garƙame falon da kwaɗo ta zauna a dakalin ƙofar shiga falon, yana zuwa tace masa Ale na barci yace kar a tashe shi.

Gwani yace ta buɗe masa ƙofa ya shiga ya dubashi ba zai tashe shi ba. Yawo ta tura baki tace sai dai ya dawo wani lokacin. Yadda ta dage ba zai shiga ba ya sa ya juya ya tafi, cikin ransa yana tunanin tabbas maganar Asiya gaskiya ce. Da yamma tareda ɗansa Malam suka zo, nan ma a ƙofar falon suka tarar da Yawo tana zaune daram kamar da safe. Wannan karan sai da Iyani da Fulani suka leƙo suna cewa Yawo ta buɗewa Gwani ƙofa domin tunda ya fara yiwa Ale addu'a suka fara ganin sauƙi.

Tana cikin magana Malam ya fito da wata dorina ya tsura mata a jiki yana faɗin "ƙarya kike la'ananniya, ƙarya kike Mayya"

Yawo ta saka ihu tana kuka.

"Kin cinye masa 'ya'ya za ki cinyeshi ko? Asirinki ya tonu" ya cigaba da zaneta. Ƙoƙarin gudu take amma Gwani da sauran Matan da yaran Ale kusan biyar sun tare wajen sun hanata gudu. Bello ma daya shigo bada jimawa ba itace ya sunkuco ya shiga taya Baffan nasa dukan Yawo.

Sai da Gwani ya tsaida su kafin suka dena dukanta. Ya tambayeta ta faÉ—a musu gaskiya. Yawo baki da hanci duk jini ta fara cewa ta tuba a yafeta.

Baffa Malam ya daka mata tsawa hakan yasa ta fara faÉ—an abinda tayi tace da gaske ne ita ta cinye yara uku a gidan amma Ale FaruÆ™ doki take da shi bawai cinyeshi zata yi ba.

Tabawa da ke gefe tayo kan Yawo da gudu ta fara dukanta tana yaguni. "Shegiya É—an nawa shine doki, É—an nawa kika mayar doki"

Da ƙyar Baffa Malam da Bello suka janyeta akan Yawo.

Gwani yace su ɗaureta kar wanda ya sake taɓata amma ina, samarin anguwa sukace basu yarda ba aka fita da Yawo ana bugu. Lokacin data suma aka fara ƙoƙarin ƙonata saiga wata tsohuwa ta ratsa cikin mutane ta zo ta taɓa Yawo shikenan ita da Yawo suka ɓace. Mutane kowa yai ta kansa sai 'yan tsiraru da suke da ƙarfin zuciya suka tsaya suna ihu suna faɗin duk ranan da suka kama Yawo ko wani maye ko mayya a garin ƙonashi za suyi.

Kwana uku da aka cigaba da yiwa Ale FaruÆ™ addu'a ya warke sarai kamar ba shi ba. Lokacin da yaji labarin cewa Asiya ce ta fara gane cewa Yawo Mayya ce hakan ya sa shi dagewa Gwani akan sai dai Asiya ta dawo gidansa da zama. Gwani bai musa ba tunda dai 'yarsa ce ya dai jaddada masa akan koyaushe Asiya ta dinga zuwa karatu.

Bayan Yawo sai da Ale Faruƙ yai shekaru huɗu kafin ya ƙara wani auren.

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

11

Dr Saifuddeen Sa'ad Kachallah saurayi ne mai kimanin shekaru ashirin da bakwai a duniya. A rana ta farko daya shigo jami'ar Congo a matsayin malami a ranan ƙaddararsa ta haɗu da ta Misturah Sulayman Adeyemi.

Da ya gama duk abinda zaiyi a ranan sai ya tattara kayansa ya wuce wajen motarsa. Ishirwa yake ji hakan ya sa shi wucewa wani kiosk da ake saida kayan masarufi da ke kusa da shi.

Yace da yarinyar da ke tsaye a shagon ta bashi ruwa mai sanyi na gora, yarinyar tace babu sai dai na leda. Saifddeen ya É—an gyatsine fiska sannan ya ce "ok kawo"

Yarinyar ta miƙa masa ruwa guda biyu a leda, lokacin ne kuma wata budurwa baƙa ta iso kiosk ɗin ta ajiye litattafanta akan kantan wajen tana huci tace "Abeg Bisi give me cold water"

Ya kalli budurwar da tayi maganar. Baƙa ce amma ba sosai ba tana da ɗan jiki amma ba zaka kirata ƙatuwa ba. Ɗan ƙaramin mayafin data yafa ta cire ta fara fiffita dashi saboda yadda take haɗa uban zufa, da gani ta sha tafiya cikin rana.

"Sista Mistura e take ye easy"

"Omo iya ko easy oo, Professor Badmus fe pawa, wahala re ti po"

Saifuddeen ya kauda kansa daga kallon budurwar ya miƙawa mai shagon naira ɗari biyu.

"Ha! Oga i no get change oo"

Ta kalli budurwar tace " abi Sista Misturah e ni change ke bami se?"

"E lo?"

"200"

"Haa! Kilo ra?"

"Omi meji"

Saifuddeen ya katse hiransu da cewa " i'll come back for it tomorrow"

"Ok Sir"

Har ya juya ya fara tafiya sai ya dawo. Ba lallai ya tuna da chanjin ba gara kawai ya sayi wani abin ya bar mata sauran.

Bayan ta miƙa masa coke mai sanyi daya buƙata yace ya yafe mata sauran chanjin.

"Ode ni Bobo yi"

Budurwar ta furta a fili. Suna haÉ—a ido da Saifuddeen tayi saurin kauda kai dan gani tayi kaman ya ji abinda tace.
Chapter 23 · 0% Book details