Sashe 25
Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin daya faɗawa Misturah hukuncin da aka yanke masa ranta ya ɓaci sosai har take ce masa dama halinsu kenan 'yan arewa, gashi tun bai aureta ba yana mata maganar kishiya. Sai dai soyayyar Saifuddeen ta rufe mata ido shiyasa ta amince zata zo gidansa a matarsa ta biyu.
Wata ɗaya da rabi Bilkisu ta shigo Nigeria, tazo ta tarar da tsarin da aka shirya mata. Za ayi bikinta da Saifuddeen nan da watanni biyu sannan za ayi na Misturah da Saifuddeen wata bakwai bayan aurensu lokacin Misturah ta gama bautan ƙasa.
Da soyayyar Saifuddeen ta taso kuma tun kafin ta tafi jami'a ta riga ta sanar da mahaifinta cewa idan ya haÉ—a aurenta da wani ba Saifuddeen ba bazata aure shi ba.
Lokacin data tsara rayuwar aurenta bata tsara cewa za tayi tareda wata bare ba. Ita da Saifuddeen za su gina rayuwarsu kuma babu wacce ta isa ta shiga tsakaninsu.
Sati biyu bayan ta iso Nigeria tasa aka fara yiwa Misturah transfer daga inda take bautar ƙasa kusa da Jahar Congo zuwa chan kudu.
Bata taɓa ganin Misturah ba sai ranan data je gidansu ta kai mata letan relocation ɗinta tareda kashedin duk ranan data sake shigowa Congo saita sa an yankata sannan idan har bata sa an kashe maganar aurensu da Saifuddeen ba zata sa a kashe Iya Bola da iyalenta, ba nan ta tsaya ba har Akure tace za ta je tasa a ƙona family house ɗinsu da duk wanda ke ciki.
Dama anacewa Yarabawa da tsoro. Tuni Iya Bola da Sikiru suka shiga bata haƙuri yayinda Misturah ta riƙe takardan da aka miƙa mata tana furzar da numfashi mai zafi...
Ƙila Saifuddeen ba zai taɓa sanin dalilin tafiyar Misturah ba domin ranan daya je hira gidansu wasiƙarta Iya Bola ta bashi inda a wasiƙar Misturah ta bayyana masa cewa ba zata iya zuwa gidansa a ta biyu ba. Daren ranan duk yadda ya daure sai da yai hawaye saboda Misturah itace macen daya fara so a rayuwarsa. Bai nemeta ba kuma har bayan ya auri Bilkisu bai nemi inda Misturah take ba saboda shi mutum ne da baya son takurawa ɗanuwansa. Duk da yana sonta sosai amma hakan ba zai sa shi tursasa mata ba. Sai da shekaru suka ja kafin watarana daya haɗu da wata ƙawar Misturah ta gaya masa cewa Misturah tayi aure a Lagos.
***
Tarihin gidan Kachallah ya samo asali daga ainihin wanɗanda suka kafa garin Congo. Lokacin yaƙe-yaƙe da Jihadi duka sunan gidan na nan. Sunada alaƙa mai ƙarfi da gidan Sarauta dan ko yau wani ya fito daga tsatson Kachallah yace zai zama Sarki babu wanda zai ja dashi dan kusan shekaru ɗari uku da suka wuce anyi Sarki Kachallah a garin wanda yai mulki na shekaru shabakwai.
Alhaji Habu Kachallah tareda matarsa Khadija wacce yanzu 'ya'ya da jikoki ke kiranta da Hajiya Dadda sun haifi 'ya'ya shida tare. Mariya Kachallah itace ta farko wacce yanzu ita da mijinta da 'ya'yanta suke zaune a Saudiyya, dan aƙalla yanzu zata kai shekaru arba'in a Saudiyya. Na biyun shine Sani Kachallah sannan Fatima Kachallah wacce ta jima da rasuwa amma ta bar 'ya'ya uku a duniya. Aminatu Kachallah wacce kowa ke kira da Hajiya Umma ta shekara arba'in da biyu da mijinta kafin rasuwarsa kuma Allah bai bata haihuwa ba sai dai ita ta raini 'ya'yan Yayarta Fatima wato Aisha, Abdullahi da Umar. Na biyar ɗinsu shine Sa'ad Kachallah sannan Hauwa Kachallah.
Alhaji Sani Kachallah ya auri mata biyu. Ta farkon Hajiya Maryam ta rasu ta barshi da 'ya'ya biyu Fatima Batula da Aminatu. Yayinda matarsa ta yanzu Hajiya Aisha ta haifa masa Rufaidah, Bilkisu, Saudah, Khadija da kuma Halima.
Sa'ad Kachallah a jami'ar Dares Salaam ta ƙasar Tanzania ya haɗu da Aysha Ali Jallow lokacin yaje wani conference ita kuma tana ajin ƙarshe a jami'ar. A wajen conference ɗin sau uku tana ɗaga hannu tayi tambaya hakan ne ya saka ya shaida fiskarta har yaji ta burgeshi. Daga baya da aka gama taron ya nemi sanin ko ita wacece kuma bai sha wahala ba saboda ita ɗin ɗaliba ce mai ƙwazo da tayi suna a jami'ar.
Kaman wasa ya mata tayin soyayyarsa ranan farko daya je wajenta, amsar da zai fito daga bakinta shine " I love Nigeria" daga haka bata ƙara da cewa komai ba hakan ya sashi tunanin ko bai mata bane. Wata ɗaya da komawarsa London ya samu wasiƙarta inda take cewa 'yar fulanin Gambia zata je gida idan da gaske yake ya je ya samu mahaifinta amma ya shirya yaƙi da danginta duk da ma ta san 'yan Nigeria jarumai ne.
Ousmana Jallow babban mutum ne a ƙasar Gambia, Shanu da Raƙuma da Allah ya azurta masa shi kansa ba zai iya lissafta adadinsu ba. Bafulatani ne mai riƙo da al'ada fiyema da addini wani lokaci. 'Ya'yansa uku ne maza Aodullahe Jallow, muhammadou Jallow da kuma Ali Jallow. Gidansa ba a auren bare hakan ya sa yisu-yisu fulanin yankin kawai suke aure. Fulanin Senegal, Cameroon, Niger ko Nigeria duk bare ne a wajensa.
ya riga ya shirya haɗa auren jikarsa Aysha da kuma Boubacar ɗan Aodullahe Jallow, jira kawai yake ta ƙarisa bokon da ubanta ya sakata dole tayi sannan ayi biki. Fiqhu da psychology take karanta amma Fiqhun kawai aka gayawa Alhaji Ousmana shiyasa ya amince da karatun ba dan ya so ba sai dan yana son Ali sosai.
Yaƙi ne kawai bai tashi ba lokacin da magabatan Sa'ad Kachallah suka zo neman auren Aysha Jallow. Sannan ita Ayshar ta nuna Sa'ad take so Mahaifinta kuma ya goya mata baya tunda a cewarsa bai san da maganar za a haɗa 'yarsa da Boubacar ba.
Cikin 'ya'yan Ousmana Jallow Ali ne yai boko mai zurfi dan alokacin ma ya haɗa Phd ɗinsa a ɓangaren Economics.
Abu dai ta kai ta kawo saida Ousmana Jallow yace ya cire hannunsa a lamarin Ali da iyalinsa, yayi duk abinda ya so.
Ali Jallow riƙaƙƙen ɗan boko ne da ko kaɗan baya so a tauye hakkin wani, shiyasa ma da ya nuna sai tilon 'yarsa tayi boko bai ji shayin ko mahaifinsa zai yarda ko ba zai yarda ba. 'Ya'ya biyu ya haifa, namijin ƙanin Aysha ya rasu tun yana watanni kaɗan da haihuwa.
Ali bai damu ba da 'yan uwansa suka ja baya da shi. Sanda magabatan Sa'ad suka dawo ya sa bikinsu nanda watanni huÉ—u lokacin Aysha ta gama karatunta.
Lokacin da akayi bikin abokanansa da 'yanuwan matarsa ne kawai suka shaida amma nashi 'yanuwan ba wanda yazo. Ousmana Jallow ya yi alƙawarin fishi da duk wanda yaje bikin.
Haka akayi biki Amarya da angonta suka wuce Nigeria. Bikin nasu da watanni shida Ali Jallow da matarsa sukayi hatsarin jirgin sama lokacin zasu koma ƙasar America saboda aiki da aka bashi a United Nation (majalisar ɗinke duniya).
Labarin yazo wa Aysha daidai tana laulayi mai tsanani hakan yasa ta birkice sosai dan soyayyar uba da 'ya dake tsakaninta da mahaifinta ba kaman na sauran 'yanuwan mahaifinta Fulani bane. Mahaifinta zai zauna da ita suyi taɗi, ya saurari matsalarta ya bata shawara ba wai ya tursasa ta ba. Mahaifinta tamkar babban abokinta ne dan shaƙuwarsu da shi ta fi ta mahaifiyarta.
Kaman baki wata biyu bayan mutuwar Ali Jallow da matarsa Sa'ad Kachallah yai hatsari ya rasu yana hanyarsa ta zuwa airport zai je London. Wannan mutuwar ta girgiza Aysha matuƙa dan sai data koma tamkar wata zararriya. Cikinta na wata shida alokacin amma har ranan data haihu cikin ciwo take. Lokacin da ake nema mata magani ne wani malami yace ko kaɗan kar a bari ta bar gidan dan sammu ne a kanta, idan suka bari ta fita ba zasu sake ganinta ba. Kullum cikin tsaronta ake kuma Alhamdulillahi maganin da ake bata ya sa bata samu ta gudun ba.
Ba ayi sunan Saifuddeen ba ta rasu hakan yasa Saifuddeen Kachallah bai san iyayensa ba sai a hoto da kuma bidiyon da akayi na biki dana wasu tarurruka da mahaifinsa ya halarta lokacin yana raye.
Sunyi mamaki matuƙa da babu ko ɗaya cikin 'yanuwan Aysha da ya zo bayan an aika musu rasuwarta, infact sharesu suka yi kamar ba alaƙar dake tsakaninsu.
A ɓangaren Boubacar Jallow kuma ya kaɗu matuƙa da ya ji mutuwar Aysha. Shi ya saka a kashe Sa'ad sannan a hana Aysha zaman Nigeria, sannan shi ya sanar da Ousmana Jallow cewa Aysha da ɗan data haifa sun mutu dan shine ya karɓo wasiƙar da aka rubuto.
Kasancewar suna zargin sammun da aka yiwa Aysha daga 'yanuwanta ne shiyasa tun Alhaji Habu Kachallah na da rai ya hana a kai Saifudden wajen 'yanuwan mahaifiyarsa.
Rashin haihuwar ɗa namiji ya saka Alhaji Sani Kachallah ya ɗaura duk wata soyayyarsa akan Saifuddeen. Shi ya zaɓa mishi makarantar da zai je da abinda zai karanta wato political science inda bayan Saifuddeen yaje chan ne ya ɗauki major biyu wato Communication and Political Science a postgrad kuma yai History and International relation.
Saifuddeen ya fara koyarwa a jami'ar Congo har ya kai matsayin Professor yana shekaru talatin da biyar a duniya. Yayi Rector na Congo Polytechnic na shekara ɗaya da rabi har lokacin kuma yana koyarwa a Jami'a kafin Alhaji Sani yasa a bashi Kwamishinan ayyuka na jahar daga nan kuma ya jawo shi cikin siyasa tsundum inda rana tsaka yace masa "congratulations Saifu, kaine mataimakin Gwamna na jihar nan" ya yi maganar tun ma ba a fara maganar zaɓe ba sai gashi watanni kaɗan bayan haka Saifuddeen Kachallah ya tsinci kansa wajen yawon kamfen har kuma a kwana a tashi ya tsinci kansa a mataimakin Gwamna, sannan yanzu alƙalamin ƙaddararsa ta juya, ya wayi gari shine Gwamnan jihar Congo...
*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....
*©Azizat Hamza*
wattpad Azi_zat
Bismillahir Rahmanir Rahim
Book one
12
*GUZURIN TAFIYA*
"Asiya....Asiya"
Juyowa tayi ta kalli Mama ba tareda ta amsa mata ba.
"Ba za ki je ki gaida Baban naki ba. Sau biyu yana aikowa wai kije"
"Mama zan je gobe, na gaji"
"Ba abinda kika yi tunda kika zo gidan nan sai kuka. An gaya miki kuka na maganin matsala ne. Tashi maza ki shirya ki je ki gaishe shi kafin Magariba ta ƙariso"
"Mama ba zan iya fita yanzu ba. Dan Allah ki bari sai gobe"