← Book details Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 38

Sashe 21

Matar Gwamna Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wani madaidaicin gida kuwa wata budurwa ce ke aikin wanke-wanke. Kwanukan yawa garesu, kuma yawancin su robobi ne madaidaita hakan zai sa ka kira su da kwanukan saida abinci.

Daga yadda budurwar ta duƙa tana wanke-wanken wani yaro wanda ba zai wuce shekaru goma ba ya ɗira ma ta dundu a baya. Budurwar ta juyo a zabure tana zare ido.

"Kurma ki je inji Mama" ya faÉ—a yana nuna mata dai dai barandar da É—akuna uku su ke jere reras.

Maimakon ta ɓata rai da abinda ya mata sai ta masa murmushi. Ta goge hannunta ajikin zaninta ta wuce ɗakin Mama Asabe.

Tana ɗaga labulen ɗakin sai da ƙirjin Mama Asabe ya buga saboda ta ɗauka mijinta Malam ne. Ganin Kurma ce ya sa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.

Cinikin da su ka yi da safe da kuma na rana ta ke irgawa.

"Yawwa Kurma zo ki je ki auno min shinkafar gobe wanda ya rage ba zai kai ba"

Ta ƙarisa maganar tana miƙa mata wani dunƙulen kuɗi da ta ajiye a gefe.

Bayan da Kurma ta karɓi kuɗin a hannunta ta cigaba da yi ma ta bayani da hannu ta yadda za ta gane. Tun tana shekara huɗu aka kawo mata ita kuma cikin shekaru goma ba abinda ba ta iya ba a yaren kurame.

Yadda ta jaddada ma ta cewa a rumfar Ale Faruƙ ta ke so ta siyo ma ta shinkafar hakan ya sa ta yi saurin zuwa ta ƙarisa wanke wanken da ta ke yi dan daga gidan su zuwa rumfar Ale Faruƙ aƙalla sai ta yi tafiyar minti shabiyar zuwa ishirin.

Lokacin da za ta fita daga gidan ne ta ci karo da Malam a zaure. Ta É—an risina ta gaida shi kafin ta wuce.

Malam Sabo Yayan Mahaifinta ne. Bayan rasuwan mahaifiyarta lokacin tana watanni bakwai da haihuwa Mahaifinta Malam Inusa bai ƙara aure ba har Allah ya ɗauki ran sa shekaru uku bayan rasuwan matar sa. A wajen Inna Talatu Zainab kurma take tun rasuwan mahaifiyarta amma bayan rasuwan Malam Inusa, Yayansa Sabo ya karɓota ya kawota wa matar sa Asabe. Da niyyar zai ɗauki nauyin marainiyya ya karɓeta amma ba wannan ne gaban sa ba irin gadon gona da gida da ƙanin sa ya bari. Ba ayi shekaru biyar ba ya cinye komai, ya siyar da gida ya siyar da gonan duka sun bi ruwa babu ko ɗaya yanzu.

'Ya'yan Mama Asabe Maza huɗu ne shiyasa ta ke moran Zainab Kurma son ranta tun tana ƙarancin shekaru.

Yau rumfar Ale Faruƙ a cike ta ke da mutane magidanta da zawarai. Benchi uku aka jera kuma duk sun cika da mutane. Yankan farce akewa Ale Faruƙ lokacin da ya ɗaga ido yaga Kurma na tahowa rumfarsa kanta a ƙasa saboda kunya.

Yana ganin yaron shagonsa Iro ya miƙe yai saurin miƙewa ya ƙariso wajen.

Da hannu ta ke nunawa Iro daron shinkafar da ke kan teburi tana nuna ma sa yatsunta biyar alamun mudu biyar zai auna ma ta. Ba yau ta fara zuwa ba shiyasa Iro ya fahimci bayanin ta. Zai fara aunawa kenan Ale FaruÆ™ ya dafa kafaÉ—an sa ya ce ya koma ya zauna zai auna ma ta.

Mudu biyar ta ke so, Iro ya faÉ—a kafin ya bar wajen dan ya san halin Uban gidansa indai ya ga mace to hankalinsa ya tashi kenan.

Sai da Ale Faruƙ ya auna mudu biyar zai zuba na shida Kurma ta yi saurin kai hannunta dan ta dakatar da shi aka ci sa'a hannunta ya taɓa nashi. Dama tuni kyakyawan fiskanta ya riga ya zautar da shi balle kuma yanzu da ya ji sanyin hannunta akan na shi. Ta yi saurin ɗage hannun tana yi ma sa bayani akan mudu biyar ta ke son siya.

Ya san biyar ɗin ne yana so ya ƙara ma ta mudu ɗaya ne saboda neman guri a wajenta.

" 'yan mata ai ba a hana Ihsani. Idan na kyautata miki na san Allah..."

"Maigida kurma ce fa" Muryan Iro ya katse shi.

Ale Faruƙ ya wangale baki yana kallon Iro da mamaki. Yana kallo Iro ya karɓi kuɗin hannun Kurma ya miƙa ma ta ledar da aka zuba shinkafan bai iya cewa komai ba.

Sai da Kurma ta yi nisa ya samu daman tambayar ko ita É—in 'yar gidan waye?. Wani cikin abokansa ya ce " shege mutumina, yanzu kuma kan Kurma za ka koma kenan" yana maganan yana dariya.

Kafin a tashi a kasuwa Ale FaruÆ™ ya samu duk wani bayanai da ya ke so gameda Kurma.

Ya san marigayi Malam Inusa, balle uwa uba Baffanta wanda abokin karawan sa ne, yanzu haka yana bin Malam Sabo bashin kuÉ—i ma su yawa.

Ya so haƙura zuwa washegari kafin ya je ya samu Malam Sabon amma kuma zuciyar sa ta kasa nitsuwa, kyakykyawar fiskar Kurma ce ke ta ma sa gizau. Kusan ƙarfe tara da rabi ya nemi babban riga ya saka ya wuce gidan Malam Sabo.

Tun a daren suka gama magana. Tunda Ale Faruƙ ya ce ya yafewa Malam Sabo bashin da ya ke binsa ya fara washe baki saboda ya san ba haka kawai Ale Faruƙ zai yafe ma sa kuɗi ba sai dai idan akwai wani abu na shi da ya ke so ne. Da farko dai ya sa a ransa indai maganan Injin niƙan Asabe ne to kuwa za ayita dan ya san halin Asabe sarai. Sai kuma ya ji zancen akan 'yar wajensa ce Zainabu Kurma, indai ita ce ba shi da matsala da wannan.

*THE GOVERNOR'S WIFE*
...... MATAR GWAMNA....

*©Azizat Hamza*

wattpad Azi_zat

Bismillahir Rahmanir Rahim

Book one

10

Lokacin da Ale FaruÆ™ ya auri Zainab Kurma matan sa uku ne, dan bai jima da sakin ta huÉ—un ba. Da ganinta da auren duka-duka sati huÉ—u ne.

Mama Asabe har ga Allah bata so aka yi auren ba, ba kuwa saboda halin Ale Faruƙ ɗin bane na auri saki sai dan saboda ayyukan da Kurma ke mata. Duk wani ƙarfin sana'arta to Kurma ce.

Ita da Malam Sabo dai sun yi ƙarfa-ƙarfa sun mata gado da tabarma da buta daga nan kuma kowa ya tsuke Aljihun sa. Duk da kuwa irin kuɗin da Malam Sabon ya yaga a wajen Ale Faruƙ ɗin.

Inna Talatu wacce ta reneta lokacin tana yarinya da kuma wasu cikin 'yan uwan mamanta su suka haÉ—u suka mata sauran kayan É—akin.

Lokacin da aka kawo Kurma gidan ɗakin Iyani aka fara kaita wacce ta ke Uwargida sannan aka wuce da ita ɗakin Fulani wacce ta ke matarsa ta biyu a gidan, matar da ta zame masa ƙarfen ƙafa ita bata haihu ba amma ta ƙi tafiya duk da kuwa rashin mutuncin da take shukawa a gidan. Sai ɗakin Halime matarsa ta uku wacce shekaransu uku kenan da aure.

Lokacin da aka kaita ɗakin Tabawa ko kallon kirki bata yi musu ba, ta ɓantari goro tana taunawa tace "Faruƙu kenan. Abin nasa yanzu ya koma kan Miskinai. Allah rufa asiri"

Inna Talatu ta harzuƙa zatayi masifa wata yayarta ta hanata. Kafin su fita kuwa Inna Talatun ta kirata da tsohuwar banza. Tabawa ta biyosu tana zagi tana tsinuwa amma babu wanda ya kulata.

Rayuwar Zainab a gidan Ale Faruƙ tamkar 'yar aiki ce a gidan iyayen gidanta. Sati ɗaya da Ale Faruƙ yai yana kwasar amarci ya dinga tattalin Zainab, shi yake siyo mata abinci daga waje: nama, bredi, ƙwai da madara sune cimarta. Baiwar Allah har ta fara sake jiki tana godewa Allah tunda rayuwar da take ciki yanzu akwai daɗi ba kamar gidan Mama Asabe ba.

Lokacin da aka fara rabon girki nan ne ta ƙwammaci kiɗa da karatu. Gidan Ale Faruƙ babban gidane wadatacce dan kowacce mata ciki da falo gareta, shima sashensa ciki da falo ne, sai ɗakuna huɗu na yara sai ɗakin mahaifiyarsa Tabawa, sannan akwai ɗakuna uku a zaure na saukan baƙi. A lokacin daya auri Zainab 'ya'yansa goma shabiyar ciki kuwa bakwai ne da iyayensu. 'Ya'yan Iyani su guda shida, maza biyu,mata huɗu sai Halime dake da 'ya ɗaya.

Da farko Fulani ce ta fara É—aurawa Zainabu nauyin girkinta daga baya Iyani da Halime suka biyo baya. Kafin kace me gaba É—aya ranakun girkinsu ita ke yi. Fulani kam hatta Sana'arta na shinkafa da wake da take da rana sai da ya zamo Zainabu ce ke yin komai , ita dai sai kawai idan ta gama ta zauna ta dinga siyarwa.

A hankali Yaran gidan da suka ga iyayensu na saka Zainab aiki sai suka fara taɓawa suma. Lokaci lokaci sai su bar mata wanke-wanken gidan ko kuma su jiƙa kayan wanki su ƙi wankewa saboda idan Kurma ta zo ta gani tana son amfani da baho ko bokiti dole sai dai ta wanke musu kayan tunda bata da mugun zuciyar da zata bar musu kayan a ƙasa. Ranan da ta fara zuwa ta ga sunyi haka, ɗakin yaran ta je tana musu bayani akan za tayi amfani da bahon wanki. Haka suka manna mata hauka akan basu san mi take faɗa ba, abin takaicin yawanci bahon nata ne dan Fulani da Halime basa taɓa barin nasu a waje. Ita kuwa Kurma ko bata fito da su ba yaran sukan shiga ɗakinta su ɗauka babu yadda ta iya.

Cikin zalunci da ake yiwa Zainabu ba abar Tabawa a baya ba. Itama ba ta taɓa ragawa Zainabun ba, dama duk cikin matan Ale Faruƙ babu wanda ta ɗauki mahaifiyarsa da daraja haka ma jikokinta. Kafin zuwan Zainabu gidan Tabawa ke wanki da kanta, haka ma abinci sai abinda aka zuba mata amma Zainabu Kurma bata taɓa mata rowan abinci ba haka nan wankinta da gyaran ɗaki duk ita ke yi.

Kafin shekara ɗaya Zainab ta zabge ta koɗe. Aikin da take a gidan Ale ko rabinsa bata taɓa yi ba a gidan Mama Asabe.

Ale Faruƙ ya san mi yake faruwa a gidan tunda shi ba makaho bane amma halinsa dama shine idan mace ta shigo gidansa komai ta tarar ruwanta ne, sai dai ta ƙwaci kanta daga sharrin sauran matansa amma shi ba zai tanka ba.

Akwai lokacin da Zainab tayi ɓarin cikin sati uku bata sani ba bata ma san cikine ba dan jinin al'ada ta ɗauka.
Chapter 21 · 0% Book details